← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 91

Sashe 88

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Cikin kwana bakwai Aalimah ta samu karfin jikinta, sabida kulawar data ke samu daga Aboulkhair da Yesmin. Ya hadata da magunguna masu kyau wadanda suka taimaka wajen rage mata yawan aman data ke fama da shi, ga kayan dadi iri-iri kullum yana baiwa Yesmin ta kawo mata leda-leda, tuni ta barwa su Inna abincinsu sai kayan kara jini dana kara kuzari da yake aikowa. Mummy Zulaiha kuma kullum sai tayi mata waya ta tambayeta abinda take son ci, tun tana jin nauyi har ta daina. Don haka kwanon abincin ta na musamman ya koma gidan Daddy wanda Mummy da kanta ke shiga kitchen ta girka mata, kullum Yesmin da Nurat ke kawo mata.
Saida ta warware sosai ta maida jikin ta Malam yayi mata iznin tafiya Kanon kamar yadda ta bukata.
A daren ranar ta hada kayanta tsab tana cike da doki. Washegari Aboulkhair ya saya mata tikiti ta tafi Nigeria. A Abuja tayi transit kafin ta taso ta sanya layin ta na Nigeria ta kira Yaya Aboubacar ta gaya masa lokacin da zata sauka. Kafin aje Kano ta jigata sosai. Amma tarbar data samu a gidan su tasa ta mance da duk gajiyar data kwaso.
Ta samu gidan nasu da albarkar baki na musamman, Dr. Suraj Kashim wan Mama da matarsa Ilham da biyu daga cikin yaransu Mustapha da Maryam sun zo ganin gida daga kasar Canada. Maryam zata yi sa’ar Sultana itace ta biyu a ‘ya’yan aunty Ilham. Mustapha zaiyi sa’an autarsu Suhaima. Don haka tuni ta ware a cikin ‘yan uwanta data dade bata gani ba anata harkar arziki, tana ta taka-tsan-tsan kada wani cikin su ya fahimci cikin nan da bata so a sani. Sai fama take da zumbulelen hijab tun zuwanta har aunty Ilham na tsokanar ta ko Mu’azzam ne yasa ta yawo da hijabi, anan Mama take gayawa Ilham ai babu auren, ta gaya mata duk abinda ya faru.
7/13/21, 5:59 PM - Buhainat: Aunty Ilham ta taimaka mata ta sanya lallausar leshin data kawo mata, ta zaunar ta gefen gadon ta tana yi mata sassanyan make-up. Sai gyaran muryar Uncle suka ji a bakin kofa yana fadin “Ilham ina ‘yar taki ne? Ta zo suje ko tausa ta yiwa mijinta ya rage gajiyar zirga-zirgar nan da ya shaâ€. Ilham tayi dariya Aalimah ta sadda kai kamar tace kasar ta tsage ta shige. Yace “maza fito ki same shi a mota driver zai kai ku masaukin shi. Daga yau har kwana uku na sallame ku, in zaku wuce U.S kuzo muyi sallamaâ€.
Aalimah kamar tayi kuka bayan wucewar Daddy, bata ankara ba kuwa ta ji hawaye sun sauko mata data ji cewa da gaske zata bar Ilham da iyalin ta bada jimawa ba. Aunty na cewa ta yi hakuri ta bi umarnin babanta, ta bar Mu’azzam ya fanshe watannin da ya yi ba tare da ita ba cikin kwanaki ukun nan. Ta armasa masa su su shiga cikin kundin tarihin rayuwar su. Sakamakon haka Allah zai iya bata Aljannah. Ga bin iyaye ga bin mijiâ€. Dariya tayi don ta san aunty Ilham wayo take mata.
Ita ta tsitstsintar mata duk abinda tasan zata yi amfani dashi ta jefa mata a jaka. Ta dauko mata jakar suka fito tare. Mu’azzam da Uncle na bakin motar Uncle suna magana direban yana daga cikin motar. Fitowarsu yasa suka yi sallama, aunty ta bude mata kofa shi kuma Dr. Suraj ya bude masa, suka shiga suka rufe musu tare da daga musu hannu.
Har suka iso hotel din da Mu’azzam ya sauka basu yi magana a junansu ba, shi Mu’azzam waya yake da Aboulkhair yana gaya masa gashi a Canada ya zo biko, Aboulkhair yace “Canada kuma?†Murmushi yayi yace “can ta yi kaura, tunda zaman gidan Malam Raazee ya gagara, kasan mace in ta wuce zaman gida tace kuma sai ta zauna to akwai matsala, don bazata taba jin dadin sa ba, musamman a cikin dattijai†Aalimah ta harare shi ta gefen ido. Aboulkhair yace “gidan Dr. Suraj ta koma kenan?†yace “eh, in dama ta ki ba sai a koma hagu ba?†Murmushi Aboulkhair yayi yace “kuma Inna Kasisin tana can tana cigiyar ta, ta dade da saukowa, auren data ke nema maka ma da bakinta tace ta fasa, ba za’a samu macen da zata zauna da Mu’azzam tsakani da Allah cikin kowanne hali irin Aalimah ba.
Tana fadi da bakin ta “Aalimah ce ta zauna dashi a halin rashin lafiya, don lafiya ta samu bazata amince wata ta more ta ba Aalimahr baâ€. Duk zancennan da suke yi akan kunnen Aalimah sabida a hands free Mu’azzam ya sanya wayar.
Ta tsurawa Mu’azzam ido jin abinda Aboulkhair ke fada. Mu’azzam ya samu lafiya as in how? Dama lalurarsa mai warkewa ce? A take kuma kwakwalwarta ta tafi tunano mata wani zance makamancin wannan da suka taba yi da Daddynta farkon aurenta da Mu’azzam. Cewa Mu’azzam zai iya warkewa bayan samun accurate treatment na akalla shekaru goma. Kuma ya dade da cika wannan ka’idar. Yadda yake romancing dinta dazu passionately kuma cikin nutsuwa ba yadda ya saba ba. Idanunta suka cigaba da budewa akan Mu’azzam yana ta hira da Dan uwansa yana ta murmushi kamar ya manta da ita cikin motar. Irin murmushin da ba kasafai yake yi ba sai yana cikin matsanancin farin ciki. Sassalkan sajensa ya kwanta lufff akan fuskarsa ya kara masa ilhama da cikar zati. Fararen hakoransa a waje, kamar wanda aka yi wa bushara da Aljannah.
Lumshe Idanunta tayi, a lokacin data ji sanyin hannun Mu’azzam a cikin nata. Ta kuma ji motar ta daina motsi wato sun iso masaukin nasu. Direban ya daukar mata jakarta da Ilham tasa mata daga bayan mota, ya rakasu da ita har kofar dakinsu ta cikin lifter. Sannan ya sake biyo lifter ya dawo kasa ya dauki motar don kaiwa ubangidansa.
Chapter 88 · 0% Book details