Sashe 17
Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da mamaki Amrah ke kallon RK, har dai ta kasa haƙuri sai da tayi magana. Murmushi yay mata da tambayarta ya gajiyar biki. Hakan data faru tsakanin Amrah da RK sai ya tsayama Yazeed a zuciya har sai da ya kira Amrah ɗin gefe ya binciketa. Kanta tsaye ta sanar masa abinda ta sani. Yayi mamaki ƙwarai da gaske. Haba no wonder yake mamakin yanda RK ɗin ke tsaye very serious akan case ɗin Manaal ɗin. Ya jima yana son haɗa al'amarin a ransa amma ya gaza samun makama, tunda shi dai sun fitone kawai suka samu motar RK ɗin a ƙofar gida, daga wannan taimakon kuma na kawosu asibiti baiyi tunanin cigaba da ganinsa ba amma sai yaga ya tsaya tsayin daka komai anayi da shi, yayi tunanin kawai tausayi da taimakone sai da aka dawo Abujar nan ya ɗan fara zargi a ransa sai kuma dai yay saurin kaudawa tunda bashi da tabbas musamman ganin RK ɗin matsayin likita shima. Ashe kuwa hakanne.
A ranar su Amrah suka koma Kaduna harda Hajiya Basariyya data wuce bisa tirsasawar Daddy dan kuwa badan taso ba, taso ace sai taga kwal uwar daka. Ta zata da Daddyn zasu tafi sai yace mata shi yana nan har sai yaga yanda hali yayi akan jikin Maanal ɗin. Hakan ya masifar ƙona mata rai, dan ta kalla abunne a sigar rainin hankali irin na maza kawai. A ganinta Daddyn nason holewa da Ammie ne a wannan ƙayataccen gida shine ya fake da ciwon agola. Ita Ammie tsaf ta fahimci manufar Hajiya Basariyya ɗin, amma sai ta basar kawai tama dinga ƙarfafa Daddy ɗin akan yaje suma suna da hakki a kansa, tunda dai Maanal ɗin tana samun dukkan kulawa anan ɗin gasu kuma ga Yazeed shi yaje ya huta gashi ya dawo daga tafiya. Sam Daddy ƙin saurararta yayi, daga ƙarshe ma ya fara fushi da ita dole tai shiru ta zuba masa ido kawai su Hajiya Basariyyan suka wuce...
A ɓangaren Yazeed kuwa ya fara janye jikinsa daga RK. Tun RK ɗin bai fara fahimta ba har ya fahimta. Dan sai wani isa ma Yazeed ke nuna masa akan Maanal ɗin yanzu da gadara. Mamaki hakan ya bama RK, dan shi a zatonsa Yazeed da Maanal uwa ɗaya uba suke ko uba ɗaya dan yana ɗan tantamar Ammie ta isa haihuwar kamar Yazeed ɗin. Bai daiyi magana ba yabar abin a ransa dan ganin iya gudun ruwan Yazeed ɗin. Ana cikin wannan dambarwa a tsakaninsu Hajiya Majdiya yayarsa tazo duba Maanal ita da yaranta tun daga Zaria. Dan shine ya kirata yake sanar mata, aiko baiwar ALLAH sai gata tazo. Ammie tayi mamakin hakan kasancewar batai waya da Hajiya Majdiya ɗin ba akan hakan. Sai Hajiya Majdiyan ke sanar mata, “Sirikinki ne ya kirani yake sanar min ai.”
Murmushi Ammie tai da faɗin, “Haba nayi mamaki fa, sai kuma hankalina bai kawo nan ɗin ba. Ai babu abinda zamuce da Rafeeq sai fatan alkairi. ALLAH yay masa albarka”.
“Amin ya rabbi. Yaya jikin nata yanzu? Dan naga hankalinsa a tashe yake matuƙa yau har cewa yay na nema masa masu saukar Alkur'ani yana son ai mata”.
Ajiyar zuciya Ammie ta sauke. Zuciyarta na sake jin nutsuwa da RK ɗin. “ALLAH sarki, ALLAH ya saka masa da alkairi. To Alhamdullahi zamu ce. Sai dai har yanzu bata san wanda ke kanta ba. Amma dai suna tabbatar mana bugun zuciyarta na dai-daita zuwa yanzu. Kowane lokaci kuma zata iya farfaɗowa cikin hayyacinta.”
“ALLAH ya bata lafiya, yasa ya zama kaffara. Abin tausayi yarinya ƙarama haka da wannan irin babban ciwo mai haɗarin gaske, ALLAH ka bamu ikon cinye jarabawoyinmu. Shiyyasa gata nan sanyi-sanyi ko kuzarin kirki bata da shi. Ban taɓa sanin tana da wannan lalurarba ai da tuni na haɗaku da Rafeeq ɗin dan aikinsa ne. Yanzu haka reshen wannan asibitin suka buɗe acan garin jos shine yaje can da kansa yake riƙe da asibitin kusan shekara ɗaya kenan, anan ne ma ALLAH ya haɗasa da ita”.
