← Book details Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 148

Sashe 46

Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.......Ita kam koda takai file office ɗin Boss ta ajema AS office ɗinsa ta koma ta cigaba da aiki, dan akwai abinda take son kammalawa kafin ta wuce gida. Kiran sallar magriba ya sata ƙarasawa sauri-sauri sannan ta tashi tayo alwala ta haɗa kayanta ta kashe komai ta fito dan su Yaqub tuni duk sun wuce sai ita kaɗai. Shiru babu motsin kowa duk an wuce. Sai offices ɗai-ɗaine ƴan over work irinta koma wanda suka fita ke'a buɗe. Ƙananun ma'aikata ma ta wuce kusan mutane huɗu basu wuce ba, koda ta fito harabar companyn ma motoci biyar kawai ta gani sai mashin biyu alamar na wanda suka ragene. Idanunta suka sauka akan motar boss. Janyewa tai tana taɓe baki, shi dama ai yafi kowa iya over work, dan kullum shine ƙarshen barin office. Masallaci ta nufa domin gabatar da magriba. Bayan an idar koda ta fito bata koma ciki ba, hanyar gate ta nufa abinta a ƙafa. Street ɗin shiru babu yawaitar mutane a ƙafa sai motoci, sai dai ko'ina akwai haske kamar kana wata ƙasa ba Nigeria ba. Taxi nada wahalar samu a wajen kasancewar duk manyan ma'aikatu ne ata wajen, sai gidajen cin abinci da suma ba laifi suke da yawa ta wajen da shopping malls guda biyu dake can farkon shigowa. Tsoron kar dare ya sake mata ya sata cigaba da tafiya a ƙafa tana jin nadamar kaiwa haka bata tafi gida ba, har Shahidah cewa tai zata aiko a ɗauketa idan ta gama tunda tace ita karta biyo ɗaukarta yau tana da aiki amma tace mata a'a zata hau taxi. Tayo tafiya babu laifi zuciyarta ta fara karaya, dan ƙafafunta sun fara gajiya. Mamakine ya kamata ganin ƴammata tsaitsaye kamar masu jira azo ɗaukarsu, amma abinda zai baka mamaki suna da yawa duk da kowanne yana tsaye ne shi kaɗai ko su biyu. Cigaba tai da tafiyarta dai tana ɗan kallonsu sai taji ana horn, da sauri duk hankalin ƴammatan ya koma wajen motar, wasu ma duk sun nufi motar ne, sai dai kuma mai motar bai tsaya ba ya cigaba da bin bayan Maanal ne ana kuma horn ɗin dai. Da sauri ta ɗan ja da baya sakamakon shan gabanta da akai da motar, cikin wani irin ɓacin rai ta ɗago dai-dai mai motar na sauke glass ɗinsa. Babban mutum ne da a shekaru ma zai iya haihuwar su Shahidah bama ita ba, yana daga baya kwance driver ɗinsa a gaba, cikin tsareta da ido ya sakar mata murmushi. Ɗauke kanta tai da sauri ta raɓa ta wuce wani irin ɓacin rai na mamayeta. Jin an ƙara biyo bayanta da mota ana mata horn again ta tsaya cak, cikin matuƙar fusata da harzuƙa ta ɗago dan ta gama shirya yima tsohon banzar nan zagin ƙare dangi, amma sai kawai taga motar boss ba wancan bane. Kafin ta iya haɗiye abinda ke bakinta AS ya fito daga gaba, kai tsaye inda take ya iso, furkarsa da murmushi ya furta, “Sister Maanal bismillah ki shiga”. Yay maganar yana miƙa mata hannu da nufin amsar kayan hannunta. Kai ta girgiza masa tare da janye hannun nata tana faɗin, “Karka damu na gode”.
          “Idan shi bai dace ba, inaga ni kamar zan dace tunda dama ni na fara tayawa”. A bazata taji muryar tsohon nan cikin kunnenta daga bayanta. Jitai gaba ɗaya kamar ta daburce, ga zuciyarta na wani kalar bugawa da sauri-sauri har numfashinta na neman fara yin sama-sama. Babu alamar wasa ko ragi a tare da ita ta juya ga tsohon nan, hannu ta ɗaga da nufin nunashi a hankali taji saukar wani tattausan hannu ya riƙe mata yatsu, batare da cewa komai ba yaja hannun nata. Ƙoƙarin fisgewa ta fara sai dai bai bata damar hakan ba har ya iso da ita jikin mota. Sai lokacin ta iya zuba masa manyan idanunta da suka kaɗa, shima kallon nata yake cikin ido. Kusan minti ɗaya suna kallon juna kafin ya zare kayan hannunta tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Get in”.
        Rasama mi zata ce masa tayi, dan sam babu ko ɗigon wargi a fuskarsa. Yayi masifar yin kicin-kicin da ita kamar zatai aman wuta. Bai kuma sake cemata komai ba ya zagaya ɗaya side ɗin ya shiga mazauninsa ya ɗauke kai. Dattijon Alhajin nan dake tsaye ransa a matuƙar ɓace ya sake takowa inda Maanal take. Ai yana buɗe baki zaiyi magana kawai ta shige motar, shiko AS ya rufe mata murfin ruf tare da kallon Alhaji fuska da murmushi ya furta, “Bye bye grandpa”. Shima ya zagaya ya shige motar driver yaja suka wuce.
      Da wani irin kallon ɓacin rai dattijon yabi motar da kallo, sai kuma ya jinjina kansa tare da cije lips da ƙarfi ya koma tashi motar. Da sauri driver ɗinsa ya buɗe masa ya shiga ya maida ya rufe suma suka bar wajen....

