← Book details Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 148

Sashe 42

Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

     Koda Maanal ta koma office zaman wasu sabbin samples na zanen ta fara dan babu wasa batare data kula kowa ba. Garama Yaqub ya mata sannu da zuwa. Tayi nisa a aikin nata akai mudu knocking ƙofa. Batare data ɗago ba ita dai taji sauran na magana da shi. Saurayine kamar su Yaqub da zai iya girmarta ita kam a shekaru, amma kasancewarsu oganninsa cike da girmamawa ya gaishesu. Sai kuma ya maida hankalinsa kan Maanal. Hakanne ya sata ɗagowa ta ɗan kallesa. Duk da tayi mamaki sai ta danne, ta amsa masa da kai. Bai damuba ya cigaba da faɗin, “Sister Maanal kinada visitor”.
     “Visitor?”.
  Ta maimaita da mamaki. Sake tabbatar mata da hakan yay ta ha hanyar jinjina kansa. Ta ɗan yi shiru kamar mai nazari tana wasa da pencil akan lips ɗinta sai kuma ta ce, “Okay ina zuwa”.
      Da girmamawa ya amsa mata da, “Ai kamar ɗan gida yake. Bari na masa iso”. Bai jira amsarta ba ya juya ya fita. Ba'a rufa mintuna biyar ba aka sake knocking ƙofar. Zamanta ta gyara da veil ɗinta, yayinda hankalin su Zaharadeen duk yana akan mai shigowar. Yana buɗe ƙofar ƙamshin turarensa na rige-rigen fara iso mata a hanci, hakan yasa ta ɗan ɗago idanu ta kallesa. Murmushi ya sakar mata yana jingina da ƙofar tare da harɗe ƙafafunsa da hannayensa a ƙirji. Sai kuma ya laluba aljihunsa ya ciro wayarsa ƙirar kamfanin Samsung mai ƙyawu da tsada ya shiga mata hotuna. Hararsa ta ɗan yi tana mai girgiza kanta ta maida ga abinda take yi. Sai da ya gama dan kansa kafin ya kai duƙe ya ɗauki abinda ya ajiye a ƙasa yana ƙarasa shigowa da faɗin, “Oh oh my queen Kinga kuwa yanda kujerar nan tai matuƙar dacewa da ke. Kin gama cika Watch Designer Maanal ɗinki Tawajena. Dan haka ina tayaki murnar shiga sabon Office. Amin afuwa dana kasance a late, tun safe naso nayi hakan uziri yasa ban zauna ba na koma asibiti. Naso tahowa da rana hakan bai yiwu ba kuma dai”.
      Ita dai kallonsa kawai take yana tsiyaya surutunsa kamar yanda sauran ma ke kallonsa suna murmushi. Hannu ya shiga basu, suna amsa da sauri da kuma girmamawa dan sun san yana da wani babban matsayi da kima a companyn. Dai da ya gama gaisawa da su ya maido hankalinsa kanta yana fiddo cake mai ƙyau daga cikin kwalinsa. Sai kuma ya tsitstsira abu a kansa kamar wata mai shirin hure birthday cake ya kunna masa wuta. Ɗauka yay ya zagaya ta inda take ya ajiye a gabanta sosai bayan ya tattare kayan zanen dake a gabanta ya ɗauke su gefe........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖2️⃣9️⃣
Chapter 42 · 0% Book details