← Book details Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 148

Sashe 110

Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Sosai Giro tama Ammie zafi, zafi mai tsanani ita da yaranta. Dan haka ta roƙi Baabu komawa Kano. Da farko ya turza, saboda gwaggo ta sakashi a ɗaki ta kitsa masa cewar yabar Ammie ta cigaba da zama anan Giro. Itako a karo na farko tattara kayanta tsaf dana yaranta washe gari ya fita shi da amaryar tasa da Gwaggo zuwa can gidansu wai babanta babu lafiya ta baro Giro bisa taimakon Baba Haruna. Taso ta kwana a kabbi. Sai dai rashin mukulli dan yana a hannunsa yasa haka suka fallo hanya. Cikin amincin UBANGIJI suka iso cikin Kano kusan tara na dare. Sai da suka shiga gida ta kira Oum ta sanar mata. Sosai Oum tayi mamaki, amma sai ta ture mamakin ta kwantar da Maanal datai barci a jikinta ta fita. Kitchen ta shiga ta haɗa musu abinci sannan ta kira Abah a waya Fawzan ya mata rakiya.
     Sosai hankalin Oum ya tashi da ganin yanda duk Ammie ta rame ta lalace. Gashi suna haɗa ido kawai Ammie ta sakar mata kuka. Jiki na rawa ta ajiye abincin ta rungumeta tana lallashi. Sai da tayi kukan sosai sannan Oum tace ta tashi tai wanka. Wankan duk sukayi sukaci abinci, sannan Oum da Fawzan suka koma gida. Damuwa fal kan Oum. Washe gari rijib Ammie ta tashi da ciwo, dole suka wuce asibiti. Aiko aka basu gado dan likitocin sun tabbatar da jininta ya hau sama matuƙa. Sai da Ammie tayi kwanaki huɗu sannan aka sallemta suka dawo gida. Washe gari cikon na huɗu sai ga Baabu da amarya sun iso. Ammie batayi mamaki ba, kuma batace komai ba, duk da taga da wani wutar bala'i da rashin mutunci yazo garin. Dan babu kunya ya rufeta da zagi harda mari wai ta taho bada izninsa ba, ta raina masa mahaifiya miye-miye. Ko ci kanka batace da shi ba, hakan sai ya dake hasalashi ya fara nemo hanyar da zai musguna mata ta mangantu ya juye mata abinda ke a ransa. Ɗaki uku ne kacal a gidan, nata, nashi, sai na yara. Haka ya murje ido yace ta koma na yaran ita amarya ta zauna a nata. Ammie ta ce wannan ne kuma bai isa ba. Dan ita ba wulaƙantacciya bace, ba gori ba gidan nan mallakinta ne idan ya manta tunda da kuɗinta aka sayeshi. To dama fa ta samu, haka Baabu ya dinga zuba tijara har sai da Abah yazo ya fiddashi a gidan aka samu masalaha. Daga ƙarshe dai dole amarya ta zauna a ɗakin shi.
     Tun wannan dawowa komai ya canja, canji mai ban mamaki daga ma'auratan dama gidan kansa. Musamman daga Baabu. Hatta ƴaƴansa yanzu ja baya suke da shi, dan abu kaɗan zakayi ya hauka da zagi. Ranar ma ƴar lelen tashi Maanal har duka taci, aiko ta haɗa inata-inata ta koma gidan Abah. Tafi sati bata shigowa gidan nasu kafin ta saki jiki kuma ta manta bisa tirsasawar Ajwaad ta koma shigowa. Ga amarya dai babu wata matsala. Ta kwantar da kanta yana fahimtar komai daki-daki kamar babu komai. Sai dare ta ishesu da ihu ita da miji. Wannan abu shine mafi girma tadama Ammie hankali, dole ta maida kwanan su Shahidah gidansu su Oum gaba ɗaya. Dama yanzu batun miji Ammie bata da shi a gidan, Baabu yana tare da amaryarsa tunda suka dawo. Sai da suka cika wata ɗaya cif sai gashi da takarda wai ya saki Ammie saki ɗaya.
       Murmushi kawai Ammie tayi da faɗin, “ALLAH yasa haka shi yafi alkairi, amma kuma babu inda zanje. Zan zauna na cigaba da rainon ƴaƴana har lokacin aurensu sai dai kai ka bar min gidan tunda dama nawa ne”.
