Sashe 42
Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
****** Haka Aalimah ta ci gaba da karatu a gidan Kawunta a Boston (Massachusetts) duk shekara suna zuwa gida su yi hutu su koma. Duk kuma zuwan da za su yi da Basma suke zuwa, inda suka girka wata irin soyayya ita da Yaya Aboubacar, yayan Aalimah. Wadda labarinta har Niger, har kunnen Malam Raazee. Da fari bai ce komai ba, don shi ba irin kakannin nan ba ne masu katsalandan cikin maganar auren ‘ya’yansu ko jikokinsu. Aalimah tana shekarar karshe, ita kuma Basma ta gama saboda karatun Aalimah na shekaru biyar ne, Aboulkhair ya kammala shekarar da ta gabata ya fito a cikakken likita mai kwalin MBBS. Ya tafi speciality a kan kwakwalwa a shahararriyar jami’ar da ta yi fice a duniya a kan ilimin psychiatry (wato John Hopkins University), wadda ke garin (Baltimore, Maryland). Duk kawaicin Malam Raazee wannan lokacin ya yanke shawarar tsawatarwa ga ‘ya’yansa biyu kan wannan zuzzurfan ilmin boko da suka dora ‘ya’yansu akai, daga mazan har matan babu mai tunanin yi musu aure a cikinsu. An gaya masa batun Aboubacar da Basma, amma har gobe bai taba jin komai a kan Aalimah da Khaleesat ba, wadda ke aji biyu a jami’a yanzu haka. Idan sun ce karatu, to shi wannan karatun ba shi da iyaka ne, ko ko ba shi da madakata? Kada dauke idonsa ya sa a shiga keta haddin Allah. Aunty Gumsu ta haihu shekaru biyu baya, ta haifi ‘ya mace Nurat. Don haka wannan zuwan da suka yi Niger har Mummy Zulaiha, ya ce a kira masa Mansour yana son ganinsa, ya zo su hadu da sauran ‘yan uwansu a yi ta ta kare kan ‘ya’yansu, ya gaji da ganinsu babu aure bakidaya. Cikin shekarar nan yake son ganinsu a dakin aure bakidaya, daga matan har mazan. Mu’azzam kuma sai sun gaya masa abin da ya hana shi aure. Mu’azzam ya dade da sulhunta Mummynsa da dangin mahaifinsa bakidaya. Har nata ‘yan uwan. Tare da ita suke zuwa duk karshen shekara. Tsakaninta da Inna Kasisi yanzu sai sam-barka, da ma matsalar daga gare ta ne, kuma da ta nutsu ta bude zuciyarta kamar yadda dan nata ya shawarce ta, ta tadda abubuwan yadda ya gaya mata su. Ita kadai ta dauka da zafi, su mutane ne masu son junansu da kaunar duk wanda ya shafe su ba tare da nuna bambanci ba. Sai dai in ka nuna musu su ba wata tsiya ba ne cikin rayuwarka za su nuna maka ka yi kadan ka keta alfarmarsu, ko mene ne takamarka. Don haka wannan zuwan har da Mummy aka zo Niamey. Kwanansu biyu kawu Mansour da Maman Aalimah da kannenta suka iso. Aboubacar bai biyo su ba, sabida aiki. Ba su samu zama da Malam ba sai da daddare. Ya sallami matan ya zauna da manyan ‘ya’yansa maza bakidayansu. “Oussama kai ne babba, kai ne kuma za ka zame min shaida kan cewa tunda ka fara haihuwa ka ke aurar da ‘ya’yanka ban taba shiga ba, ban taba cewa da kai ga abin da ya kamata ba, saboda kai ka san ya-kamatan, ‘ya’ya mata ba sa wuce shekara sha shidda a gabanka. Kaninka Edrissa ya biyo bayanka da wannan kyakkyawan koyi. Amma wadannan (ya nuna Ishaq da Mansour) guguwar