Sashe 21
Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau da wuri Nene ta dawo asibitin. Dan haka ta kora su Amaal gida suma saboda mijinta daya shigo Abuja. Daga nan ma asibiti da yazo ya duba Maanal ɗaukar Amal ɗin yay suka wuce masaukinsa. Itama Shahidah da mijinta yazo sai suka wuce kawai. Hakan yasa Maanal ta kasance daga ita dai Nene a ɗakin. Sai kuma duk kaɗaici ya isheta. Dan Nene da zaran tayi sallar isha'i zakaga ta fara gyangyaɗi abinta. Gashi babu waya a hannun Maanal ɗin, tana Kaduna aka barta, bakuma a kawo mataba har yanzu. Shiyyasa ma taima Shahidah maganar a sayo mata kayan zane-zanen ta dan ta iya sosai, shine Yazeed yaji ya hana Shahidah siyowa shi ya sayo mata. Tun ɗazun daya kawo mata su ta ajiye bata sake bi takansu ba. Sai yanzu ta jawo ledan ta fiffito da su. Komai da take buƙata akwai, harma da wanda batace a sayo ba ya sayo. Dan haka sai ta gyara zama kawai ta fara zanenta dan shine hubby nata tun tana yarinya. Maanal ta masifar iya zane ta yanda idan ta zana abu sai ma ka ɗauka ba itace ta zana ɗin ba. Da farko ɗakin jiyyar tata ta fara zanawa harda Nene dake zaune a kujera tana famar gyangyaɗi, sai ita kanta a yanayin da take zaune. Koda ta gama taga komai ya mata sai ta tsinta kanta kuma da fara zana agogo. Abinda ta jima batayiba a rayuwar zanenta kenan. Ta zana guda biyu tana akan na uku RK da Doctor Ranjet suka shigo ɗakin. Firgigit Nene ta farka, yayinda Maanal tai ƙoƙarin rufe zanen nata amma sai caraf RK ya rikesa.
“Woow!, this is amazing”. Ya faɗa yana kallon zanen cike da matukar mamaki. Sai kuma ya kalleta. “Dan ALLAH da gaske kece kikayi Baby?”.
Kafin ma Maanal ta bada amsa Nene ta cafe cikin taɓe baki. “Yo in dai Manaalu ce ai baka rabata da zanen aljanai Rafeequ. Tun tana yarinya uwar tayi tayi amma ina harma an barta taitayi itace zata ƙare da mafarkinsu ai ba wani ba”.
“Nene ai abune mai ƙyau wannan ɗin.....”
“Ɗan nan a al'adar yahudu da nasara ba. Amma mudai a musulunce banjin cewar abune mai ƙyau duk da ni ɗin ba malama bace”.
Dariya RK yayi, sai kuma ya miƙama Nenen zanen yana faɗin, “Amma Nene kinyi fa ƙyau a wajen nan kamar wata sarauniya a kujera”.
Ba ƙaramin zare ido Nene tayi ba tana kallon kanta an zane ras harda yanayin atamfarta. Duka ta kaima Maanal itako ta kauce tana ƙara ɓata fuska. Aiko ta shiga zazzaga jaraba shi dai RK da Dr Ranjet na dariya abinsu. Manaal dai ta miskile fuska kamar ba ita tai tsiyar ba. Sai da Nene tayi mai isarta sannan ta fice dan idan anzo duba Maanal ɗin fita takeyi. Bayan fitar Nene Dr Ranjet na duba Maanal RK daya kasa ajiye zanen ya dubi Maanal cikin serious ya ce, “Amma basirar nan naki bai kamata ya tafi a banza ba kawai, yana da ƙyau mutane su amfana da shi”.
“Kamar ya?”.
Ta faɗa a ƙasan maƙoshi. Bai damu ba, dan zuwa yanzu ya sake fahimtar miskilancinta mai lasisi ne.
“Akwai Companyn da nasan suna matuƙar buƙatar aiki da mai irin wannan basirar taki”.
A daƙile ta furta, “Ba buƙata”.
Cikin ɗan girgiza kansa ya ce, “Wlhy seriously Baby akwai companyn da zakiyi wannan aikin fa kuma anan Abuja ne, Please kada kice a'a dan ko kina gida zaki iya musu aiki ma”.
Rasama abinda zata cemasa tayi, dan yanda ya wani marairaice fuska ya tsareta da manyan idanunsa sai ta ji ta kasa furta komai. Dr Ranjet ne ya saka baki a zancen nasu, “He is telling you the truth my patient.. Ko game da ciwonki idan kin samu abinda zai dinga maidaki busy zaisa ki rage saka damuwar abubuwa a ranki da har zai dinga yawan tashi akai-akai”.
Shiru kamar bazatace komai ba. Sai zuwa can ta sauke ajiyar zuciya tana ɗan girgiza kanta. “Su Ammie bazasu amince ba ne. Kadai ji abinda Nene ta faɗa ai”.
“In dai har kin amince zakiyin ki barni dasu kawai”.
“Mi zakace musu?”.
“Ke dai kawai ki amince zaki ji ai”.
“Zanyi tunani”.
Ta faɗa a taƙaice tana zamewa ta kwanta. Bai sake magana ba shima sai ɗaukar hoton zanen da yay a cikin wayarsa kawai. Bayan fitarsu kafin barci yay awon gaba da Maanal tai zurfi matuƙa a tunanin zancen RK ɗin da Dr Ranjet.....
