Sashe 27
Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Tabbas da manufa kam ta ƙarfafa maganar taki Asiya. Amma kada ki wani damu. Mu ALLAH yasa haka shine mafi alkairi. Dan nima ta bakinki zuwa yanzu auren Maanal da yaron nan ya fita a raina. Duk kuwa da shi ɗin mutumin kirki ne. Amma halin uwarsa da ƴan uwansa bazai bar Maanal zama lafiya ba. Gata ita mai rauni. Ni yanzu abinda nake gani kawai mu lallaɓa Maanalu ta bama yaron nan Rafeeq dama ya shigo sosai, shi kansa Yazeed ɗin ba lallai idan sun aura masa tasu ba su barshi haka ai”.
Tabbas hakanne Nene, ni kaina wlhy yaron nan Rafeeq yamin. Yaron a haka dai kamar baida wata damuwa. Gashi kuma ɗan uwan Majdiya uwa ɗaya uba ɗaya. Majdiya mutuniyar kirkice ga addini. Dan hatta yaranta tarbiyyarsu ta banbanta da sauran ƴaƴan gidansu. To dan dai yaran yanzu ne kai kana hango musu alkairi su suna wani hange daban. Amma dai yanzu zanyi duk yanda zanyi ta cigaba da zama can Abujan dan bana sha'awar dawowar Maanal gidan nan a yanzu kuma sam Nene wlhy”.
“Wannan ma tunani ne mai ƙyau. Gara ta zauna a can ɗin kusa da ƴar uwarta. Tunda shima can yake Rafeeq ɗin sun ma fi samun shaƙuwa. To amma shi maigidan naki bazaiga an masa ba daidai ba?. Kinga dai yanda yake matuƙar ƙaunar yaran nan da musu hidima. Tunda kuka dawo hannunsa bai taɓa bambanta al'amarin su dana ƴaƴansa ba”.
“Tabbas hakane Nene. Nima idan na tuna hakan jikina yana sanyi. Dan ya musu abinda mahaifinsu da ƴan uwansa suka gagara musu. To amma yaya zamuyi, matar nan wlhy ta wuce duk yanda kike tunani. Nata ma mai sauƙi ne, dan babbar matsalarta itace ƙanwar nan tata. Saboda mashawarta ne bata moreba kawai, amma duk masifarta ta wani fannin tafi Basariyya sauƙi”.
“To mu cigaba da addu'a, ALLAH ai bai manta da kowa ba. In sha ALLAHU komai zai kasance da sauƙi. Yanzu dai sai kisan dabarar da zaki masa akan zamanta ɗin can dan a rabu lafiya har su gama wannan bikin nasu. Saboda yanzu kam kema fa sai kinyi haƙuri, zakiga abubuwa da yawa wanda za'a dinga miki su da gayyane.”
“Hakane Nene. In sha ALLAHU babu damuwa. Dama dai matsalar tawa Maanal ce. Dan su wannan samarin babu ruwansu. Itace dai dama ina tsoron a jangwalo ciwon nan nata. Amma idan bata gidan koma mi suke shirin yi suyita yi”.
Nene ta gamsu sosai. Dan haka suka cigaba da tattauna batun Maanal ɗin dai. Nene bata bar gidan ba sai bayan magrib. Ammie ta rakota sukaci karo da Hajiya Yaya itama ta rako Sabuwa. Kallon banza suka dinga musu. Dan Nene ma na gaishesu amma ko kulata basuyi ba sai ma tsaki da Sabuwa taja musu mai ƙarfi. Abin ya ɓatama Ammie rai amma sai ta danne. Itama Nenen duk da nata ran ya ɓaci sai ta danne dan bata son ƙarama Ammien damuwa...
_________★
Damuwa da ɓacin rai da tashin hankalin hukuncin da aka yanke yasa a ranar Yazeed ya koma Abuja batare da sanin kowa ba. Ita kanta Hajiya Yayan sai da dare ta aika Basira kiransa ta dawo ta sanar mata ɗakinsa ma a kulle yake. Waya ta ɗaga tai kiransa. Batare da amsa sallamarsa da gaisuwarsa ba tace yazo tana nemansa. Haƙuri ya bata akan shi fa ya koma Abuja. Dan ya samu kira na gaggawa. Ranta ya matuƙar ɓaci amma sai ta danne bisa shawarar da Sabuwa ta bata na a dinga lallaɓashi yanzu har ayi a gama lafiya. Cikin sauƙaƙa murya tace shike nan idan ya dawo sayi magana. ALLAH ya bada sa'a.
Ya amsa mata da Amin, dan ko yaya ya ɗan ji sauƙi a ransa na jin bata fushi da shi. Yazeed mutum ne mai kiyaye fushin iyaye, sannan yana da takatsantsan akan al'amarinsu. Ko wannan maganar Manaal ɗin da ace babu goyon bayan Daddy duk son da yake mata da tuni ya haƙura saboda mutuntasu....
________★
A Abuja dai kam RK ya riƙema Maanal wuta. Dan kullum sai yazo gidan Shahidah sai ya fake da dubata yazo yi kasancewar dama sun sanar dasu hakan. Sai dai abinda basu sani ba duk tsarin RK ne dama akan batun zuwa gida dubatan kullum. Ya cigaba da kwaɗaita mata zancen aiki. Tun tana dojewa harta sanarma Shahidah. A mamakinta sai Shahidah ta bata goyon bayan mizai hana ta amshi tayinsa. Ai abune mai ƙyau neman nakanka musamman a wannan zamanin. Cikin damuwa Maanal ta ce, “Amma Didi kin san Ammie bazata yarda ba. Hakama Daddy zaiga kamar mun nuna gazawarsa ne musamman idan mukai dubi da duk yaransa mata babu wadda ya bari tayi aiki, ko ku sai da kukai aurene yace idan mazanku sun yarda kuyi aikinku. Idan ni kuma nazo masa da sabon tsari sai yaga kodan bai haifemu bane ba”.
