← Book details Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 148

Sashe 146

Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

         Ranar juma'a jirgin ƙarfe goma suka bi zuwa Kano. Kowa ka gani a cikinsu sam babu walwala a tare da shi. Sai ma AA ɗin ne ke ɗan nuna dakiya. Sai dai a kallo guda zaka fahimci yanda yay wata irin zabgewa ta rama a tsaye. Sai manyan idanunsa da suka sake fitowa fatarsa ta sake haske ga gashin fuskarsa ya fara taruwa fiye da yanda yake barinsa dan yaƙi yay gyaran fuska. Shi kaɗai yasan irin dogon gargaɗin da yasha akan Mamy a safiyar yau da daren jiya. Shi yanzu al'amarin mahaifiyar tasu yama daina bashi mamaki ko tsoro. Abinda kawai bata sani ba ko bata cigaba da takurashi da gargaɗin ba a shirye yake ya mata biyayya koda kuwa hakan ne zai zama ƙarshen rayuwarsa. Dan shi ya sani a wannan gaɓar babu kuma abinda ya rage masa a wannan rayuwar sai jiran mutuwar.
     A gefe kuma Oum sai dama-dama take da shi. Tun daga jiya zuwa yau sai faman lallashinsa da lallaɓashi take akan batunsa da Maanal ya sanar mata ko akwai wani abu da basu san da shi ba ne. Baya son tada mata da hankali, dan haka murmushi kawai yake mata yace ta kwantar da hankalinta ALLAH na tare da kowa. Duk da bata fahimci abinda yake nufi ba ita dai lallaɓashi take yi akan in sunzo koda an tambayesa ya faɗi yana da wadda yake so. Dan ita bata ɗauki wani batun kai kuɗin Rafeeq gidan su Maanal ɗin da muhimmancin da zai hana komai ba. Kawai gargaɗin Abah ne ma ya hanata kiran Rafeeq ɗin ta masa tas, dan yaja mata dogon gargaɗi akan hakan. Shi kuma Rafeeq ɗin kamar yasan abinda ta shirya masa yaƙi komawa Abujan. Ko waya yaƙi kiranta ma.
      Mahmud da Hassan ne sukaje ɗaukarsu a airport. Koda suka iso gidan Baba Sardauna sun samesa cike da dukkan ahalinsu. Dan kamar ma su kaɗaine basu kai ga isowar ba sai Gwaggo Khadi data taho daga Yola. Dan sai da sukai kamar awa ɗaya ma sannan itama ta iso da tata tawagar. Itama dai bayan Mahmud data mallakama Baba Sardauna a wancan lokacin tana da yara biyar a yanzu. Uku maza, biyu mata. Mazan biyu sunyi aure. Hamza da Lamiɗo. Sai Nuwaira da Raihana. Sune ƴammata da take damuwa da rashin yin aurensu. Sai autanta Abdullahi, shi kam da sauransa. Koda yake koshi ɗin yanzu akama auren zama zai yi da matar sumul.
      Tuni an kacame da hirar zuminci a ƙaton falon gidan Baba Sardauna da dama an tanadesa domin irin wannan haɗuwar. Ƴaƴa da iyaye anata zabga hira cike da farin ciki. Akwai irin AA marasa yawan magana a cikinsu, amma idan akai irin wannan haɗuwar kakanji bakin kowa ya buɗe. Hatta shi AA ɗin yakan ɗan saki jiki kaɗan. Sai dai yau tunda aka gama gaisawa yama zame jikinsa yabar falon. Sai da Oum ta farga baya nan ta fara jajensa. Sai Modibbo ke sanar mata ai yana waje yana waya, jin haka yasa ta cigaba da hirarta, duk da rabin hankalinta na kansa, wani kuma tsagi nakan rashin ganin Rafeeq. Wasa-wasa AA bai dawo falon ba sai da za'a fara meeting. A lokacin ne kuma Rafeeq shima ya iso tare da Abbu, dama shima bai kai ga isowaba. Alhaji ƙarami da Mah-mah ne kawai sai Rufaidah. Bayan addu'a ga wanda suka rasa da kuma su da suke raye aka fara abinda ya tara kowa. Nasiha ce mai ratsa jiki Baba Sardauna ya fara sannan ya tafi kai tsaye kan abinda yasa su tara wanan taro na gaggawa. Ba komai bane face auren da suke son ƙullawa. Maganar Rafeeq itace farko, Baba yay bayanin sun riga sun kai kuɗi kuma an amsa nan da sati uku biki, dan haka zasu haɗe da sauran suma ayi a huta kawai. Amma an bama AA da Najeeb da su Nuwaira dama idan suna da wanda suke so su faɗa. Da Najeeb aka fara kasancewar uba a wajen su AA ɗin. Kansa a ƙasa yace shi baida wacce yake so, amma su ƙara bashi lokaci zai kawo. Baba Sardauna yace Sam bashi yiwuwa, babu wata dama da zasu ƙara basu, ya zaɓa a cikin ƴaƴan dangi gasu nan. Rasa abin cewa Najeeb da ransa ya gama ɓaci yayi, sai kawai yace shike nan ya basu dama kowacce suka zaɓa masa. Albarka aka shiga saka masa. Kafin aka koma kan AA. Sarai yana kallon irin kallon da Oum ke masa, hakama Mamy, hakama Yaya Fawzan da Babban Yaya. Abah ne kawai baya hangowa da ƙyau. Amma duk sai ya ture komai cike da dakiya yace shima ya basu dama duk wadda sukaga ta dace su bashi. Da ƙarfi Oum ta runtse idannunta, yayinda Fawzan kema AA wani irin kallon takaici da jin haushi. Mamy kuwa murmushi ta saki tare da sauke ajiyar zuciya a cikinta. Dan tasan dai zaɓinta data ba su Baba Sardauna zasu bashi. An koma kan su Nuwaira sukace suma sun bada zaɓi.
     Sai dai me, bayan an sakama AA albarka shima buɗar bakin Baba Sardauna sai cewa yay, “To Alhamdullahi, munyi farin ciki da wannan biyya taku. Dan haka bama sai anje da nisa ba. Mun yanke shawarar haɗa auren ku ku huɗun lokaci guda, zakuma muyi amfani da ranar Rafeeq da aka tsaida dan ayi a wuce wajen. Tunda ku dukanku ba muhallin zama kuka rasa ba. Babu kuma wanda bai da abinyin da idan yau akace za'ayi nasan zaku shiga ku fito. Balle ma bama buƙatar komai daga kowanneku, ku shirya tarbar matayenku kawai. Magana ta ƙarshe akwai zaman da mukai shekaru uku da suka wuce a wannan falon game da Ajwaad na auren yarinya da aka bashi wadda ta fito daga ke ɓangarenki Kamila”. Da sauri Mamy ta kalla baba Sardauna ranta fal farin ciki amma tana ɓoyewa. Cigaba yay da faɗin, “To ban manta ba, dan haka zamu tuntuɓi iyayen nata in sha ALLAHU. Sai yarinya daga Kaduna da ƙanin mahaifinyarta da kansa ya kirani itama yazo da batunta akan tarayyar su da Ajwaad ɗin dai suka kuma bamu damar zuwa tsaida magana itama in har ya shirya zamuje ayi magana tunda shi da alama da mata biyu zai fara, ya nuna mana duk ya fimu gwarzantaka har mu dake iyayen naku”. Yanda yay maganar da ƴar raha ya saka wasu yin dariya. Yayinda mamaki ya gama lulluɓe wasu, Ajwaad ne wai da auren mata biyu lokaci ɗaya, duk wannan jin kan nashi tab ɗin. Oum kam suman zaune tayi, burinta su haɗa ido da AA amma yaƙi yarda. Haka Abah da su Babban Yaya ma. Ran Mamy kam fes. Haka dai akai addu'a taro ya tashi.........✍️

