Sashe 60
Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ƙarfe huɗu da kusan rabi danƙareriyar motar Fawzan ta iso gidan. Yana gama parking Barrah da Haneeff suka fice zuwa cikin gida aguje suna ƙwala kiran mamansu. Dariya Fawzan ya dingayi, dan shi ALLAH ya ɗaura masa son yara matuƙa. Kodan har yanzu ALLAH bai bashi bane. Dan matarsa bata taɓa ko ɓatan wata ba shekara shida kenan. Oum ma dariya take ma yaran. Maanal dai komai batace ba, sai ma jagorantar su Oum tayi zuwa cikin gidan. Sun sami Shahidah na ƙoƙarin fitowa tarbar su Oum, dan haka sukaci karo a ƙofa. Cike da wani irin farin ciki Shahidah da Oum suka rungume juna. Sai kawai Shahidahn ta saki kuka. Harga ALLAH tana matuƙar son Oum, dan mace ce ƴar halak da bazasu taɓa mantawaba a tarihinsu. Ta matuƙar taka rawar gani a garesu da Ammien su ta yanda baki yayi kaɗan ya bada labari. Itama Oum ɗin hawaye take da murmushi duk a lokaci ɗaya, ta ɗago Shahidah tana mai share mata hawaye. “Uhm-uhm kefa yanzu kin girma Sheedan Oum, ke uwa ce babbar yaya kuma”.
Dariya Shahidah ta shigayi, hakama Fawzan dan tuno wani abu daya shuɗe. Maanal ma dai murmushi ne mai faɗi akan fuskarta. Abinda a yanzu yake da matuƙar tsada da wahala a gareta. Sai da Shahidah ta saki Oum sannan ta lura da Fawzan, cike da mamaki ta riƙe haɓa da faɗin, “Oh ni ALLAH wanake gani haka ya zama dattijo?”.
“A'a tsoho na zama ba dattijo ba”. Fawzan ya bata amsa yana hararta. Dariya duk suka sanya masa. Shahidah ta ce, “ALLAH kuwa ka yarda ka zama dattijo yanzu Yaya Fawzan”.
“Kema kin zama dattijuwar ai”.
Ya faɗa dai-dai suna kaiwa zaune a ƙayataccen falon nata. Dai-dai nan mijinta ya fito. Cike da mamaki idonsa akan Fawzan ya ce, “Kai kai wanake gani haka kamar Darma a gidana”.
“Ya arrahaman Busam!”.
Shima Fawzan ya ambaci sunansa yana miƙewa. A tare suka cafke alamar lallai sun san junan kuwa sani bana wasaba. Ai sai su Oum suka koma ƴan kallo. Sai da ƙyar Shahidah ta iya faɗin, “Nifa ban gane ba, wai dama kun san juna ne?”.
“Farin sani ma kuwa. Darma tare mukai degree master namu ai a Germany, sannan a yanzu haka akwai alaƙar aiki a tskaninmu. Kawai dai baya son zumuncine shiyyasa baki taɓa ganinsa a gidan nan ba.....”
“Wulaƙanci ai kai zumuncin kake so?”.
“Nadai fika tunda ni naje gidanka har sau biyu”. Cewar Abban su Barrah. Dariya Fawzan yay da faɗin, “Gori kenan. To yanzu ai gashi ALLAH ya kawoni, ashema ni ƙanwata kake aure kai wannan abin kunya da yawa yake”.
“Ato kaima dai ka faɗa”.
Cike da girmamawa Abban Barrah ya gaida Oum. Itama ta amsa masa da kulawa cike da farin ciki. Nan fa aka ɓalle taɗi tsakanin Oum da Shahidah, Fawzan da Abban Barrah. Yayinda Linda tuni ta cika musu gabansu da kayan ciye-ciye Maanal na tayata. Duk wannan bidiri da ake Huznah na ɗaki tana shaƙar barci abinta. Sai da Maanal ta taje ɗakin ajiye kaya ta ganta baje a gado. Komai bataceba ta ajiye ta dawo wajen su Oum. Sai ga RK da dama yay musu alkawarin samunsu a gidan. Nan fa hirar ta ƙara armashi dan tuni Abban Barrah ya janyesu sun koma falon baƙi dan Oum ta sake itama suyi tasu hirar. Hakan yama Oum ɗin daɗi sosai, dan ta samu tattauna abubuwa da yawa da Shahidah wanda Maanal ta kasa sanar mata komai saboda zurfin ciki da miskilanci. Sai da akai magriba sun dawo Huznah ta fito. A ɗan yatsine ta gaishe su, sai dai saukar idanunta akan Fawzan yaso birkita mata lissafi. Sai da ta nutsu ta fahimci ashe ba AA ɗinta bane kammanni ne kawai. Dan suna kama sosai da AA ɗin, sai dai wasu abubuwa da suka ɗan babbanta su. Hakama kuma suna kamanni da Oum matuƙa. Hankalin Huznah ne ya tashi, dan haka kawai take ji a ranta wannan mutumin na kama da AA ɗin ta hakama matar, sai dai yanda ta gaishesu yasa daga amsa gaisuwar kowa ya watsar da ita musamman RK da kamar basu ƙaunar juna ita da shi.