Murmushi Ammie tayi tare da jera addu'a ma RK ɗin. Ganin yanda Ammie ta ɗauki zancen da muhimmanci Hajiya Majdiya ta cigaba dama ɗan uwanta campaign wajen Ammie. Yinin gaba ɗaya suna a tare sai bayan Magrib RK ya ɗaukesu ya maida can gidan babbar yayarsu dake nan Abujan zasu kwana anan dan sai gobe idan ALLAH ya kaimu zasu koma Zaria. Sosai Ammie taji daɗin kasancewa da Hajiya Majdiya a wannan rana. Dan zaman ya sake tasirantar da abinda take ji a zuciyarta game da RK da Maanal idan har ALLAH ya tashi kafaɗunta. Bata ɓoyema Nene da su Shahidah ba akan alaƙar Dr Rafeeq ɗin da Maanal. Suma sai abin yay musu daɗi matuƙa, dan suna ganin idan har ALLAH ya baiwa Maanal lafiya wannan itace hanya mafi sauƙi da maganar Yazeed zata janye cikin sauƙi batare da sun ɓata ran Daddy ba kamar yanda duk suke gudu. Dan gwara dai a haƙura da batun Yazeed ɗin nan haka nan tunda dama ita wadda ake dan ita bawai tana sonsa bane. Abu na biyu sudai a haka yanayin Dr RK ya musu hundred percent, dan mutum ne mai sauƙin kai ga girmama na gaba da shi, ga yanda yake ɗawainiya dasu a asibitin nan cike da mutuntawa ma abin a soshi ne. Shi kansa Daddyn sun fahimci RK ɗin ya shiga ransa. Sai dai babbar matsalar sun san ga Yazeed za'a sameta kam. Dan kowa yasan Yazeed na matuƙar son Maanal wannan a bayyane yake. Sannan shi kansa mutumin kirki ne, dan yana da nagartattun halaye masu yawan gaske daya gada ga Daddy, tako ina Yazeed ya cancanci zama mijin Maanal kodan halaccinsa garesu, dan hatta Daddy ya sansu ne a dalilin Yazeed. Sannan kodan Daddy a bama Yazeed auren Maanal, mahaifiyarsa ce kawai matsalar gaskiya, dan Hajiya Yaya sam ba kanwar lasa bace. Bata da kirki ko misƙala zarratin, kanta kawai ta sani, kuma tabbas zata iya aikata komai akan wannan auren kamar yanda take shan faɗa idan har akayisa. ALLAH dai ya bama Maanal ɗin lafiya, zasu cigaba da tayata addu'ar zaɓin alkairi dan duk MAZAJE biyun nan sun matuƙar cancanta da aurenta...
★ A mota Hajiya Majdiya ke bama RK labarin hirarrakinsu da Ammie, babu abinda yake sai murmushi da ƙara jin ƙaunar ƴar uwar tasa. Sai da ta gama bashi labari tsaf sannan ya jeho mata tambayar abinda ke cimasa zuciya..
“Humm Aunty Alhamdullah na samu karɓuwa wajen Ammie da ƴan uwan Maanal, sai dai ba duka ba”.
“Kamar ya ba duka ba miye matsalar to?”.
“Yazeed Aunty, Yazeed shine matsalar kuma na fahimci yana da ƙarfin faɗa aji akan ƴan uwan nasa. Da farko dai ni da shi normal gaskiya. Amma kwana biyun nan ban san miyyasa ba ko ya fahimci alaƙata da Maanal ɗin sai naga yana jajja baya dani, sannan yana min gadara da al'amarin Maanal ɗin. Dan ma baida yanda zaiyi ne kasancewata ɗaya daga cikin likitocinta shiyyasa. Har abin ya fara bani mamaki dan kamar wani mai kishi da ni. Sai dai nasan ba hakan bane tunda mizai sakashi yin kishi akan wadda suke Uba ɗaya ne ko uwa ɗaya ma ban sani ba”. Ya ƙare maganar cikin damuwa sosai.
Fuskar Hajiya Majdiya cike da damuwa itama ta furta, “To kodai Yazeed ma son Maanal yake?”.
“What?!!!”..
RK ya faɗa a ɗan razane yana taka birki da sauri.........✍️
🤣Sai ka ɓarar daku malam Rafeequ
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖1️⃣3️⃣
______________
Abubuwan da nake saidawa
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries