← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 91

Sashe 72

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin ya dawo an gama komai. Gidansa ya zama sabo kal daga sama har kasa. An zuba wasu gogaggun furnitures farare sol ‘yan kasar Italy an lullube shi da curtains ruwan madara. Dakin sai wani kamshin sabunta yake yi mai dadi. Haka gidan bakidaya an pente shi da wani irin fenti fari kal mai santsi da sheki. Alamu ne na cewa (white) is the favourite colour na mamallakin gidan. Har kitchen ba’a bari ba shima ya sha gyara ta ko’ina da sababbin kitchen cabinets sai daukar ido yake.
Yana shigowa gida daga tafiyar da yayi Mummy da jin motsinsa da sallamar sa ta fito daga daki da sauri har tana tuntube, zaninta na kuncewa. A dugunzume ta tare shi da tambaya ko bari ya huta bata yi ba daga gajiyar zaman jirgin kasan da ya kwaso tun daga SanFrancisco har Las Vegas.

“Mu’az, aure ka yi ne babu labari?â€

Ya lalubi kujera guda cikin tausasan leathers din da ke falon, ya zauna cikin nutsuwa, a lokaci guda yana mai loosing neck tie din wuyanshi shi yadda zai ji dadin zaman. A gajiye yake matuka.
Dariya Mummy ta bashi sosai, ya yi murmushi, ya ce.
“Sai dai in ke ki ka sake yi min babu labariâ€.
Ta daure fuska ta ce, “Ka bar zancen wasa, tsakani da Allah aure za ka yi?â€
Sai a lokacin ya ji gabansa ya fadi dammm! A wancan lokacin Mummy ce ta yi masa; ba ya fatan a wannan karon ya kasance Daddy ne ya yi masa ba da saninsa ba. A dinga janyo wa rayuwarsa bankada da terere yana zamansa lafiya cikin kwanciyar hankali babu gaira babu dalili.
Amma sai ya samu kansa da kasa kiran Daddy ya nemi ba’asi, sabida tsoron abin da kunnuwansa za su jiye masa.
7/5/21, 10:03 PM - Buhainat: KAUSAR LANTO

Da ya koma daki sai ya kasa zaune ya kasa tsaye. Ya shiga safah da marwa. Addu’a yake cikin ransa Allah yasa kada zargin Mummy ya zam tabbatacce. Bashi da sauran buri wanda ya danganci aure a halin yanzu. Ya riga ya mika wuya ga kaddarar data same shi. Baya mafarkin wata rayuwar daban bayan wannan wadda yake ciki. A yadda ya ji muryar Daddy sanda suke waya ya fahimci yana cikin madaukakin farin ciki. Ya san in suna da wani buri a yanzu to bai wuce auren nasa ba, wani abu da shi kuma ya riga ya cire daga dictionary din rayuwarsa. Idan zargin Mummy ya tabbata haqiqa Daddy ya shiga rayuwarsa ta inda bai taba tsammani ba.
Mummy na zaune a falon Mu’azzam, Yesmin na yi mata matsar kafa, komi na duniya yayi mata zafi. Ta shiga tambayar kanta har tsawon yaushe za ta yi ta zama gidan Mu’azzam? Ga shi ba ya bukatar taimakonta a kan komai. Ya samu lafiya sosai. Komai shi yake yi wa kansa, lafiyarsa kuwa Dr. Nebrass ke kula da ita. Hana rantsuwa za ta ce yana amfanuwa da girkinta.
A wannan dan tsukin kewar mijinta na yawan damunta. Ga Yesmin na zaune babu karatu, ta ki yarda tayi karatu a Las Vegas. Ba karamin sabo tayi da Boston ba tun haihuwarta har girmanta. Ga Gumsu can ta samu miji a bagas ita kadai sunata barzar soyayya sai zubo masa ‘ya’ya take, mijin da tafi kowa cin wahalarsa tun bai mallaki komai ba, suna can rayuwa tayi musu daidai sun manta da ita. Ita tana nan tana gadin Dan ta wanda baya bukatar komai daga gareta. Gabadaya ta sauya, hatta Mu’azzam da bai faya shiga shirgin kowa ba ya lura Mummy ba ta cikin walwala a ‘yan kwanakinnan. Ba halinsa ba ne tambaye-tambaye ba, don haka bai tambaye ta ba. Ya san in wanda ya shafeshi ne da kanta zata zaunar da shi ta gaya masa.

A daren ranar suna gama cin abincin dare ya yi musu sallama ya haye sama inda bedroom dinsa yake, ya sha magani ya yi sallolin nafila raka’a hudu da yake yi duk dare kafin ya kwanta. Sannan ya yi light off ya kwanta. Amma tunanin me Daddy ke nufi da shi ya hana shi barci. A hakan da yake a kwance ya lalubo waya ya kira Daddy don ya san su a can yammaci ne, zai same shi a lokacin da ya dace.
Daddy na dagawa ya ce,
“Ya ya aka yi Mu’azzam? Ba ka yi barci ba?â€
Ajiyar zuciya ya yi, cikin damuwa ya ce, “Na kasa barcin Daddy, tunani iri-iri nake yi kan dalilin da ya sa ka sa ni furnishing din gidaâ€.
Ya ce, “Mu’azzam!â€.
Ya ce, “Na’am Daddyâ€.
“Ka san dai ba zan yi abin da zai cutar da kai ba, sai wanda zai amfane ka da mu bakidaya ko?â€
Ya ce, “Kwarai da gaske Daddyâ€.
Kai tsaye ya ce, “To aure na karba maka. Ka yi hakuri da ban yi shawara da kai ba. Nima abin ya zo mini unexpected ne, duk da na dade da wannan niyyar cikin zuciyata tun bayan rasuwar Aboulkhairâ€.

