← Book details Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 148

Sashe 101

Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Bayan sun kammala cin abincin ta gama tsiyaya musu surutunta Oum tajata zuwa ɗakinta tai mata wanka. Kaya gareta fal a gidan, anan ɗakin Oum da ɗakin su AA a cikin kayansa. Tana cikin shiryata Ajwaad ɗin ya shigo hannunsa riƙe da kayan tsifa. Tana ko kallon hannunsa ta ɓata rai dan bata ƙaunar kitso sam. Fuska a marairaice kamar zatai kuka ta ce, “Besty kaina na ciwo”.
       Harararta ya ɗan yi yana kaiwa zaune a bakin gadon Oum da faɗin, “Idan an gama zaki sha magani”. Sosai ta tura baki gaba, sai kuma ta kalla Oum dake gumtse dariya. “Oum dan ALLAH kaina bada zafi ba? Taɓa kiji ma”. Dariya sosai Oum ta fashe da shi tana taɓa kan, “Gaskiya Babyn Oum babu wani zafi, kanki yayi datti ki daure a tsefe kinji, jibi ƙasa a cikinsa tule. Ko baki son kuje Saudian da Abah yace?”. Jiki a sanyaye ta ce, “Ina so Oum”.
     “Yauwa ton daure kinji ƴar albarka. Ai Auta bazai miki da zafi ba kin sani ko? Gama chocolates bari na baki kije anayi kina ci baza kiji ma anayi ba har a gama”.
     Da wannan lallashin ta yarda badan taso ba. Haka suka fito hannunta ɗauke da ɗan bowl da Oum ta haɗa mata kayan kwaɗayi, ɗayan kuma Ajwaad ya riƙe mata. Tsakar gida suka fito tacan baya inda garden ɗin gidan yake, wajen akwai ni'ima sosai dan an gyara shi yanda ya kamata. Ga kujeru an shirya domin hutawa harda na yara, sai lilo da dai kayan wasan yara. Koda suka zauna sai da ya ɓare mata chocolate ɗin ya bata wayarsa sannan ya fara mata tsifar. A hakan ma yana farawa ta ɓata fuska zatai masa kuka. Sai da shima ya ɓata fuskar da faɗin, “Oh nacema Abah ɗin  mu wuce mu barki?”.
     Da sauri ta girgiza masa kai.
Ya ce, “To oya malama nutsu”.
Baki ta tura gaba da faɗin, “Niba sunana malama ba”.
    Murmushi yay a karo na farko, tare da jan hancinta ya ce, “To Bestyn bestyn ta ko?”.
      Cike da jin daɗi ta ce, “Yes”.
  Ƙaramar dariya yayi, sai kuma ya buɗe baki alamar ta bashi chocolate ɗin. Cirowa kuwa tai ta saka masa a bakinsa, ganin ya ɗan ɓata mata yatsun yasa shi kama hannun nata ya lashe wadda ta maƙale. Murmushi tai da faɗin, “Kwaɗayi”.
      “Ai ke kika koya min”.
Ya bata amsa yana murmushin shima. Sannan ya fara mata tsifan. Tana kallon cartoon ɗin daya sanya mata tana masa surutu da juyowa ta bashi chocolate ɗin da sauran kayan ciye-ciyen. Shi ko yana biye mata. Dama in kaga Ajwaad na zuba surutu da murmushi to lallai Maanal na a wajen kuwa tabbas. Baya wasa da al'amarinta ko kaɗan. Idan ka gansu dole su birgeka kamar ba yara ba. Haka dai aka gama tsifan, wajen taja kuma aka hau faɗa, sai da ya riƙeta da ƙyau sannan ya iya taje mata, ita ko tana kuka da faɗin babu ruwanta da shi kada ya sake kulata. Dariya ya dinga yi shi dai bai kulata ba sai da ya gama ya ɗaure mata da ribbon duk da yayi datti. Dan cikinsa uban ƙasa ne na faɗan data dinga kwasa a Giro, a hakan ma wai kusan kitso na fin biyar ne akan nata a zuwansu. Koda suka dawo cikin gidan fushi ta dinga masa, sai ta koma kula Fawzan shiko Ajwaad ɗin ya sharesu. Hakan da yake yi idan tana tare da wani a cikinsu yake sa suke faɗin suma yana kishi da su akanta..

