← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 91

Sashe 30

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

suka girmi Ishaq, Uncle Edrissa da Uncle Oussama, wadanda suka kasance sun fito ne daga ciki daya, ragowar duka kannensu ne. a mazan akwai wadanda ba su kai ga yin auren fari ba suna karatu, sun biyo Ishaq da Mansour. Amma a nan jami’ar Abdou-moumoun babbar jami’ar kasar Nijar. Ranar ta zamo wata ranar reunion ta iyalin RAAZEE. Matan ma da ke gidan aure duk sun zo wajen Yayan nasu da suka dade ba su gani ba, da kyawawan ‘ya’yansa wadanda suka dauko gida a kamanninsa. Da daddare bayan kowa ya koma gidansa dakin Inna Kasisi ya koma. Ya ce, shi ba abincin wanda zai ci sai nata. Murmushi ta yi da ta tuna wani abu, ya fi kowa son girkinta. Har satar dumame yake mata tana barci, in kuma Mansour ya cinye masa abinci kafin ya dawo yana cin uban duka. Bai sani ba tun tafiyarsa dakin Malam ta shiga kicin ta shirya masa lafiyayyen abincin abzinawa na asali. Ya ci ya yi hani’an kamar mai yin cin biyan bashi. Washegari ya gaya wa Yayansa Uncle Oussama yana so zai je Tessoua da Zinder son samu har Arlit ya kai yara su ga asalinsa da dangin Inna da ke can, da na Malam. Uncle Oussama ya bada mota Hilux da suke shiga sahara da ita, da kuma dansa Hamoud ya tuka su, ya fi kowa iya tukin mota a gidan, kuma ya saba shiga garuruwa da sahara tare da Malam. Tun suna tafe kan kwalta har ta soma bacewa ganinsu. Tafiya ce suke ta yi cikin rairayin sahara. Aalimah na kallon yanki da bigire na tsatson mahaifinta tana jin wani shauki a zuciyarta. Tafiya ce mai dadi da ta sanya nishadi a zukatansu. Ga guzurin abinciccika kala-kala a warmers da ababen sha masu sanyi a coolers Inna Kasisi ta yo musu. Duk wanda ya ji yunwa zai bude ya diba ya ci ya sha. Tafiya aka ce yankin azaba, kuma mabudin ilmi. Tsananin ranar kasar Nijar da zafin rairayin sahara ya sanya ita kanta A.C din motar ta daina bada wani sanyi mai karfi. Ba abin da Aalimah ke so a wannan tafiya irin kallon rakuma da makiyayansu, Daddy na ba su labarin kuruciyarsu da yadda suke taya mahaifinsu kiwon nashi rakuman a Tessoua, garin da za su je. Tafiyar awanni masu yawa ta kawo su birnin Tessoua.Tessoua na daya daga cikin manyan birane goma da kasar Niger ke ji da su. Hamoud ya dauke kan motar ya shiga unguwar da za su, har kofar wani gidan laka mai cike da yawan dabbobi da almajirai fal! A kofar gidan Mazaje ne suna daukar karatu tare da wani dattijo. Wannan shi ne ainahin gidan kakannin su Daddy, wato gidan iyayen Malam Raazee. Dattijon da ke bada karatun shi ke amsa sunan Malam Yahyya, kani yake ga Malam, shi ke zaune a gidan yanzu da iyalansa, sai sauran ‘yan uwan Malam da iyalansu duk a gidan suke kasancewarsa babban gida na gado. Sun samu kyakkyawar tarba daga jama’ar gidan, abinci kala-kala na abzin, rago guda aka gashe musu don Malam Yahya ya san da zuwansu. Har gonar kiwon kakansu an raka su. Su Basma ‘yan Massachusetts yau an yi kwanan gadon alawayyo. Sauro ya ci rabonsa ya more. Sun ga dangi-dangi sun gansu. Washegari da safe Hamoud ya cika tankin motarsu da mai tatul suka kama hanyar Zinder. Tafiyar sai ta zame musu tamkar ta yawon bude ido, ga Hamoud da ke yi musu bayanin ko’ina. Basma da Khaleesat, sai suka bude wayoyinsu suka shiga recording abubuwan da suka burge su. Zinder babban gari ne, kuma jiha mai tarin al’umma masu ethnic group daban-daban. A gidan iyayen Inna Kasisi suka sauka, nan ma an musu tarba ta musamman duk da ba su san da zuwansu ba. Daddy ya bi ‘yan uwa lungu-lungu ya yi musu alheri mai yawa, kamar yadda ya yi a Tessoua. Kwana biyu suka yi harama suka dauki hanyar Arlit. Awanni masu yawa a tsakani suka isa. Arlit nan ne tushen su Inna Bintou kishiyar uwa, wadda ta zame musu babu maraba da uwa mahaifiya. Ta ba su kulawar da ba su samu daga mahaifiyarsu ba, don haka tana da matsayi sosai a wurin ‘ya’yan Inna kasisi. Nan ma Daddy ya yi alheri sosai, don duka dangin nasu tun daga na Tessoua, na Zinder har nan na Arlit suna cikin yanayin rayuwa, abin sai godiyar Allah. Daddy yana shan mamaki in yana jin sunan Mu’azzam a bakin danginshi sosai, ba wanda bai sanshi ba, ba wanda ba ya yi masa addu’ar alheri saboda taimakon da yake musu, wanda Daddyn ba shi da masaniya sam. Jinjina kai yake yana sanya mishi albarka cikin zuciyarsa. Sun baro garuruwan bayan Hilux dinsu cike da tsarabobi kala-kala na abubuwan amfani, irin nasu. Da suka dawo Niamey ma ba su huta ba, zagaye suke na gidajen ‘yan uwa.
Chapter 30 · 0% Book details