← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 91

Sashe 51

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Watanni uku cif! Da auren Aboulkhair da Aalimah, Mu’azzam ya yi kokari ya samar mata aikin da ya yi alkawari a asibitin da mijinta yake.Sabida tana zaune a gida bata komai. Wani pharmacy suka tura ta a babban reshensu wanda shi ba asibitin kwakwalwa ne kawai ba, babban asibiti ne General hospital da ya kunshidepartments na kowanne bangare. Sun tura ta wani pharmacy dinsu a Ophthalmology department (bangaren harhada magunguna a tsangayar ido). Kowanne bangare na asibitin akwai pharmacy a cikinsa, don haka duk inda ka ke so a nan za ka sayi magani cikin katafaren asibitin.
Don haka kullum Aboulkhair sai ya fara sauke ta, ya raka ta har cikin ofishinta, ya cire mata abaya ya dora mata farar rigarsu damini hijab dinta da ba sa hana ta sakawa sabida kare martabar addininta, ya rungume ta ya sumbace ta, sannan yake tafiya.
Idan ya riga ta tashi zai zo ya jira ta har ta tashi, sannan su tafi gida. Idan akwai abin da za su saya su biya kasuwa, sannan su karasa gida. Idan kuma ita ce ta riga shi tashi komai dadewar da zai yi haka za ta zauna ta jira shi. Son juna suke kamar su hadiye junansu, ba sa taba gundura da juna. Soyayyarsu mai ban sha’awa da tsafta, wadda duk inda suka zauna sai ta fallasa kanta.
Tun zuwanta gidan Mu’azzam na farko, ba ta kara yarda ta bi Aboulkhair ba, shi kadai yake zuwa. Ta yarda kin mutane da Mu’azzam ke yi, yana da nasaba da mental state dinsa. Da ace za’a bata dama, da ta zauna dasu Basma ta fahintar dasu wanene Yayan su Mu’azzam? A yanzun sun mallaki hankulan kansu sunyi ilmi mai zurfi, sosai zasu yi masa uzri, su bude zukatansu su bashi gurbi. Gurbi na dan uwa mai tsananin kirki kamar Aboulkhair. Maganin wata guda Aboulkhair ke kai masa. Har ta haddace magungunan Mu’azzam don ita ke hadowa ta ba shi. Dose da mgduka ta rike. Rannan yake gaya mata babban likitan Mu’az ya ce zai kara karfin mood stabilizers dinshi, don a samu ya riki wasu al’amuran na social life bayan aiki da ya kwallafa kafatanin rayuwarsa a kansa. Ba ya tunanin kowa, ba ya tunanin komai, babu kowa babu komai a zuciyarsa sai proffession dinsa.

Mummy Zulaiha hankalinta ya dada kwanciya ganin cewa, Mu’azzam ya samu ‘yan uwa a garin da yake, duk da ba gidansu daya ba, ta san ko ya ya ne za su taimaka masa ta wani fannin. Ba zasu barshi cikin ragaita da zaman kadaicin nan nasa ba koda baya so.Ta san cewa, kulawar lafiyar tasa bakidaya ma yanzu a wuyansu ta ke ba.

Aalimah Mansour, na tsaye tana kare wa dan kyakkyawan ofishinta kallo, tana kuma kallon alert na damin kudin da ya shigo mata daga bankinta WellFargo, wai duk wannan albashinta ne na farko. Iyayenta ta shiga yi wa addu’a ba ji ba gani, har Daddy Ishaq ba ta cire cikin addu’arta ba. Wadanda suka tsaya tsayin daka tayi ilmin da ya bata wnnan matsayin. Fitowa ta yi ta rufo ofishin zuwa Atm mafi kusa ta yi wa Daddy transfer na gabadayan kudin, ko dala guda ba ta rage ba, ta hanyar western money transfer. Kudin na shiga Dr. Mansour ya kira Aalimah.
“Kudin me ki ke ta turo mana ne kamar wata ma’aikaciya? Kin yi ya kai sau hudu ina shiru, na yau yafi na baya, ina ki ke samu? Aalimah kada ki kasance cikin masu dora wa mazansu hidimar da ta fi karfinsu don ki wadata iyayenki. Mu din we’re contented with our life ba mu nemi komai mun rasa ba, Aboulkhair me ya tara, yaushe ya fara aikin da ki ke kwakularsa wadannan makudan kudaden?â€
Dariya Aalimah ta yi, sannan ta soma yi masa bayani, cewa kudin farko, na biyu da na uku duk Mu’azzam ke saka mata cikin ATM don ta yi lalurorin gabanta ba tare da ta roke shi ba. Ita kuma ba ta da bukata shi ya sa ta tura musu. Na yau din kuwa halak dinta ne, guminta ne, albashinta ne na aikin da Mu’azzam ya samo mata daDesert Parkway Health Center.
Dr. Mansour kasa magana ya yi, akwai matashi mai zuciyar riko da zumunci a duniya irin MU’AZZAM ???
“Yaa Allah ka dubi wannan bawa naKa da tarin alherinsa da jin kansa ga ‘yan uwa da sauran al’umma, Ka ba shi lafiyar da ka ke jarrabtarsa a kanta, ya yi rayuwa mai dadi kamar kowanne dan Adamâ€. Addu’ar da Dr. Mansour ya shiga yi wa dansa Mu’azzam kenan, wani Da mafi soyuwa a zuciyarsa cikin dukkan ahalin Raazee, manyan su da yaransu.
Chapter 51 · 0% Book details