Sashe 90
Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Basmah tace “to shi da kike jin tausayi baya tausayin kansa, da yana tausayin kansa da ya dade da neman sulhuâ€. Sai da Gumsu ta kafa naci sannan Basmah ta hakura ta bata lamabar Aalimah ta Ontario. Sanda Gumsu ta kirata Mu’azzam take wa cumbing kanshi ya fito daga wanka. Don haka bata daga ba sai da ta gama, ta kuma taimaka masa ya gama shiryawa, Mus’ab ne zai zo ya daukesu zuwa gidan Uncle suyi sallama ta hada kayanta don gobe jirgin asubah zasu bi zuwa U.S. Gumsu bata fasa kira akai-akai ba har Mu’azzam ya gaji yace ta daga wayar nan. Tana dagawa taji Gumsu. Ajiyar zuciya tayi tace “ko dai wrong number ne?†Gumsu da borin kunyar ta tayi ta bata hakuri tana gaya mata abinda take hange na barinta gaban ‘ya’yanta tunda in ta ki Mu’azzam ta ki Aboulkhair karshenta dole wani daban zata aura ta bar yaran cikin maraici ita abinda bata so kenan tayi hakuri ta fahimceta ta daina kullatar kowa akan haka, soyayyar da suke yi mata ne ya janyo hakanâ€. Mu'azzam ya gaji da jiran Aalimah su fita yace da hannu wacece ne? A hankali ta motsa labbanta tace masa “Gumsu-Moiram†murmushi yayi ya karbi wayar yace “inason fita da iyali na, ko za’a bar wayar sai mun dawo?†Gumsu ta shaqa tace “ina can ina maka kamfen, har gaba na kulla sabida kai, kana nan kana min kora da hali ko?†Yace “to ai ni ban sa ki ba, dadi na dake sa-kai a uku babu gaira babu daliliâ€. Aalimah bata san sanda ta saki dariya ba, in Mu’azzam ya san yadda Gumsu ta damu da al’amarinsa da bai yi mata haka ba. Ta karbi wayar tace mata ta hakura, sannan ta barsu suka fita. Sunyi kwalliya ta alfarma cikin shigar mutanen Nijar dukkansu. Mus’ab na tuki suna baya. Ya dan juyo ya dubi Aalimah yace “we’re gonna miss you so much Adda, kwana ukun nan da baki gidan baki ji yadda gidan ya koma boring ba kowa baya walwala musamman Maryamâ€. Murmushi tayi tace “nima zanyi kewar ku, yadda halshe bazai iya bayyanawa ba, duka gidan I enjoyed your company so muchâ€. Mu’azzam yana jin su bai ce musu komai ba. Daidai lokacin da suka iso gidan, duk mutanen gidan suka tarar a falo. Kowa yayi jigum kamar wadanda aka yiwa mutuwa. Aalimah na shigowa Maryam ta nufe ta ta rungume tana kuka tana rokonta kada ta tafi. Daddy yace “yau naji ikon Allah in da za’a ce kada mace ta je gidan miji, kema kwana nawa zakiyi a gidan da zaki hanata zuwa nata? Kuma wai don rashin kunya a gaban mijin ta?†Su Taufeeqah suka hau dariyar Maryam, Mu’azzam yace “Maryam duk sanda kike son ganin Adda zan miki visa kije Las Vegas. I promisedâ€. Ai nan da nan Maryam ta saki Aalimah ta hau tsalle. Anan suka ci abincin dare suka nitsa hira har saida yaran suka yi barci, Anty da kanta ta hadawa Aalimah kayanta tsab, Mus’ab ya sanya a mota. Anan suka karar da rabin daren, sai da zasu tafi Anty ta fiddo sayayyar data yi mata na kayan jarirai unisex cikin katuwar jakka, dana su Basmah suma kowa ya samu jaka guda. Daddy kuwa kudi ya zuba mata cikin account din da ya dade da bude mata tun zuwanta kamar sauran ‘ya’yansa, duk wata yana saka musu kudi don bukatocinsu, yace in tana so ta kwashe ta mayar U.S account din ta ta rufe account din in kuma zata bar shi to, Aalimah sai hawaye, ta rasa bakin godiya, tace bayan dawainiyar da suka sha da ita wata da watanni, kuma har da karin wannan dawainiyar. Uncle Suraj Kashim yace “akul! Ta sake kira masa dawainiya, dole ne yayiwa Asseya da ‘ya’yan ta dawainiyar don bata da kowa sai shiâ€. Da haka suka yi sallama Aalimah na ta kuka. Don ji take kamar wannan shine lokaci na farko da zata je gidan miji. Basu samu sunyi barci ba don suna shigowa lokacin sallar asubah na yi. Sallah suka yi daga nan suka kimtsa. Chauffeur na hotel din shi ya kaisu filin jirgi tare da kayan su. ****** A cikin jirgi Aalimah ta kwantar da kai a kafadun Mu’azzam, rayuwarta bakidaya ta dinga gilma mata tamkar a majigi. Ta faro ne daga zuwanta Boston, inda daga nan tarihin rayuwar ta ya fara, rayuwarta gidansu Mu’azazam, haduwar ta da Aboulkhair, aurensu har zuwa rabuwar su. Aurenta da Mu’azazam da irin kalubalen data fuskanta a cikin auren, haihuwarsu zuwa rabuwarsu da kuma kalubalen data fuskanta a cikin rabuwar. Har kuma zuwa yau da Ubangiji ya sake binding dinsu together. Hakan kadai ya ishi bawa ya yarda Ubangiji Subhana mai yawan hikima ne, komai yayi kada bawa yasanya ayar tambaya. Duk abinda ya tsara ya san dalilin yinsa. Data yi hakuri da kaddarar auren Mu’azzam yau gashi ta ci ribar hakurin ta. Ubangiji ya san cewa Mu’azzam shine mafi alkhairi gareta akan Aboulkhair shiyasa ya canza rayuwar su ta fuskar da ya ga dama. Hakurin data yi a zama da Mu’azzam bai tashi a banza ba. Hakika kowa ya bi iyayensa ya kuma fawwala al’amarinsa ga Allah zai iya masa. The fact that ana son juna kamar a hadiye juna baya hana rabuwa a wa’adin da Allah ya tsara, ko ba’a mutu ba rayuwa tafe take da kaddarori kala-kala masu sabbaba rabuwar. Kuma karfin soyayya baya hana karewar aure a wa’adin da Ubangiji ya nufa. Wannan shine ya faru tsakanin ta da Aboulkhair wanda har abada bazata manta ba a karkashin zuciyar ta. Abu guda take da tabbacinsa; daga ranar da ta soma son Mu’azzam a matsayinsa na mijinta, daga ranar da ta zama sirrin Mu’azzam ya zama sirrinta, gabadaya rayuwar data yi da Aboulkhair ta zama shudadden al’amarin da bata sake tunawa da wani feeling ba. Aboulkhair ya rikide ya juye ya koma kamar Yaya Aboubacar a idanunta.