_Humm wlhy kuna bani dariya da yanda kuka matsu da al'amarin Mamy dama sauran mutanen da mukema kallon ƙalubale a wannan labarin. Shin wai mun taɓa ganin rayuwar da babu ƙalubale a cikinta ne?. Ni da ku mu koma cikin rayuwarmu mu kalla mana, itafa rayuwa gaba ɗayanta ma jarabawace, mukance ai rayuwa rayuwace, rayuwar novel kuma rayuwar novel ce kana karantawa ne dan nishaɗi da farin ciki. Eh hakane kam banyi musu ba, amma mu sani mutane da yawa na ɗaukar darasi da fahimtar tasu rayuwar a dai wannan rayuwar novels ɗin da mukema kallon nishaɗi da labarin hikayoyi kawai. Da ace labarin akan soyayyar su AA da Maanal ce kawai, ƙalubalen rabuwar ma bazai shigo ba, Sai kawai suyi rayuwar ƙurciyarsu suyi aure shike nan miya rage. To koma ita kanta soyayyar ai duk daɗinta ƙalubalen cikinta yafi yawa koda a zahirin ne. To amma ni akwai saƙon da nake son isarwa a labarin gaba ɗayansa. Idan kukai haƙuri za'akai fiye ma da inda kuke tunani. Ka aikata alkairi ma yaka ƙare balle akasinsa a wannan rayuwar. Dole ne mu yarda akwai farin ciki, akwai kuka a rayuwa. Duk yanda muke tunanin mu masu gaggawane duk gaggawarmu muna tafiya ne bisa zartarwar hukuncin UBANGIJI. Dan haka dan ALLAH ku barni na isar da sakon da nake son isarwa dan masu buƙatar hakan su amfana. Ni da nake wahalar rubutun da hana kaina barci da wasu muhimman abubuwan rayuwa nafi ku ƙagauta naga nakai gacci, dan banƙi na runtse ido naga na kammala ba. Fatan alkairi a gareku baki ɗaya🙏_

_Maanal kuma sai Uncle RK ko Abuja babu kowa ehe🤪🏃🏃🏃_

09032345899

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖9️⃣5️⃣

______________
Chapter 146 · 0% Book details