     Wannan furuci nata shine ya kawo tashin hankali, tashin hankalin da dole sai da Abah da Oum suka shiga yanzu ma. Da ƙyar dai aka sasanta bayan Abah ya nusar dashi illar abinda yake shirin aikatawa. Shine fa ya maida Ammie. Haka aka cigaba da haƙuri Ammie bata da miji, bata taɓa tada kai ta kallesa ba har tsawon shekara biyu. (Kenan dai tun da amarya ta tare😭) Ko'a fuska Ammie bata nuna masa damuwarta, karatunta kawai take na Islamiyya da take zuwa da kula da tarbiyyar yaranta da sana'arta. Dan takai yanzu ma itace ke ciyar da kanta. Zuwa yanzu su Maanal fa an shiga secondary, Dan suna aji biyu ma duk da da ƙyar suka amsheta saboda sunce tayi ƙarama da yawa, yayinda Shahidah ke shirin kammalawa ita da Fawzan, babban yaya kuwa ya wuce ƙasar Saudiya karatu.
          Amarya bata shiga sabgar Ammie, itama bata shiga tata, dan a zahiri bata da matsala da ita sai da Babu, sai dai tushen matsalar daga gare ta ne tazama macijin sari ka noƙe ne kawai. Har lokacin kuma dai babu ciki, sai da ta shiga shekara ta uku sai ga ciki, nan fa su Babu aka shiga murna da addu'ar haihuwar ɗa namiji. Ita dai Ammie ko tari bata musu ba, duk taɓarar iskancin da amarya keyi bata nuna tasan suna numfashi a gidan ba ma. Sai da ciki ya shiga wata biyar sannan ya ɗauketa suka wuce Giro, dawowar da basu sake yi ba sai da ta haihu akasha shagalin suna a Giro dan buri ya cika an haifi Namiji. Ashe duk wannan abun da ake Baabu na cikin Kano, tunda ya kai amarya gida Gwaggo ta sharɗanta masa hanashi komawa wajen Ammie wai har sai in matarsa ta haihu. Ammie bata taɓa sanin haka ba sai bayan dawowarsu da jinjiri da Gwaggo, wai itama ta dawo nan Kano da zama, ashe aure dai ya ƙare tsakaninta da Baba Haruna duk kuma akan Ammie ne, dan bayan tahowar su Ammie a wancan karon ansha fitina Baba Haruna ya saki Gwaggo shine fa ta ɗau alwashin yanda ya saketa itama sai an saki Ammie, idan kuwa ma ba'a saketan ba sai ta ɗanɗana fiye da abinda itama ta ɗanɗana. Wannan duk shine tushen matsalar da suke ciki a yanzu shiyyasa Amarya data san komai ta koma gefe ta nutsu tana shan kallo dan tace faɗan na manya ne ba nata bane.
      Dawowar Gwaggo Kano ba ƙaramin tashin hankali su Ammie suka shiga ba ita da yaranta. Musamman Maanal mai bakin tsiwa datai matuƙar tsanar Gwaggo, kuma a zahiri take nunawa bata ɓoyewa. Yayinda Gwaggo itama ta tsani Maanal fiye da su Shahidah, ta kuma tsani Ajwaad, dan shima a dalilin ƙin Maanal da su Ammie daya ga Gwaggo nayi ƙuru-ƙuru ya sashi tsanar matar, dan sam Ajwaad baya son mugu da mugunta. Rayuwa tayi tsanani wa Ammie, uwar miji, da miji da kishiya sun saka rayuwarta gaba data ƴaƴanta. Shekaru kusan huɗu bata kwanciya da miji, baya shiga ɗakinta. Yanzu kuma haihuwar namiji tasa kullum cikin aibanta mata yara suke da shegantasu, dan akwai randa Baabu da bakinsa yace yana tantanamar ma su Shahidah ƴaƴansa ne. Wannan abu ya girgiza Ammie, ya sakata kuka mai tsanani da sake jin sabuwar kewar iyayenta data rasa. Amma ya zatai, haka ta haƙura ta share hawayenta ta barma ALLAH komai. A wajen Oum da Abah kawai take samun sauƙi da soyayya da ƙauna ita da yaranta.
         Kammala secondary ɗin Shahidah yasa Abah tada zancen aurenta da Fadeel. Dan yace za'a fara nasu, ita kuma Amaal sai Fwazan ya kammala. A ɗan tsukun Fadeel yazo gida hutu, dama can shi da Shahidah tuni sun ƙulle, dan haka aka saka ranar aurensu ya koma saudia. Bayan komawar tasa Shima Fwazan ya shiga lallaɓa Oum akan kawai a haɗe nasa dana Amaal lokaci ɗaya dana Babban Yaya, sai su tafi jami'ar tare. Dan shi rashin ƙyawun result daya samu yasa dole ya ƙara shekara ɗaya a ƙasa sai da ya canja ssce ɗinsa duka.  Duk da a lokacin ita Amaal na ss2 sai yace kawai tayi exam ɗin itama su wuce tare. Oum ta tunkari Abah da zancen, yay shiru yana nazari, sai zuwa can yace ta bashi lokaci zai yi magana da Baabu, kuma zai kira Baba Haruna a waya....

