← Book details Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 148

Sashe 141

Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

    ★A ɓangaren Huznah ma tana can sashen Ammie, hatta Mamy tayi mamakin ganinta, amma sai ta basar. Cike da ladabin daya bama Ammie da su Amaal mamaki take gaishesu, sai wani sissinkuy da kai take. Ita Oum ma bata wani maida hankali a kanta ba, hirarsu suke da Maanal dake jikinta kwance. Dan itama tun shigar su Hajiya Basariyya falon Daddy ta baro can.
     Saheeba dai da Nibras harara suketa antayama Huznah a kaikaice, dama kuma basu tanka ba koda tai gaisuwa. Bayan ficewarta cike da takaici Huznah tai tsaki da faɗin, “Ya akai tasan nan? Ko biyomu tayi ne? Nifa ban san ballagazanci wlhy. Yo ko mata sun ƙare mi Yaya Ajwaad zai yi da ita, balle ma yanada matarsa a hannu. Ai wlhy inaga sai Nuratu ta sake mata wani sabon zanen a fuska zata kiyayi mata saurayi”.
     Da mamaki Oum ta ce, “Ban gane ba, ke ina kika san wannan ɗin Saheeba?”. 
        Batare da Saheeba ta kula kallon gargaɗin da Mamy ke mata ba ta ce, “Oum itace fa wadda sukai faɗa akan Yaya Ajwaad da Nuratu a Abuja”.
     “Ikon ALLAH, ai ni ban ganeta ba sam wlhy. To ya akai tasan nan ɗin?”.
   Amaal da Shaheeda da Ammie mamaki ya gama kashesu, Maanal kam yi tai kamar bata ji mi suke tattaunawa ba. Sai ma karanta saƙon da ya shigo mata a waya take wanda AA ne kuma ya turoshi akan tazo, amma ta masa reply da a (anƙi ɗin). Amaal ce ta bama Oum amsa da, “Oum ai anan gidan take, ɗiyar matar tsakkiyar gidan nan ce”.
         “Oh shiyyasa na ganta a gidan Shahidah kenan. To ALLAH ya rufa mana asiri ”.
   Da Amin kowa ya amsa aka saki zancen. Bayan sun kammala cin abinci ne Ammie da Oum da Hajiya Majdiya da Mamy sai Amaal, Shahidah da Maanal suka nufi sashen Daddy da yay kiran Ammie a waya. Sun samu suma sun kammala cin abinci, dan haka akai zaman gaisawa cike da mutunta juna. Abah nata tsokanar su Amaal. Dan yanda sukai jiki suka zama manyan mata ya bashi mamaki. Hakama yaransu da su Waleed duk suna zagaye da shi yanata sanya musu albarka da musu wasan jika da kaka. Sai da ya gama tsokanarsu yaran suka fito suka bar su Ammie can. Da wannan damar Abah yay amfani wajen bama Ammie haƙuri da neman gafararta akan abinda ya faru a baya. Ya ɗora da faɗin,..........✍️

09032345899

*_ALLAH ka gafartama iyayenm
u 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖9️⃣2️⃣

______________

........“Nasan zakuyita mamaki akan rashin bin bayanku da bamuyi ba a wancan lokacin, a randa kuka wuce a ranar Fateema jikinta ya rikice matuƙa, dan yanke jiki tai ta faɗi, dole muka wuce da ita asibiti, amma sai suka turomu Abuja dan al'amarin nata banbane, paralysis na neman kamata. Tashin hankali yasa bamu tsaya Abujan ba kawai muka fara shirin fita da ita waje da tunanin bazamu daɗe ba zamu dawo sannan gwaggo ta huce, ashe wasa farin girki, dan shima Ajwaad sai ciwo mai ban tashin hankali ya samesa, ga depression. A haka suna cikin jiyyar su duka biyun Fateema ta matsa ni da Fadeel muka taho Nigeria domin ku, kai tsaye kuma Giro muka nufa, amma sai muka samu cewar wai ai suma sun wayi gari kun gudu, kuma an sanar dasu a majiya mai ƙarfi kuna dangin mamanki ba kuma a ƙasar suke ba. Bamu da wani dalilin ƙin yarda da su, dan haka muka juya muka koma. Amma Fateema naji tace ƙaryane, baki da wani dangi a ƙetaran Nigeria, ta sake tada hankalinta har takai jikinta dana Ajwaad yayi rikicewa mai ban tsoro, dan Ajwaad akwai daren da ma har mun gama yarda ya rasu, sai kuma ya farfaɗo gabannin asuba. Sai da akaita tausarta tare da mata alƙawarin a hankali zanta bincikenku sannan,  muka maida hankali akan Ajwaad kuma. A lokacin ne kuma aka bani ambassador, shiyyasa bamu dawo Nigeria ba, amma inata ƙoƙarina batare data sani ba akan neman ku. Sai dai kuma ALLAH bai ƙaddara ba sai a dalilin samuwar aikin Maanal a kamfanin Ajwaad ta dalilin Rafeeq. Dan ALLAH mu yafi juna Asiya, mu ɗauka dukkan abinda ya faru ƙaddararmu ce babu mai canjata. Mu dawo da zumincinmu tamkar a baya can.”
       Hawayen dake gudu a fuskarta Ammie ta share. Ta ce, “Babu komai Yaya komai ya wuce. Ni dama ban taɓa ƙullatarku ba wlhy. Sannan ban san ma Maanal a ina take aiki ba dan basu sanar min ba. Da tun kafin kuzo nan ma nice zanzo gareku, ban dan Rafeeq nada alaƙa da ku ba shi da Maman Najma. ALLAH ne kuma bai ƙaddara haɗuwar tamu ba shiyyasa, tunda gamu tare da Majdiya fin shekara huɗu”.
      “Ikon ALLAH ai yafi gaban wasa. Wannan wata hikima ce ga UBANGIJI mai ɓoye al'amura ta yanda yaso, a kuma inda yaso. Shi kuma yasan dalilin yin hakan garemu”..
Haka ne. Kowa ya faɗa cikin jinjina kai....