_____________★

         Washe gari suna gama breakfast Ajwaad ya tasa Maanal gaba zuwa wajen kitso. Ita ko tana faman kuka da faɗin bafa zataje ba. Sai da ƙyar Oum ta lallaɓata ta yarda bayan ta mata alƙawura. Koda suka fito tsakar gida inda ɗan kekensa yake sai da ya hau itama ta hau daga gabansa tanata cika baki da iska. Shi dai bai kulata ba yaja keken suka fito. Ai tun daga gida har zuwa shagon Aunty Saloon duk inda suka gitta sai an musu magana. Dan Maanal fa cele ce a anguwar tasu saboda tsabar fitinarta da neman faɗa. Yara ɗai-ɗai ne batai rigimar da taja Ajwaad ya jibgesu ba.
            Da farin ciki Aunty Saloon ta tarbesu tanama Maanal oyoyo da dawowa. Itako ta ɓata fuska taje jikin Ajwaad ta maƙure idanunta cike da ƙwalla. Dariya Auntyn ta fara yi da faɗin, “Maanal ke baki girma da ƙin kitso? Haba ƴar gatan Ajwaad Bestyn ta. Shi gashi yana son yaga ana gyara masa ke da kitso ke kuma baƙya so”.
     Baki Maanal ta sake turawa gaba da kallon Ajwaad, shima kallon nata yake yi. Sai ta sake ɓata fuska zatai kuka. A hankali ya kai durƙushe gabanta ya dai-dai tsahonsu hannayensa duka akan kafaɗarta cike da lallashi ya ce, “Ba kin min alƙawari bazakiyi kuka ba? Ko kina son yaran anguwar nan su ganki su samu abin raina ki da tsokana”.
    Kanta ta girgiza masa hawayen dake cike a idonta na gangarowa. Hannu yasa ya share mata, “To kada na ƙara ganin hawayen nan. Inba hakaba kuma na fasa shiga secondary ɗin tare dake”.
      Da sauri ta haɗiye kukan, cikin rawar murya ta ce, “To bana bari ba”.
    “Yauwa my sweet Besty. Faɗa min mi kike so naje na saya miki? Ko awaran can?”. Ya nuna mata waje can tsallaken titi da mai awara ke ta soyawa. Kanta ta jinjiina masa. Shima sai ya miƙe tare da kama hannunta ya kaita saman kujerar wanke kan ya zaunar, fita yayi tana kallonsa daga nan. Bai wani jima ba ya dawo da awaran a leda. Lokacin har Auntyn Saloon tayi shirinta na fara wankema Maanal ɗin kai. Dan duk ta fito da kayan shampoo ɗinta da suka zo dasu a cikin ƴar bag. Haka komai na Maanal a tattale yake ga Ajwaad. Sam bai yarda a mata amfani da kayan wankin kan wajen saloon ɗin ba, duk abinda yasan ana buƙata idan sukaje shopping da Abah ke kaisu duk ƙarshen wata zai ɗakkosa. Dan shi dama ko a wajen shopping ɗin zakaga duk abubuwan da yake ɗakkowa na Maanal ne. Ƙalilan zaka samu nashi. Kujera ya jawo gabanta sosai ya zauna, dan yasan bazata yarda ba sai anyi darun. Bai bata awaran ba ya ajiye gefe yacema auntyn Saloon ta fara. Kuka Maanal ta fara ƙoƙarin farawa ya girgiza mata kansa, sai tai shiru. Haka dai aka wanke kan yana riƙe da hannunta da lallashi kamar wata ƴar mitsilar yariya can ba ƴar shekara kusan takwas ba. Koda aka gama shi da kansa ya goge mata kan da towel ɗin da sukazo da shi ya ɗaure mata shi, sannan ya dinga bata awaran a baki ana busar da kan. Da aka zo kitso kam daru aka sha na haƙiƙa, dan dole sai da ya riƙeta, amma a hakan yasha cizo a hannu da bibbigewa. Kitson ma ba wani mai yawa ba dan shikku ne. Sosai ya mata ƙyau aka saka mata bet. Maanal akwai gashi Masha ALLAH, dan sun biyo Ammie ne cikar gashi da tsaho kamar ba nasu ba.
         Sai faman sauke ajiyar zuciya take idanu sun yi jazur saboda kuka ta kama hannunsa tana dubawa, dan duk sayin ƙananun haƙwaranta. Sake fashewa tai da kuka tana shafa cizon da kallonsa, shima idon nasa duk ya kaɗa saboda kukan nata. A hankali ya ce, “Minene kuma? Ba'an gama ba?”.
      Hannunta na bin wajen cizon ta ce, “Da zafi ko? Muje na amshi magani wajen Oum na baka”.
     Murmushi yay mata da girgiza kansa, sai kuma ya shafa kitson nata da yay ƙyau sosai ya ce, “Babu zafi fa. Jiba yanda kanki yay ƙyau. Ya kamata ki daina kukan kitso Besty kin girma.”
         “To ai Oum ta ce idan na girma zan daina ”.
    “Wane girma kuma ya rage Besty. Secondary fa zamu shiga ai kin girma ko. Ba kiga ni idan kika rakani wajen aski bana kuka ba”.
         A sanyaye ta ce, “Zan bari. Besty muje gida zanyi barci”.
   Kansa ya jinjina mata tare da miƙewa. Cikin girmamawa ya kalla Auntyn Saloon dake kallonsu cike da sha'awa da mamakin irin wannan al'amari tamkar ba yara ƙanana ba. Godiya ya mata ya ɗauka bag ɗin sannan ya duƙa Maanal dake faman lumshe ido ta hau bayansa. Kekensa ya kalla sai kuma ya kalla Auntyn Saloon ɗin. “Aunty zanje na kaita sai na dawo na ɗauka”.
       “To babu damuwa Ajwaad sai ka dawo. Ka gaishe da Hajiya. Maanal daru sai kuma next”.
   Maanal dai bata kulata ba, sai ma sake lafewa da tai a bayansa dan barci take ji sosai. Tana fita wanda ke a cikin shagon suka fara gulma. Aunty Saloon dai dariya take yi da sake basu labarin wannan shaƙuwa ta Maanal da Ajwaad dake birge kowa a layin tamkar ba yara ba...