  ____________★

         Kamar yanda suka saba tashi sallar asubahi kullum yauma hakanne. Saida Fwazan ya fara yo alwala sannan babban yaya ya shiga. Ajwaad shine ƙarshe, sai wani ciccin magani yake. Ya girma sosai a tsaye, dan a yanzu shi da mutuniyar tasa suna js3 ne. Suna shirin tafiya ss. Shekarun girma sun gama bayyana mai, dan har wani ɗan tsigin gemu ya ajiye (kamar jelar tsatso inji Ibro.😂 ALLAH ya gafarta masa da iyayenmu baki ɗaya 🙏).
     Yanda yake tafiya kamar mara laka a jiki ya saka Fawzan sarkin tsokana faɗin, “Wai na Lilly kodai barcin nan bai isheka bane ba?”. Harrarsa kawai ya ɗanyi ya wuce abinsa, dama Fawzan tsokana, Ajwaad miskilanci. Haka suke kullum, sai ya ƙuresa ne yake tanka masa. Juyawa Fawzan yay ga babban yaya dake canja kayansa zuwa jallabiya, shi kam tako ina ya zama cikakken saurayi, ga cikar kamala da nutsuwa ta sake baibayesa,  duk da shima Fawzan ɗin tsokanar ce kawai, amma a nutsensa yake. Har sun kammala shiryawa yau ma Ajwaad na cikin bayi, babban yaya ya dubi fawzan da faɗin, “Wai mike damun auta ne yanzu?. Da babu wanda ya kaishi himma shirin fita sallar asuba, amma tunda nazo garin nan naga sai mun fita yake fitowa”.
      Murmushi Fawzan yayi da ɗan sosa kai, sai kuma ya ɗage kafaɗa da faɗin, “Maybe yana wani uzirin ne”.
    “Kamar ya?”.
  Shiru Fawzan yayi saboda fitowar Ajwaad daga bayin a tunaninsa sun fita ɗin. Turus ya tsaya yana kallonsu, suma duk sai suka zuba masa ido........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖7️⃣1️⃣

______________
Chapter 110 · 0% Book details