← Book details Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 148

Sashe 34

Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖2️⃣4️⃣

.........Wata irin ajiyar zuciya director Mustapha ya saki. Sai kuma ya saki murmushi a ransa yana mamakin kansa da ɓoyema Doctor Rafeeq ɗin sauran gaskiyar abinda ya faru da yay... Kirane ya shigo daga landline ɗin office ɗin, ganin daga office ɗin CEO ne ya sashi saurin ɗagawa. AS ne ya sanar masa CEO na buƙatar ganinsa yanzun nan, kuma ya taho da file ɗin sabuwar staff ɗinsu. Bai wani tsaya wasa ba ya miƙe yana dariya. A fili ya furta, “Anya babu wata a ƙasa akan yarinyar nan kuwa? To madai ji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta”.
       Sai da AS ya shiga yay masa iso sannan ya shiga. A yanzu kam AA ɗin na zaune ne a kujerarsa ta aiki saɓanin a yanda RK ya samesa ya kuma barshi. Gaisuwa Director Mustapha ya miƙa daga tsayen batare daya zauna ba. Shima AA ɗin da hankalinsa ke kan computern desk ɗin batare daya amsa ba yay masa nuni da vesitors chair ɗin gaban desk ɗin kawai. Zama yay, kafin cikin girmamawa ya ce, “Gani Sir. Dama ina ƙoƙarin ƙarasa haɗa komai ne na kawo sai kuma ga kiran AS akan kana son ganina”.
      Shiru bai amsa masa ba, yanata aikin gabansa kawai har lokacin hankalinsa nakan screen ɗin computer ɗin, sai da yaja kusan mintuna uku kafin ya ajiye tare da maido hankalinsa kan Director Mustapha ɗin. “Am sorry ina wani abune”. Ya faɗa cikin muryarsa mai zurfi. Da sauri Director Mustapha ya ce, “Babu komai Sir”.
     Kansa kawai ya jinjina masa. Sai kuma ya miƙa masa hannu alamar ya basa file ɗin. Miƙa masa yay da sauri cikin girmamawa. Yayinda shi kuma ya shiga buɗesa yana duba komai daki-daki. Sai zuwa can ya ɗan ɗago. “Baku ƙarasa bane?”.
        “Eh sir! Saboda kana fita itama ta miƙe ta fice muna ƙoƙarin tsaidata amma bata sauraremu ba. Mun cigaba da abinda ya dace ne kawai saboda ka bada umarnin hakan. Dan mu harma mun fara tunanin ko tanada wani c......”
    Muƙutt ya haɗiye zancen saboda wani shegen kallo da AA ɗin ya jefa masa. Sai kuma ya duƙar da kansa yana shashshafa ƙeya. Shiru office ɗin ya ɗauka na kusan minti biyu kafin yay masa nuni da hannu alamar yaje. Miƙewa yay tare da ɗan rissinawa na girmamawa sannan ya fice a office ɗin.....