zamani ta debe su tana neman kai su ta baro. Babu Allah a ransu sai ilmin nasara wanda iyakarsa duniya babu amfanin da zai yi musu a lahira. Sun aje balagaggun ‘ya’ya maza da mata ba sa ko tunanin yi musu aure. Bayan cikinsu babu wanda ban yi wa auren gata ba, tun kafin ya kama kwalin ilmin bokon don dai in fita hakkin Allah. Nauyin auren bai hana ku zama abin da ku ke son zama ba, don haka ku zama shaida, ko yau na fadi na mutu Ishaq da Mansour su suka yi ajalina. Sun ki aurar da ‘ya’yansu, sun ki gaya min matsalar Mu’azzam, kullum abin nan na damuna a zuciya, da shi nake kwana nake tashi. Shi ma Mu’azzam din ba ya son na yi masa zancen aure, daga shi har Abulkhair ba su da niyyar yi musu aure, balle kannensu mata. Ga Aboubacar shi ma ya dade yana aiki, amma babu abin da suka yi a kan zancensa da Basma, wanda na dade da ji yana yawo a bakin su Bintou. Yau ga su a gabanku su gaya mana gaskiyar lamarinsu. Me suka dauki rayuwar duniya? Wallahi ba inda za ta kai ku idan ba ku bi dokokin Allah baâ€. Ya soma matsar kwallah, duk kuma maganar cikin harshensa Temachek yake yinta. Shiru ta ratsa a falon Malam Raazee. Daddy Ishaq idanunsa sun kada sun yi jazir. Jijiyoyin kansa sun fito rada-rada. Baban Aalimah bai ce komi ba, ko shi yana son jin mene ne matsalar Mu’azzam. Tambaya ta karshe da ya yi masa shekarun baya zuwan Aalimah na farko hutu, da ya tambaye shi cewa ya yi da shi, Mu’azzam addu’arsu kawai yake so, amma ba abinda yamadidi da lalurar tasa zai amfana masa. Don haka yau shi ma ya zuba masa ido a qagare da son jin amsar bakinsa. Maganar Aboubacar da Basma ya santa ba tun yau ba, bai taba daukanta da muhimmanci ba ne saboda a ganinsa Aboubacar ba shi da abin da zai rike Basma, kuma ba za ta iya adopting tashi rayuwar ba. “Kai muke saurare Ishaqaâ€. Uncle Edrissa ya katse masa dogon shirun da ya yi. Ajiyar zuciya ya yi, yau kam ya san ba shi da mafita ban da gaya wa mahaifi da ‘yan uwansa ko wane ne Mu’azzam. In ba haka ba za su yi zaton bai dauke su a bakin komai ba, kuma yana nufin ‘ya’yansa ba nasu ba ne. Mutuncin Mummy Zulaiha a idanunsu yake tattali wanda Mu’azzam din ya samu ya farfado da shi ba da jimawa ba. Ina ga in sun ji ita ce ta illata wa wannan dan da suke matukar so rayuwa bakidaya? Duk da shi ma da nasa laifin, amma tarbiyya a hannun mace ta ke, ita kuma ba ta zauna a gida ba balle ta zama ginshikin samar da ita. Ta debi al’adun al’ummar da ta samu kanta a cikinsu ta yafa gabadaya babu gaira babu dalili. Shirunsa ya kular da Uncle Oussama ya soma fada, da ma shi masifaffe ne. Ya fadi kalamai wadanda ba su yi wa Daddy Ishaq dadi ba. Ya ce don su ba su yi ilmin boko ba ne shi ya sa yake daukarsu ba a bakin komai ba; a wadanda ba su da kwakwalwar fahimtar abubuwa. Daddy Ishaq ya rasa inda zai sa kansa, sai ya soma hawaye. Zuciyar Mansour ta tabu saboda ba ya hada Ishaq da kowa cikin rayuwarsa. Hakuri ya soma ba wa babban Yayansu ya ce Ishaq ba haka yake nufi ba. Zancen ne yake yi masa nauyin