__________★
Lokacin da Yazeed ya iso gidan sha ɗaya saura na dare. Dan haka ya samu Daddy ya ma kwanta. Sai ya zarce sashen Ammie, samunsa yay shima a rufe, hakan na nufin tana sashen Daddy kenan dan su Waleed ba nan suke kwana ba suma. Dole sashen Hajiya Yaya ya nufa inda ya tadda ƙannensa zaune a falo jugum-jugum. Hatta da television bata aiki a kashe take yau. Da gudu Amrah tazo ta shige jikinsa tana sakin kuka mai ban tausayi. Rungumetan yay shima yana ɗan shafa bayanta. Kusan mintuna biyu sannan ya ɗagota tare da kama hannunta suka ƙarasa cikin falon. Nuni yay ma sauran da su zauna dan suma duk sun miƙe tsaye. Shima ya kai zaunen Amrah a gefensa.
“Mike faruwa ne?”.
Kafinma ya rufe baki su duka sun saki kuka. Wadda ke bimasa da suke kira Suhana ce ta fara masa bayani muryarta na rawa. “Yaya muma bamu san ainahin abinda ya farun ba. Kawai dai Mamma taje sashen Daddy, babu jimawa sai gata ta dawo kuma tana hawaye. Mun tambayeta bata kulamuba ta hau haɗa kayanta. Bamu sani ba ko sakinta Daddy yayi”.
“Saki?”.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖1️⃣6️⃣
..........“Haka muke tunani Yaya. Tunda bamu taɓa ganin Mamma ta haɗa kaya tabar gidan nan ba dan sun samu matsala da Daddy.”
Basira ta bashi amsa cikin kuka. A take zufa ta gama wanke masa jiki, harma ya gagara cewa komai. Badiyya ce ta sake katse masa tunani da faɗin, “Yaya kuma wlhy koma minene ya faru da sanya hannun waccan munafukar matar a ciki. Dan tana a sashen Daddyn komai ya faru, ko sanda Mamma zata tafi da muka je kiran sa itace ta hanashi”.
Cikin mamaki ya ce, “Ita wa?”.
Kai tsaye ta bashi amsa da, “Amaryarsa mana”.
Hararar daya zuba mata ya sata kame bakinta tana turashi gaba. Dama sun san ai bazai yarda ba tunda agolan ƴarta ce budurwarsa. Bai sake cewa komai ba ya miƙe, sai da ya kusa kaiwa ƙofa ya juyo yana kallonsu. “Kutashi kuje ku kwanta zuwa da safe koma miza'ai sai ayi. Ku kulle nan ɗin”.
Wasu sun amsa masa da to, wasu ko da hararar ƙasan idanu suka rakashi dan sun san babu damar yi a zahiri mutum yaci dukan banza a daren nan balle ma babu Mamma.....
★★★
Washe gari koda Yazeed yazo ganawa da Daddy sai ya samu har ya fita. Sashen Ammie ya nufa, inda ya taddata zaune jihum alamar tana tare da damuwa harma da ɓacin rai. Gaisheta yay da girmamawa kamar yanda ya saba. Itama ta amsa masa cikin kulawa tana danne damuwarta.
“Yanzu ka iso ne?”.
“A'a tun da daddare. Around eleven na samu kunyi barci shiyyasa na haƙura har sai da safe. Yanzu kuma naje sashen nashi naga alamar a rufe yake”.
“Nima nazo na haɗa masa breakfast na koma naga yabar gidan. Ka ganni tun ɗazun nake kiransa yana rejecting daga ƙarshe ma ya kashe wayarsa gaba ɗaya.”
“Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un”. Yazeed ya shiga ambata yana mai dafe kansa da dukka hannayensa biyu.
“Yazeed nikam da zakaji daka haƙura da batun auren nan na Maanal. Dan idan zamu duba gaskiya duk batunsane tushen wannan matsalar. Kayima Hajiya biyayya ALLAH sai ya baka wadda tafi Maanal”.
“Amma Ammie ina sonta, wlhy matuƙar so nakema Maanal dan ALLAH kar kice haka, ke da Daddy ne ƙwarin gwiwata. Sannan shima Daddy ai yanada hakki a kaina kuma yana son auren. Miyasa Mamma bazata fahimta ba. Miyyasa bazata fahimci Aunty Sabuwa tana zugatane kawai saboda ta samu biyan tata buƙatar na auri tata ƴar bane?”.
“Amma Yazeed ƴar uwartace fa, uwa ɗaya uba ɗaya. Taya bazata tayata son abinda take so ba.”
“Amma wlhy Ammie akwai manufa a zuciyar Aunty Sabuwa. Mamma ɗin ce kawai ta kasa fahimta”.
Rasa abincewa Ammie tayi, dan itakam wannan cakwakiya ta ma fara gundurarta wlhy. Tabbas tana matuƙar son Maanal ta auri Yazeed kodan ƙyawawan halayyar yaron. Sai dai tana tsoron halin Hajiya Yaya gaskiya. Sannan tana tausayi da fargabar jefa rayuwar yarinyarta mai raunin ciwo a cikin wani hali. Yazeed shi kaɗai ke son auren nan sai mahaifinsa. Amma ƴan uwansa da mahaifiyarsa da mafi yawan danginta basa so sam.....
________________★