Duk yanda yaso cigaba da aikin zuwa lokacin break hakan ya hagaresa. Dan wani irin zazzaɓi ne ma ke neman rufesa. Ga ciwon kai. Dan hatta fararen idanunsa launinsu ya canja zuwa jaa sosai alamar akwai wani abu dake damunsa. Sai dai sam fuskarsa bata nuna komai.
Kwanciya yay a office ɗin bayan dawowa sallar azhar, kamar wasa zazzaɓi mai azabar zafi ya rufesa, ga wani irin sanyi da yake ji. Ya kulle kofar tare da ma AS gargaɗin baya buƙatar kowa. Hakan yasa ko lokacin Asr AS bai masa knocking ba dan yasan ogansa baya wasa da salla. Ganin har biyar na yamma lokacin ma'aikata sun fara tashi babu alamar zai fito hankalin AS ɗin ya fara tashi, ya dai daure dan yasansa da iya yin over work. Kamar wasa har magrib companyn yayi shiru sai securitys. Dole fa yaje ya fara masa knocking amma shiru kake ji wai malam yaci shirwa. Hankali tashe AS yay kiran wata number, bayan an ɗaga yayi gaisuwa cikin girmamawa ya sanar da halin da boss ɗin nasa ke ciki. Banji mi aka sanar masa ba, sai dai ya amsa da girmamawa yana sauke wayar. Yana nan yana faman kai-kawo a bakin ƙofar sai ga wani nutsetstsen mutum da zai iya kaiwa shekara arba'in haka. Sosai yake kamanni da AA ɗin, hatta da rashin yawan fara'ar fuska kamar AA ɗin dai. Gaisheshi AS yay da girmamawa. Ya jinjina masa kai yana amsawa, sai kuma ya fiddo wani ɗan card a aljihun jallabiyarsa fara ƙal ya goga a jikin handle ɗin ƙofar. A take kuwa ta rabe gida biyu ta buɗe. Gaba ɗaya an kashe wutan office ɗin, hakan ya saka gabansa faɗuwa, dan sun san minene ganin AA a duhu yake nufi, wayarsa ya zaro ya kunna fitilar, hakan ya bashi damar ƙarasawa ga makunan fitulun office ɗin ya kunna. A take haske ya gauraye ko'ina. Idanunsa suka sauka akan AA dake kwance a kan sofa. Cike da sassarfa ya ƙarasa garesa yana kiran sunansa, amma shiru babu allamar zai amsa, har ya zauna a saman table ɗin gaban sofa ɗin tare da kai hannunsa saman na AA daya dafe kai da shi, hannun ya janye a hankali ya maye gurbinsa da nashi, sai da gabansa ya faɗin jin wani irin hucin zafi, sanyin hannunsa yasa AA buɗe manyan oily idanunsa gently, sunyi wani irin mugun kaɗawa jazur, sam babu hasken nan mai kama da madara a cikinsu yanzu, sai ƙyallinsu daya sake saka jan yin bauuu. Ga kuma jijiyoyin kansa da suka sake fitowa ruɗu-ruɗu....
“Ya arrahaman Auta! Baka da lafiya amma kazo nan ka kwanta? Are you mad da baka san muhimmancin lafiyarka bane?”.
Maimakon amsa masa sai AA ɗin ya maida idanun nasa kawai ya sake lumshewa. Tsaki mutumin yaja tare da miƙewa ya tada AA ɗin shima. “Oya get up and go home?”.
Bai masa musu ba ya miƙe ɗin, haka ya kamashi suka fito yana bama AS da hankalinsa ya tashi da ganin halin da boss ɗinsa yake ciki umarnin tattaro abubuwan AA ɗin. Cikin sauri ya amsa shi kuma ya wuce da shi......

_____________★

       A hankali yake juya steering kamar baya so. Yayinda gaba ɗayan hankalinsa ke akan al'amarin Maanal. Yama rasa yaya zai fassara lamarin, musamman a yanzu daya koma Maawad yaji komai daya faru. Shin murnar samun aikin ce ta sakata kukan? Ko kuwa mike faruwa?. Rashin mai bashi amsa ya sashi ɗaukar hanyar gidan Shahidah, dan gaskiya yana buƙatar ganin Maanal ɗin. Ya ɗan yi nisa da tafiya kira ya shigo masa. Kamar bazai ɗauka ba sai kuma dai ya ɗauka saboda ganin abokin aikinsa ne na asibiti. Neman gaggawa ake masa zuwa asibiti yanzun nan, dole yay reverse zuwa asibitin dan yanda yaji Doctor ɗin a rikice yasan akwai babbar matsala. Kafin ya isa kiran wasu doctors biyu ƴan uwansa ya sake shigo masa. Dole ya ƙara gudu cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya iso.....

        _________★
Chapter 34 · 0% Book details