← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 91

Sashe 33

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

******
Jirgin Ethiopian Air ya sauke su a Boston Logan International Airport da misalin karfe goma na dare agogon Massachusetts. Mummy ba ta san da dawowarsu ba a ranar don tsayin lokacin nan babu wanda ya yi magana da ita, daga su har Daddy. Su kansu ba su san dalili ba, don rashin sayen layi na kasar bai isa ya zama dalili ba, abubuwa da yawa sun janye hankalinsu a Nijar, kama daga tafiye-tafiyen da suka yi ta yi, da yadda suke zama busy cikin ‘yan uwa. Ga shi Mummy ba ta yin social media, hada layin ne ya zame musu wahala. Don haka cab suka dauka tun daga airport har kofar gidansu da ke cikin rukunin gidajen Martha’s Vineyard Estate, Mummy ta jima da kwanciya sai jin kararrawar gidan ta yi tana ta faman ruri ba kakkautawa.
Barci fal idanunta ta zo ta bude kofar, sai kawai ta gansu kamar daga sama, sai murmushi suke dukanta da shi. Sai dai wannan hargagin nasu duk babu, Yesmin ce kawai ke mata karadi, ta kuma hahhanga bayansu ba ta hango sanyin idaniyarta ba, ba ta hango tauraron zuciyarta ba, ba ta hango Ishaq dinta ba.
‘Where’s your Dad (ina Babanku)?†Shi ne abin da ta fara tambayarsu, kafin ta bi su da runguma da sumba daya bayan daya. Amma da ta zo kan Aalimah hannunta kawai ta kama, sannan ta ce mata, “Welcome back (sannu da zuwa)â€.
Zubewa ta yi a kan gwiwoyinta ta ce, “Mummy ina wuni, ya ya gida, mun same ku lafiya?â€
Sosai ta ji zuciyarta ta motsa, ta kai hannu ta daga yarinyar tsaye sannan ta rungume ta. (kyautatawa da ladabi suna canza kiyayya daga zuciyar ma’abocinta, zuwa akasinta- Takori).
Aalimah ta lumshe idonta na lokaci mai tsawo da ta ji ta yau a jikin Mummy Zulaiha. Ji ta yi kamar ABULKHAIR ne ya rungume ta. Kafin ta farfado daga duniyar shaukin Abulkhair da ta tafi a jikin Mamansa, Mummy ta sake ta, sannan ta kama hannunta tare da taya ta da daukan jakarta daya suka shige cikin gidan.
Mummy ta tambaye ta, ya ya ta samu mutanen gida? Nan ta ke gaya mata, “All our stay was in Niamey (Niamey kawai muka je)â€.
Ta jinjina kai. Suka ci gaba da hira da sauran ‘ya’yanta. Labarin zuwansu Zinder, Arlit da Tessoua suke ba ta da irin wahalar da suka sha a sahara. Dukkansu kamar an sa zare da allura an dinke musu baki, babu wadda ta yi gangancin faxa mata maganar auren Daddy, ko da da subutar baki ne. Ta tambaye su ina yake? Suka ce akwai abin da ya zaunar da shi, zai taho in ya gama.
Yau Aunty Zulaiha cike ta ke da farin ciki wanda dawowar ‘ya’yanta gare ta shi ne sila. Ba su taba daukar irin tsayin wannan lokacin ba sa tare ba. Kowa ya kasa barci, raba dare akai ana hira. Ta yi musu alkawarin kai su MIAMI RESORT shakatawa sati mai zuwa idan yayansu Abulkhair ya zo hutu.
“Wouldn’t you take us to Las Vegas?†Yesmin ta tambaya tana mai kwanciya a jikinta. Duk da baya sake musu, ba ya shiga sha’aninsu kamar Abulkhair, zuciyar Yesmin tana son Mu’azzam. Duk da suna daukar lokaci mai tsawo ba su ganshi ba ba ta manta shi. Duka Khaleesat ta kai mata, Mummy ta janye ta da sauri,
“Mu je mu yi kaniyarki a Las Vegas?â€
Rungume Yesmin Mummy ta yi tana murmushi, “He is not at Las Vegas Yesmin, he went to Bahamas. I promised taking you to him as soon as he is back (ba ya Las Vegas yanzu, ya je Bahamas. Na yi miki alkawarin kai ki wurinsa da zarar ya dawo) in ba ku koma makaranta baâ€.
Aalimah upstairs ta haye ta barsu, ta shige dakinsu. Nemo layin wayarta ta yi na gidan wayar Verizon jikinta har rawa yake ta sanya cikin wayarta, she cannot even express how much she missed him, (bazata iya fadin yadda tayi kewarsa ba) kawai ka sanya wa zuciyarka mai karatu cewa, Aalimah ta yi kewar Abulkhair yadda hasashenka ba zai iya bayyanawa ba. Duk da ta yi farin cikin ji daga bakin Mummy cewa, yana nan zuwa sati mai zuwa. Unfortunately, alkawarin da suka daukar wa Daddy ya fado mata, na haramta musu kiran juna a ranakun mako. In ta yi hakan ta ci amanar Daddy…
Da sauri ta yi jifa da wayar a kan gadonsu ta fada bisa lallausan gadon ta nitse cikin (water mattress) dinsa tana maida numfashi dai-dai. Su Basma na shigowa ta rufe idonta kamar mai barci. Barcin ta ke so ya dauke ta don ta huta daga azabtuwa da zuciyarta ke yi da tunanin Abulkhair. Basma ta hango wayarta tsakiyar gado ta dauka ta sanya mata a charging.
Washegari tun asubah da ta yi sallah ta kira Mamanta, Daddynta da Yaya Aboubacarsuka sha hira. Ta ba su labarin zuwansu Niger. A karshen wayarsu kowannensu sai ya ce da ita ta gaida Abulkhair. Kunya ta ji tana kamata, ko dai Abulkhair ya ce musu wani abu ne? Sai kuma ta ce, “Kai ba zai fadi komai ba, tunda Daddy ya ce ya bar masa komai na maganarsu a hannunsa, ba zai yi wannan azarbabin baâ€.
Ita kadai ta yi breakfast a gidan don rashin kwanciya da wuri ya sa duk ba su tashi da wuri ba. Kafin ta bar kitchen Easther ta zo suka gaisa ta bar kicin din bayan ta shirya musu karin kumallon a dining. Basma ta tayar don ta shirya, ta ce mata ba za ta iya shiga makaranta ba yau, akwai gajiya mai yawa tattare da ita. Wanka ta shiga ta fito ta shirya tsaf! Ta kira Joseph a waya ya kai ta makaranta. Sun yi karin sati daya a kan hutunsu, don haka ta tadda note mai yawa a wurin Alex da abubuwa masu yawa da suka soma tsere mata. Sai dai tana tunawa da Abulkhair da alkawarin da ta yi masa ba ta kara kebewa da Alex ba. A cikin aji suke magana gaban kowa, Khaleesat da Yesmin su da ma nasu hutun na sati hudu ne. Islamiyya kawai suke zuwa.
6/28/21, 7:33 AM - Buhainat: HAULATU 66

%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%
Chapter 33 · 0% Book details