     Kafin su iso gida har tayi barcin. Oum da Mamy na falo suka shigo. Muskar Oum da murmushi ta miƙe tana faɗin, “Ai na sani dama da barci zaku dawo gidan nan. An sha darun ma yau kenan?”.
      Fuskar Ajwaad da murmushi shima ya ce, “Tab Oum miza'a fasa. Duk na sha cizo”.
    Dariya Oum ɗin tayi da faɗin, “In ba Bestien taka ba wazai cijeka a zauna lafiya Auta. Maza jeka ka kwantar da ita to”.
     Ɗakin Oum ya kaita ya kwantar, sai da ya rage acn ɗakin ya cire mata ɗab hijjabinta sannan ya fito. Oum na tambayarsa ina kuma zaije yace zai ɗakko kekensa ne. Daga haka ya fice. Mamy dai bata saka musu baki ba. Yana kuma fita suka ɗora da hirarsu da suke yi ita da Mamyn hankali kwance cike da farin ciki kuma kamar ba kishiyoyi ba. A haka Ajwaad ya sake dawowa ya samesu. Ɗakinsu ya wuce yana tambayar ina su Fawzan. Oum tace sunje aikan datai musu ne. Daga nan zasu duba malaminsu na islamiyya suji yaushe zasu koma. Dan tun wancan satin ya kamata su koma matar ya sayyadin ta haihu, haihuwar kuma tazo da matsala shine ya ƙara hutun, sai dai bai sanar da ranar komawar ba taka maimai. Ciki ya shige suma su Oum ɗin suka miƙe dan lokacin salla yayi.........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨
Chapter 101 · 0% Book details