Wuta ta dauke wa Mu’azzam na lokaci mai tsawo. Numfashinsa ya nemi daukewa. Ya rasa a duniyar da yake. Shidewar wucin-gadi ce ta same shi a lokaci guda.

“Daddy, ka san abin da ka ke cewa kuwa?â€
Ya tambayi mahaifin nasa in subdued (cikin karayar murya). Bayan ya tabbatar cikin zahiri ne abinda yake ji din daga bakin mahaifinsa ba mafarkin ido biyu ba. Kuma ta bakin sa yake son ya ji.

“Ni kuwa na san abin da nake cewaâ€.
Ya bashi amsa.

“Daddy, likitoci sun ce maka na samu waraka ne?â€
Girgiza kai yayi kamar Mu’azzam din yana ganinsa. “Ko kadan Mu’azzam, kawai na mika komai hannun Ubangiji neâ€.
Mu’azzam ya yi shiru cikin harhada kalmomin da zai jefa wa mahaifinsa, amma kunyar abin da zai ce din ta hana shi magana. So yake ya ce da shi cikin biyun wanne ya zaba masa? Za su zauna da matar ne ya zuba mata ido har abada a matsayin ta na matar auren sa, yana ci gaba da taking kwayoyin anti-androgens, ko kuwa zai daina shansu ne ya rayu da ita cikin compulsive-sexual behaviour? Da aggressiveness mai iya tashi a kowanne lokaci?
Kamar Daddy ya san abin da yake sakawa da warwarewa a zuciyarsa, sai ya sanyaya murya ya soma magana cikin yanayin rashin nuna karaya,
“Ni dai Ishaq Sarhamu, ban tanadar wa rayuwar ku komai ba, ban zabi daya ba cikin abin da ka ke tunani. Babu kuma likitan da yace min ka warke. Da Allah na dogara. Shi na damka wa rayuwarka Mu’azzam, Ya yi yadda Ya ga dama da ita, na amince (wa man yatawakkal alal-lahi fa huwa hazbuhu). Amma ba zan juri ganinka cikin wannan rayuwar da ka ke yi ba mara future, mara ma’ana, mara focus, mara aspiration. A matsayina na Uba dole in yi wani motsi a kai ko da kuwa motsin nawa ba zai zamo solution ba, ko da motsin nawa ba shi ne daidai ba. A kalla dai na samu sanyi a zuciyata na cewa na sauke nauyin da ke kaina, wanda Ubangiji ya rataya min
Likitoci basu ce bazaka iya aure ba, kaine ka zabi hakan Mu’az sabida bacin ran abinda Halima tayi maka da bakin cikin rasa ita waccan ‘yar Ethiopia. Amma zasu iya taimaka maka kayi normal rayuwar aure kamar kowa based on treatment. Please accept my decision and submit everything to Allahâ€.
Mu’azzam bai san lokacin da ya ce, “Daddy, ita kuma matar fa? Ba ka tunanin me zai faru da tata rayuwar? Me hakan ke nufi ga tata rayuwar? Ba ni da soyayyar da zan ba ta! Ba ni da kaunar da zan raba da ita. I have no feelings a kan diya mace. Daddy wannan zai zama zalunci ne a gareta....…â€.
“Mu’azzam!!!â€
Mahaifin ya kira sunansa da karfi.
‘‘Da kai da Aalimah duka ‘ya’yana ne, ba zan zalunci kowannenku ba, ina da kyakkyawan hope na cewa ban cutar da kowa a cikinku ba. Gata na yi wa dukkanninku.
Ba wanda zata samu da zai yi replacing Aboulkhair a gareta in ba kai ba. Ba wadda zaka samu ta rungume ka tsakani da Allah sama da ita. Ya rage naku ku karbi wannan gatan ko ku hambare shi ku bada mana kasa a ido. Suna nan tafe karshen satin nan, a kara gyara ko’ina na gidan kamar yadda na yi umarniâ€.
Daga haka ya kashe wayar sa. Ba tare da ya bashi damar cewa komai ba.

Ya dade rike da wayar a hannunsa, ya dade yana tauna kalaman mahaifinsa a bisa ma’auni na hankali da tunani. Da ya ji tunanin na son janyo masa ciwon kai, kuma babu wata hanyar kubuta a cikinsa dole ya hakura ya kwanta bayan ya kashe wayar sa. Amma duk yadda ya so ya runtsa hakan bai samu ba. Wani suna da Daddy ya ambata yake son tuno a inda ya san sunan.

“Aalimah!!!â€

Ya fadi sunan a kan harshensa duk dai a kokarinsa na tuno mamallakiyar sa. Wa ya sani da wannan sunan a duniya bakidaya ban da matar rabin ransa ABOULKHAIR???

Mu’azzam ji ya yi duniyar na yin katantanwa da shi kafin ta dire shi a kan tsakiyar gadonsa. Tambayar kansa ya shiga yi; tsakanin shi da su Daddy wane ne mai cutar kwakwalwa? Wa ya fi dacewa da karbar rehabilitation? In har Aalimar da ya sa ni suke nufin sun karba masa auranta, tabbas lokacin da zai yi gammo ya bar gari ya zo kafin su zo su tadda shi. Abu na karshe da ba zai iya ba ko duk duniya za ta taru a kansa!!!
Chapter 72 · 0% Book details