_________★

       Da yamma sosai su Abah sukai shirin wucewa, sai dai fa Oum tace suje ita sai gobe in sha ALLAHU. Jin haka AA yace shima ya fasa, ƙafar babarsa ƙafarsa. Wani irin takaici ne ya turniƙe zuciyar Mamy, dan haka kawai take ji a ranta wani abun Oum ke son ƙullawa. Sai kawai catai ai itama kuwa tana nan ɗin. Sam babu wanda ya kawo komai a ransa a tsakanin Oum da Ammie, sai AA ne yay wani iri. Daga baya kuma yace to kawai shi bari ya bisu. Yana ganin hararar da Mamy ke masa amma ya basar. Nibras kam wani sanyi taji a ranta, dan har hankalinta ya tashi da zaman AA a tsakiyar kuraye biyu da take kallo. Wato Maanal da Huzna😂, yayinda Huznah da keta dama-dama da AA ɗin taji kamar tayi kuka. Haka dai babu yanda ta iya suka wuce. Dama Maanal ko'a kwalar rigarta, sai ma hirarsu suke da Fawzan....

        Da daddare akai gagarumar dinner ɗin datai tsawa da amsa kuwa a garin na Kaduna kamar yanda su Hajiya Sabuwa sukai fata. Yau ma su Ammie sunje, kuma harda Maanal. Inda rigima taso tashi a hall ɗin, saboda matsawar Hajiya Majdiya Maanal da su Shahidah sukaje yima amarya da ango liƙi. Aiko Yaya Yazeed ba kunya Maanal na liƙa musu kuɗi yana liƙa mata, sai kawai abokansa ƴan neman magana suka taso suka rufe Maanal da liƙi aka daina liƙama amarya. Nanfa masifa ta tashi, Aunty Sabuwa da Hajiya Yaya suka miƙe zuwa wajen. Wani kalar fisga da Hajiya Yaya taima Maanal kaɗan ya rage tai muguwar faɗuwa ALLAH ya taƙaita Yaya Yazeed ya tareta. Wayyo ina wuta su saka Maanal, nan fa ƙannen Yazeed sukai ma Maanal zobe wai zasu daketa, sai da Oum ta shigo tsakkiyarsu cikin ɓacin rai ta janye Maanal ɗin dan daga ita har Mamy sun halarci dinner ɗin suma. Gaba ɗaya suka bar hall ɗin banda Mamy data maƙale, dan dama damar hakan take buƙata na keɓewa da Hajiya Basariyya....
       Abu kamar wasa tun a daren ƙawayen amarya da ƙannen Yazeed suka dinga posting hotunan Maanal a media suna faɗin maganar banza a kanta. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa abu yayta yawo. Kafin wayewar gari al'amari ya zama babba, dan tunda ahalin su Hajiya Yaya suka dawo daga wajen dinner sabon rikici ya dake ɓalle. Ga amarya an kawo amma bata batunta ake ba. Wannan tashin hankali ya saka Maanal ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazzaɓi. Dole da safe Nene tai shirin wucewa da ita gidanta. Saboda wannan rikici ya zama wani babban al'amari daya bama kowa mamaki, wato zancen fyaɗe da akaima Maanal sai gashi a bakunan mutane harma da Media dangin Hajiya Yaya na gorantama Ammie da Maanal. Matuƙar tashin hankali Ammie da su Amaal da su Oum sun shiga, dan sun rasa daga ina wannan magana ta fita. Sirrine da babu wanda ya sanshi a gidan daga Daddy sai Yazeed. Ai sai fa jikin Maanal yay bala'in birkicewa, abinda ake gudun dai ya nema kaiwa ga faruwa, sai da akai gaggawar kiran likitanta abokin Yaya Yazeed dake anan cikin Kaduna..
     Wannan fitina ba'a samu kwantawarta ba sai da Baban su Hajiya Yaya yazo gidan da kansa. Shine fa yay musu kaca-kaca yace kuma biki ya tashi kowa ya shirya ya koma inda ya fito tunda amarya ta shiga ɗakinta. Sauran shagali kuma ya soke su, wanda kuma yake ganin bai isa ba zai yi ga fili ga mai doki. Hakan ya ƙara baƙanta ran Hajiya Yaya da Aunty Sabuwa, sai dai babu yanda kuma suka iya..
Chapter 141 · 0% Book details