        Sosai Maanal ta takure jikinta waje guda, yayinda idanunta ke'a lumshe bugun zuciyarta kuwa gaba ɗaya ya sauya daga normal bugu. Ambaton sunan ALLAH kawai takeyi tare da ƙoƙarin danne kukan dake son kufce mata.
      AA Darma dake a gefenta kam tunda ta shigo bai ko kalleta ba. Gaba ɗaya ya tattara hankalinsa ne ga document ɗin hannunsa da dama shi yake dubawa kafin suga Maanal ɗin, koda yake bama shine ya ganta ba, AS ne ya ganta cike da mamaki ya furta (kai wannan ai Sister Maanal ce Alhaji Bukar ya tsare a hanya halan bata sami abin hawa bane har yanzu). Driver na tambayar AS wacece ita ɗin AA Darman ya daka masa tsawa akan su dakata, shine dalilin tsayawar tasu.
        A yanzun ma driver ne cikin ɗari-ɗari ya furta, “Sir! Zamu fara saukeka ne kafin a kaita?”.
     Shiru bashi da alamar amsawa. Sai da ya mula dan kansa batare da ya bar abinda yake ba ya bashi amsa a taƙaice. “Fara ajiye ta”.
     “Okay sir. Sister ina muka nufa?”. Ya maida akalar tambayarsa akan Maanal. Shiru bata amsa ba sai da ya sake maimaita tambayar sannan ta dawo hayyacinta. Cikin ƙoƙarin danne komai da yanayin nan nata na kamewa ta furta, “Samu waje kawai zan sauka na ƙarasa a taxi”.
      Kallon AA Darma drivern yay ta mirror ɗin gaba da tunanin ko zaiyi magana. Amma sai yaga ko kallon inda wani cikinsu yake bai yiba ma. Dan haka sai ya kalla AS cikin marairaicewa. Murmushi AS yayi tare da juyowa saitin inda Maanal ɗin take, “Please Sister Maanal bafa zamu ajiyeki ko'ina ba sai gida”.
      Rasama mi zatace tayi, sai kawai ta faɗa masa sunan anguwar a taƙaice. Bai gaji ba ya sake tambayar street, nan ma kamar bazata kula shi ba sai kuma dai ta faɗa. Daga haka bata sake magana ba ta maida idanunta ta rufe. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso abinka da lafiyayyar mota a saman lafiyayyar kwalta. Shigowarsu cikin street ɗin ya sa AS sake mata tambayar inda za'a sauketa. A taƙaice ta ce “Nan ma yayi”. Shi dai driver tunda taƙi faɗar no ɗin gidan da zataje ai sai kawai ya samu waje ya tsaya abinsa. Itako ta kama handle ɗin motar ta buɗe da nufin fita. Sai kuma ta ɗan juyi domin ɗaukar kayanta da AA Darma ya amsa a ɗazun akai rashin Sa'a shima ya kawo hannu kan kayan da nufin ɗauke file ɗin daya ɗora kawai ta riƙe masa hannu. Da sauri ta jiyo jin ta kama abu, dai-dai shima yana kallon hannun nasa da yaji an cafke. A tare suka dubi hannun sai kuma suka kalli juna. Maanal ta saurin yarfar da hannun tamkar wadda ta kama wuta, yayinda shi kuma ya wani irin dunƙule hannun nasa waje guda tare da dimtse lips ɗinsa da hakori tamkar zai kai naushi. Sauka Maanal ɗin tayi tare da zare kayan nata ta ajiye masa file ɗin batare data sake gigin kallon ko inda yake ba taima AS godiya da driver tai gaba abinta ko waiwayen motar bata sake yi ba. Shima driver sai kawai ta tada motar suka wuce.
       Tunda suka tafin AA Darma hannun nasa kawai ya zuba ma ido tamkar mai karanta wani abu a jikinsa ko cigaba da ganin hannun Maanal ɗin. Kamar ance ya kalla inda ta tashi idonsa ya sauka akan ɗan abin hannunta da alama wajen yarfar da hannu da tai sanda ta kama nashi ya cire batare data kula ba. Hannu ya kai a hankali ya ɗauka ɗan hannun ya juya. Mai ƙyau ne sosai kalar golden, an masa kwalliya da fararen stones, da gani ba wani mai tsada bane, amma yayi ƙyau sosai. Yanda ya tsirama ɗan hannun ido yana kalli da jujjuyashi haka su AS ke kallonsa zuciyarsu cike da gulma, suna ganin zai ɗago suka kama kansu. Shi ko a cikin aljihun jacket ɗin suit ɗinsa na ciki ya cusa ɗan hannun kawai ya gyara zamansa......

      Ni dai nace, “Hummm. Idan tayi wari dai maji🤪🏃”.

_____________★
Chapter 46 · 0% Book details