“Hakane Maanal. Amma idan aka duba naki al'amarin ke ai yana buƙatar uziri. Bazamu yanke hukunci ba yanzu ki bari zan sanarma Ammie to. Itama Amal zanyi magana da ita. Amma ko nan Daddyn su Barru shi goyon baya ya bada ɗari bisa ɗari, ya kuma ce in dai dan Daddy ne shi a barsa zaiyi magana da shi. Kinga an samu sauƙi kenan ai”.
“Shike nan ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi.”
“Amin ya rabbi, wannan dama itace addu'ar daya kamata kiyi tun farko. Sannan dan ALLAH idan yazo ki daina ɗaɗɗaure masa fuskar nan taki, hakama idan ya kiraki kina ɗauka Auta. Wulaƙanci sam bashi da ƙyau”.
“Didi ba wulaƙantasa nake ba nima. Bana son ya saki jiki akan abinda bazai samu bane kawai”.
“Hummm Maanal kenan. ALLAH dai ya zaɓa mana abinda yafi alkairi”.
Maimakon ta amsa da Amin sai Maanal ɗin kawai ta koma ta kwanta dama tana a ɗakinta ne tana karatun novel ɗin nata na fama Shahidahn ta sameta........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenm
u 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖2️⃣0️⃣
........Shahidah ta kira Ammie ta sanar mata da komai game da abinda RK yazo ma Maanal da shi. A mamakin Shahidah sai ji tai Ammie na maimaita kalmar Alhamdullah. Kasa daurewa tai ta ce, “Ammie kin amince kenan kema tayi aikin?”.
“Sosai kuwa Shahidah. Dan wannan wata mafita ce da masalaha UBANGIJI ya kawo mana. Ban sanar daku bane kawai amma tunda muka baro Abuja na dawo gidan nan a cikin cakwakiya ake da tashin hankali duk kuma akan batun auren Maanal da Yazeed ne. Namayi mamaki da kikace yau kusan kwana biyar bai leƙoku ba tunda yana Abujar shima.”
“Wlhy kuwa bai zoba Ammie, nama zata ko yana Kaduna ko yayi tafiya ne wani waje. Amma naga yana ƙoƙarin kiranta a waya yaji lafiyarta. Wai Ammie miya faru ko ɗaura musu aure kukai? Ko har yanzu Mamma ɗin ce ke tijarar bata son?”.
Ƴar dariya Ammien tayi da faɗin, “Kefa daɗina dake shirme Shahidah. Auren lafiya kuma yarinyata na a wannan halin na ciwo mai girma irin wannan hauka nake zan bari a mata aure bada amincewarta ba. Akan dai Hajiya Yaya ne da batun auren......”
Tsaf Ammie ta zayyanema Shahidah yanda komai ya faru da kuma matsayar da ake akai yanzu.
“Kai wannan mata ALLAH ya rabamu da masifarta Ammie. Ita dai ta sani mu ALLAH yasa haka shine mafi alkairi ma, dan wlhy garama ta auri Rafeeq ɗin amma haɗata kishi da wannan ƴar iskar yarinyar sangartacciya ai wani hatsarinne. Zasu iya haɗe kai su dinga cutar da ita watarana mu wayi gari zuciyar tata ta buga. Amma kinga Rafeeq ɗin nan wlhy Ammie yana da hankali da tarbiyya. Damma Maanal ɗin ce taƙi sakin jiki da shi kin dai san halinta”.
“Karki damu a hankali ne. Kudai ku cigaba da tayata da addu'a. Watarana ai sai labari. Amma in sha ALLAHU batun Yazeed kam nima bana mata fatansa kuma suje can su ƙarata. Yanzu ki bani zuwa gobe zan yi magana da Daddyn naku, idan ya tirje sai shi mijin naki ya masa magana ko naje Zaria na haɗashi da abokin nasa.”
“Shike nan ma Ammie wlhy dama haka kikayi”.
“A'a bari dai na fara masa magana dan bana son butsutsunsa. Yaya jikin autar?”.
“Alhamdullahi Ammie jikinta na ƙyau sosai. Dan naga har ta koma karance-karance novels ɗin nata na fama. Gata can ma tana shiri Abban Barru yace idan ya dawo zai kaita bookstore ta samo wasu”.
“To Masha ALLAH, ALLAH ya ƙara lafiya. Nima zan shigo na sake ganinta in sha ALLAHU zuwa next week haka komai ya ƙara lafawa.”
“ALLAH ya kaimu Ammie muna nan muna jiranki. Itama Amal tace next week zata dawo”.
“To shike nan idan naga zai mana dai-dai sai kawai mu taho tare, amma ni ranar zan dawo gaskiya”.
“Kai Ammie miyasa bazaki kwana ba?”.
“Daga dubiya sai kawai na kama kwana. Tunda ina jinku kullum a waya ai Alhmdllh ya wadatar, ba kuma sai na zauna na kula da tsohon mijina ba da ƙananun ƴaƴana”.
Dariya sosai Shahidah ta sanya. Daga haka sukai sallama....
___________★