Sashe 49
Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ba, a wata babbar islamic school mai lasisi a kasar ta Amurka. Wadda Larabawan kasar Morocco ne suka bude ta. Auren Juwaira ya tabarbarar da lafiyar kwakwalwar Mu’az a karo na biyu, abin da ya tada hankalin Daddy ya dawo da tsohon zancensa na aura wa Mu’az cousin dinsa Halima, a ganinsa auren shi zai daidaita Mu’azzam. Daddy bai san cewa, son aure daban, soyayya daban ba. Mu’az ba aure ya damu ya yi ba, Juwaira yake so. Auren Juwaira shi ya tado matsalar Mu’az ta zama sabuwa sharr! Watansa guda a psychiatric yana karbar magani kafin ya manta da Juwaira, ya koma normal life dinsa. Ya kuma nemi (MBA) a nan Nevada (Las vegas) a jami’ar da ya yi ya soma karatun (MBA inOil and Gas Management) tsayin shekara daya, ya gama cikin tarin nasara, domin hakika shi din gifted ne, irin jajirtattun mutanen da ba su da yawa a cikin al’ummah. Ashe karfin kwayoyi ne kawai ya binne Juwaira daga zuciyar Mu’az, da ya samu labarin haihuwarta wajen wani makocinsu, sai abin ya dawo sabo. Sabida duk cikin wannan lokacin da ya samu nutsuwa jira yake Juwaira ta kaso aurenta ta fito daga gidan mijinta su yi aure. Haihuwarta da ya ji kuwa ya tabbatar masa Juwaira ta daidaita da zabin iyayenta, ba ta da sauran abin da za ta ba shi. Aggressive tendency din ya motsa. Sai da ya kara kwanciya a asibiti, aka kara kokari ya dawo daidai, likitocinsa kuma suka bada shawarar a yi masa aure da gaggawa zai rage masa frustration din Juwaira da ke damunsa. Ba tare da bata lokaci ba aka yi auren Mu’az da Halima, aka taho da ita gidansa a Las Vegas. Ranar da aka kai masa Halima a matsayin matarsa, a ranar ya samu labarin rasuwar Juwaira da iyayenta, a dalilin hadarin jirgin sama. Bayan Mummy da Daddy da suka kai ta sun musu nasiha sun juyo ne aka yi masa wayar aka fada masa. Gabadaya sai kansa ya juye, ga Halima zaune a gefensa, ya kasa yarda da abin da aka gaya masa. ya juya yana kallon Halima da rinannun idanunsa kamar ita ce sanadin mutuwar Juwairan. Duk wani anger, duk wani temper, duk wani frustration dinsa na lokaci mai tsawo ya sauke su ne a kan yarinya Halima ‘yar shekaru goma sha bakwai. Bai taba zina ba, bai san neman mata ba, bai san ya ake yi ba, don haka aggressiveness dinsa na ranar maimakon fashe-fashe ya kare ne a kan Juwaira a matsayin auratayya ba tare da wani feeling ko kankani game da yarinyar a zuciyarsa ba. Sai bayan ya fara dawowa hayyacinsa ne ya lura yarinyar ba ta motsi, ga ta kuma cikin jini face-face. Mummy ya kira, ya ce su zo su dauke wannan yarinyar da suka kawo masa, kawai don ya yi having sex da ita sau daya ta mutu. Mummy da Daddy suna hanya ba su kai ga isa Massachusetts ba daga kawo masa Halima da suka yi wayarsa ta riske su. Hankali tashe suka juyo duka dawo. Suka shirya Halima suka kai ta asibiti, likitoci kin karbarta suka yi, suka ce rape case ne wannan,rape din ma wanda akayi da karshen rashin imani, sai police sun shigo ciki, duk da rantsuwar da suke musu na cewar matarsa ce, da marriage certificate, wanda Daddy ya yo musu daga Nigeria, kin yarda suka yi. Wane miji ne zai yiwa matarsa haka? Sai da police suka shiga sannan suka karbe ta, suka shiga kokarin nemo numfashinta. Kin san Bature da rape case ba sauki, balle baturen Amurka. Shi ma Mu’az din nasa likitocin sun rike shi don sun ce za su kara bincike a kansa da Daddy ya kira consultant dinsa ya gaya masa abin da ya faru. Report din asibitin Mu’az shi ne kadai ya cece shi daga wannan lamari, da tuni ya kare behind bars, saboda ba’a shari’a da maipsychologicaldisorder kowanne iri, balle Mu’az da ya dade a cikinta. 6/29/21, 9:01 AM - Buhainat: KWATARKWASHI