fada da alama, ya barshi ya hada zaren maganar da ke bakinsa a hankali. Daddy Ishaq ya ji dadin abin da kaninsa ya ce, ya ce su yi masa alfarma ya kirawo Zulaiha a yi zancen nan a gabanta, amma yana rokon alfarmar abubuwa guda biyu kafin ya fada musu komai. Na daya, su yi wa Zulaiha uzuri su yafe mata kamar yadda ya yi mata uzuri, ya kuma yafe mata. Kowa rai ya yi wa dadi baran mai shi ne. Ta fi kowa kasancewa cikin damuwa da yanayin rayuwar Mu’azzam, kuma da tana da yadda za ta yi da tuni ta fitar da shi daga halin da yake ciki. Na biyu ba ya so zancen nan ya je kunnen mata har Inna Kasisi da Inna Bintou. Malam ya ce yana sauraronsa, kuma ya amince zancen zai tsaya a tsakaninsu su kadai. Mikewa ya yi ya fita, ya tura yaro cikin gidan ya kira Mummy Zulaiha. A nutse Mummy ta shigo falon, ta ratsa ta tsakiyarsu ta wuce ta nemi wuri can nesa da su ta zauna. Malam ya maimaita mata makasudin taron da bukatarsa na aurar da ‘ya’yansu bakidaya a lokaci guda, har Mu’azzam. Idan kuma sun ce rashin lafiya ya hana shi aure, to yau yana bukatar su fayyace masa wace irin rashin lafiya ce da abin da ya raba auren da ta yi masa shekarun baya. Mummy kuka ta saki, a hankali ta rufe fuska da mayafinta. Daddy Ishaq ya ce, “Zulaiha yau zan gaya musu, don ba ni da wanda ya fi su. Dukkaninmu ni da ke masu sakaci ne, amma naki ya fi nawa yawa. Idan Allah ya ce haka Mu’azzam zai kare rayuwarsa babu tsimi babu dabaraâ€. Tiryan-tiryan ya soma ba su labari tun barinsa Nijar zuwa Amurka tare da maidakinsa da dansu guda daya da suka haifa a nan Niamey, wato Ibrahim-Mu’azzam, wanda sunan Malam Raazee na gaskiya ya ci. Shekaru talatin da uku a baya, da duka abin da ya wakana cikin shekarun har zuwa yau shekarar da muke ciki. Falon ya dauki shiru, sai shesshekar kukan Mummy Zulaiha kadai. Jikin Uncle Oussama ya yi sanyi da fassarar da ya yi wa dan uwansa a baya. Uncle Edrissa ya nisa ya ce, “To ku ne kun gama yin amanna da maganar bature da maganinsa, ban da haka ai babu cutar da ba ta da magani sai mutuwa da tsufa. Kuma ni ban yarda wannan cuta ba ce a nahiyarmu, can a kasashenku kadai ake wannan ciwace-ciwacen a ce ba su da magani. Mu a addinin musulunci mun yarda cewa babu maganin da babu a cikin Alkur’ani. Shi din (Alkur’ani) waraka ne, kuma magani ne na kowacce irin cuta. Mu’azzam ya dawo gida, ya rabu da wannan maganin da yake sha, mu yi wanda muka gada iyaye da kakanniâ€. Uncle Oussama da ke kallon Mummy a hasale babu ko digon tausayinta a ransa sabanin sauran kannensa ya ce, “To kukan me za ki damu mutane da shi yanzu? Wanda ya ja ruwa ai shi ruwa kan doka. Ni ban taba ganin mace irinki ba, kawai don kin je kasar turawa sai ki dauki kanki jinsinku daya, ki kasa bambance mai kyau da mara kyau, ki saki koyarwar addininki ki kama ta wadanda tun a duniya Ubangiji subhanahu wata’ala ya gaya mana makamashin wutar jahannama ne su (yahudu da nasara). An yarda babu inda neman abinci da yanayin rayuwa ba ya kai mutum, amma musulmi ya dinga