← Book details Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 148

Sashe 106

Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

     To bayan dai kai ruwa rana da faɗi tashi, da kace nace da ƙyar dai Kamila ta amince bisa tsayawar ƴan uwanta biyu da suka dawo Nigeria a lokacin tare da mahaifiyarsu. Sosai farin ciki Fateema ta nuna da amincewar Kamila, taje har gida tai godiya. Anan ne suka fara sanin juna da sauran ƴan uwan Kamila da kuma mahaifiyarta da a yanzu itama take ƴakin neman komawarta ga mahaifin su Kamila ɗin.
          An fara shigi da fici akan auren Aliyu da Kamila, sai dai shi ango ya tare gabas ya tare yamma akan shi babu ruwansa. Da ƙyar ma ya amince yaje yaga Kamila a gidansu sau biyu. Dai-dai da lefe da sadaki duk Fateema ta biya. Dan kaf Family ɗin Baffa Ishaq Darma nada kuɗaɗensu a asusun bankuna tun daga manya har yara. Kamar yanda Fateema ta buƙata babu wanda ya saka mata hannu a hidimar wannan aure itace tai komai da kuɗaɗen asusun bankinta. Sai abincin taron biki ne da abubuwan da suka biyo baya Baba Sardauna ya sauke mata akan dole ba dan taso ba. Haka dai aka ɗaura Auren Aliyu da Kamila. A kuma lokacin ne Baba Sardauna ya bama Aliyu gidan zama, dan yace yakamata shima ya koma nashi da iyalinsa yabar gidan gandu. Hakan baima Aliyu ba, amma baya iya musu dole ya amsa. A sabon gida aka kai amarya Kamila, ita kuma Fateema tace sai bayan kamar wata guda zata tare. Da kanta taima ango rakkiya gidan amarya. Sai kuma bayan ta koma gida taci kuka harta godema ALLAH. Daga baya kuma ta maida komai ga ALLAH taita sallolinta harta samu natsuwa zuciyata tai fayau kamar ba ita ba. Sai ma walwalarta ta ninku a safiyar ranar. Har Aliyu da yazo gidan ya nuna jin haishin yanda ya ganta cikin farin cikinta. Wai ai bata kishinsa ta masa auren dole. Bayan dariya kawai bata kulashi ba ita dai. Tunda dai taci nasara sai fatan kuma ALLAH ya azurtasu da abinda ake nema...
      To da farko dai zaman Aliyu da Kamila babu wani armashi. Dan bai taɓa kulata a shimfiɗa ba. Baya sakar mata fuska. Baya zama suyi hira. Takurar Fateema ma ke sakashi zaman gidan amaryar da cin abincinta dan yasan idan yaje can wajenta ba bashi zatai ba. Gashi ta saka masa takunkumin bayan sati ɗaya ta ƙara masa sati uku wata guda zai yi a wajen amarya. Su Umma kuma sun goya mata baya. Hakan kuwa dole ya cika wata gudan nan a wajen Kamila sannan Fateema ta tare a gidan, har lokacin kuma bai taɓa kusantar Kamila ba. Itako Kamila hankalinta a tashe yake, dan bata tabbatar tana son Aliyu so mai tsananin gaske ba sai a yanzu da suka zama ma'aurata. Yanda yake mata, ko duk motsinsa Fateema dai yasa ta fara jin kishin Fateema mai tsananin gaske a zuciyarta. A ganinta ba'ai mata adalci ba. Idan ance Fateema tasa aka aurota to ai dama bawa baya wuce ƙaddarasa. Tun ran gini tun dan zane. Koda sawar Fateema koda rashin sawa dama ALLAH ya ƙaddara sai Aliyu ya ta zama mijinta. Wannan zafin kishi daya fara taso mata yasa ta tunkari mahaifiyarta da ƴan uwanta da batun, maimakon su tausheta su lallasheta su kuma sai suka fara ɗorata a hanya mara ɓillewa. Aiko ta mitsithtsike ido ta nunama Aliyu bafa zata yarda ba. Dan yanzu matsayinta ɗaya da Fateemar da yake damun mutane da batunta. Tofa wannan abu ya tayar ma Aliyu da hankali, yo tunkan aje ko'ina kenan ma. Tab ɗin jan inji mata, ai dole yayma tufƙar hanci. Nan fa ya zauna ya warware Kamila tsaf da rashin mutunci, yo har a gayama bafillace zuciya da baƙar magana. Uwar watsi sukai yace taje gida za taga aike. Hankalinta ya tashi sai kuma duk ta gigice. Ita ina taga ƙafar tafiya gida tabar wannan daular da kowa ke mata barka da arziƙin shigowa. Sannan ma auren sati uku kawai ai wannan abun kunya ne da ko'a mafarki bata fatansa. Dole fa ta zubar da makaman yaƙi ta shiga neman afuwa da rusar kuka da ban haƙuri tana tabbatar da sharrin shaiɗan ne. Hakan ma bai saurareta ba, yace saifa ta tafi. Haka kuwa dole ta tafi gida batare da kowa ya sani a dangin Aliyu ba. Amma sai dai me, a ranar iyayenta suka maidota, suka kuma duƙufa bama Aliyu haƙuri suma da tabbatar masa ƙuriciyace ke damun Kamilar kawai. Amma yay mata afuwa ko Fateema kada ya bari tasan wannan al'amarin dan ALLAH. Suka kuma masa alƙawarin canjawar Kamilar fiye da yanda yake buƙata.