Su Oum na gidan nan har tara, dan har sai da Autan ta ya kirata yana damunta shi dai ta dawo ya koma gida tun ɗazun duk basa nan gida babu daɗi kuma yana jin yunwa. Dariya Oum take masa da tsokanarsa akan wannan hali nasa na ɗafa, ya girma amma bai san ya girma ba koda yaushe yana laƙafe da ita. Idan tai masa aure yaya kenan. Shi dai roƙonta ya cigaba da yi akan su taho kawai. Tace shi bazai zo ya samesu anan ba yace ya gaji. Ƙyalesa tai tace gasu nan tahowa. Amma wayar Maanal fa ba'a gyara bane?. Sai cemata yay eh wai mai gyaran yace sai Monday ma.
“ALLAH ya kaimu” ta bashi amsa tare da sanar masa gasu nan dawowa. Sosai Shahidah ta haɗama Oum shata ta arziƙi, duk da tasan tafi ƙarfin duk abinda ta batan. Saboda suma su Maanal haka Oum ɗin ta haɗo musu abubuwa iri-iri na tsaraba. Da suka fito kuma sai da suka shiga super market ma aka ƙara wasu sayayyar. Huznah dai duk jikinta yayi sanyi da ganin waɗan nan ƴan gayun mutane gogaggu wayyayun ƴan boko da hutu da jin dadi ya gama ratsawa. Sai kuma gefe ɗaya na zuciyarta ya kasa samun nitsuwa akan kamannin Fawzan da AA ɗinta da kuma Oum. Jiki a sanyaye ta biyo su Maanal rakkiyar su Oum har mota. Maanal na manne da Oum ɗin sai shagwaɓa take mata cikin maganar nan tata ƙasa-ƙasa dake sake narkar da RK tana baƙanta ran Huznah da ganin tsantsar iskanci ne kawai da bariki kesa Maanal ɗin maida muryarta haka. Gefe kuma Fwazan na tsokanarta wai sun saka musu Oum ɗin su tsakkiya da shagwaɓar tsiya, ita tayi Auta yayi.
Dariya kawai Oum tayi da faɗin, “Babu ruwanka barni da kayana, suyi abinsu san ransu ko Auta?”.
Cike da jin kunaya Maanal ta ɓoye fuskarta a jikin Shahidah. Dariya suka sanya mata. Daga haka sukai sallama Oum na sanar mata wayarta zata taso mata ƙeyar AA ya kawo mata idan an gyara. Kai kawai ta iya ɗagama Oum tana ɗan murmushi, amma a ranta tasan bamai yiwuwa bane ya kawo da kansan. Shima kansa Fawzan murmushi yayi yaja mota suka fice. Sai RK dake tsaye jikin tasa. Ciki su Shahidah suka koma da yaran aka bar Maanal a wajensa zasuyi sallama, kamar zata sharesa. Sai dai ganin yanda Huznah ke wani binsu da kallon ƙwaf ya sata nufarsa....
“Humm dama haka kika iya shagwaɓa my queen?”.
RK ya faɗa yana binta da kallo ƙasa-ƙasa. Murmushi kawai tai masa mai sanyi kanta a ƙasa. Batare da tace komai ba. Shima sai ya saki murmushin da sake maida hannunsa ya harɗe a ƙirjinsa. “Koda yake ma ni fushi fa nake dake”.
Ɗan ɗagowa tai ta kallesa da faɗin, “Akan mi?”.
“Humm akan komai ma. Yanzu ace akwai alaƙa mai ƙarfi irin haka a tsakaninki da AA amma ban taɓa sani ba Maanal, ko'a fuska baki nuna min ba shima haka kuka wani rufeni a duhu. Zaman amana kenan?”.
Sosai gaban Maanal ya faɗi, ta zuba masa ido, ganin shima ya zuba mata nasa idanun tai saurin janye natan zuciyarta na duka. A ranta kuwa tunani take wace alaƙar a ciki yake magana kenan? Badai yaji komai ba? Badai yasan komai ba? Shi AA ɗin ne ya sanar masa kenan kamar yanda yace zai yi ko kuwa? Dan tanada yaƙinin Oum bazata faɗa masa ba duk da kasancewarsa jininta ƙani uwa ɗaya uba ɗaya.
Cikin wani irin sanyi ta ce, “Mi kaji a kaina?”..........✍️
😨😨😨😨😨🚶♀️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖4️⃣0️⃣
______________