     Badan dai Aliyu yaso ba wannan wuta ta mutu a haka. Sai dai kuma ya sharɗanta ma Kamila sharuɗai masu tsauri game da Fateema in har tana son cigaba da rayuwa a cikinsu. dole kuwa ta amsa da hannu bibbiyu tayi biyya. Sai dai kuma acan ƙasa ta ɗauke karatun uwarta da ƴan uwanta tsaf. A haka Fateema ta tare gidan itama. Da gaske Kamila ta kwantar da kai fiye da zaton Aliyu. Tana bin shariɗɗansa sau da ƙafa. Bawai shariɗɗansa kawai ba, da gaske Fateema mugun kwarjini take mata, dan matar nada wata irin baiwa da nagarta mai ban mamaki. Ga ƙyaƙyƙyawar zuciyar zama da kowa da gaskiya. Sai dai bata son raini, bata son munafunci da wulaƙanci. Wannan abinda Kamila ta sani ne tuni, dan haka ta shirya yaƙar Fateema da su har ma da Aliyu. Sannu a hankali kuwa suka fara tasiri, dan duk wata hanya ta gwaji Aliyu yabi akan Kamila game da zamansu bai kamata da kowane laifi ba. Sai ma yanda take bin Fateeman ya fara saka masa jin nutsuwar zama da ita. A gefe kuma ga Fateema kullum damuwarta da fatanta taga Kamila da ciki.
      To tsakanin mace da namiji kwance a ɗaki ɗaya sai ALLAH, yau da gobe kuma bata bar kowa ba. Dan sannu a hankali dai Kamila taci nasara akan Aliyu cikin dabaru da kissa irin na mata ya maidata cikakkaiyar mace. UBANGIJI kuma mai hikima da yin yanda yaso a lokacin da yaso ba'a rufa wata biyu da Kasancewar tasu a ƙarƙashin inuwa ɗaya ba sai ga Kamila ta fara laulayin ciki. Ya rabba zokuga murna ga Fateema. Sai ma ka ɗauka itace da cikin. Gaba ɗaya ta kwashe kulawarta kacokan ta maida kan Kamila. Hatta shi kansa Aliyun yanzu ba wani yana samun lokacinta bane, har ya fara kishi da hakan sai da ta zauna ta lallashesa. Bawai baya farin ciki da cikin da Kamila ta samu bane, a'a yana dannewa saboda baya son ko yaya zuciyar Fateemansa ta sosu. Dan haka ya barma zuciyarsa nasa farin ciki ita ya bari take nata a bayyane dama zuciya. A haka kwanci tashi ALLAH ya sauko Kamila lafiya, ta haifo ɗanta namiji mai tsananin kamanni da Aliyu da Fateema tamkar sunyi kaki, dan in baka sani ba kazo saika ma ɗauka Fateeman ce ta haifi yaron. Wannan shine ƙalubale na biyu daya sake girgiza Kamila da ahalinta, sai dai sun shanye a cikinsu suma sunata fatan alkairi. Sai ma ɗaukar jinjiri da Kamila tayi domin sake samun fada ga Aliyu tun a randa ta haifesa ta damƙawa Fateema tare da alƙawarin mallaka mata shi na har abada. Ta kuma sake maimaitawa a gaban Baba Sardauna da Umma da dukkan ahalin Aliyu da nata ahalin. Ranar kuka sosai Fateema tayi da sake jin ƙaunar Kamila. Tana ji a ranta lallai batayi zaɓen tumun dare ba. Hakama Aliyu wata sabuwar soyayyar Kamila ce yaji ta soki ƙahon zuciyarsa tayi tasiri a ciki tare da mamaye komai. Duk wanda zai so Fateeman sa to har abada zai dawwama shima kam yana sonshi da ƙaunarsa ne.
        Haka dangin Aliyu da Fateema ma suka zo aka haɗu akasha shagalin suna yaro yaci suna Fadeel (Babban yaya 😂👍).
      Bayan shan shagalin suna aka bar masu ɗansu. Gaba ɗaya Fadeel a ƙarƙashin kulawar Fateema yake. In dai ka ganshi a hannun Kamila to lallai za'a bashi abincinsa ne. Sai ko dare yayin yin barci. Amma dukkan wahalhalu na raino da kulawa Fateema ce. Kai hatta daren ma yana fara kai watanni shida ya koma kwana hannun Fateeman. Dan ALLAH yayisa bamai fitina ba. Tama kai ba wani ya damu da shan nn bane ba.........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖6️⃣8️⃣

______________
Chapter 106 · 0% Book details