← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 91

Sashe 4

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A Yamai Zulaiha ta haifi danta na fari, wanda Ishaq ya radawa sunan mahaifinsa ‘IBRAHEEM MU’AZZAM’, shekarar Mu’azzam daya Ishaq ya samu aikin da ya kai shi kasar Amurka a Niger Consulate America. Suka tattara suka koma kasar Amurka shi da iyalinsa.
Ya jima yana aiki a consulate na kasarsu kafin hanyoyi su bude masa sosai, ya koma karkashin siyasar gwamnatin kasar mai tabbataccen aikin gwamnati a hannunsa, ya ajiye aikin consulate a gefe ya zama dan kasa mai zaune da cikakken lasisi. A can ya haife sauran yaransa hudu daya bayan daya; Abulkhairi, Basma, Khalisat da Yasmin. In ka hada harYayansu haifaffen Yamaisun zama su biyar kenan.
Bayan dawowarsu Amurka Mummy Zulaiha ta ci gaba da karatu, inda ta yi digirinta a fannin tsimi da tanadi (Economics). Yanzu haka MummyZulaiha Raazee ma’aikaciyar banki ce da (JPMorgan Chase). Girman kai da fadin raisai abin da ya karu cikin halayenta. Al’adunta duk sun juye sun zama na al’ummar da ta ke zaune da su.
A hakan kuma ta raini ‘ya’yanta mata guda uku, mazan kam Babansu na matukar kokari a kansu, a halin yanzu yana jan su a jikinsa yadda ya kamata.He’sspending most of his leisure time with them yana dora su a kan tafarki mai kyau tun bayan mummunar kaddarar data shigo rayuwarsu. Da ma an ce ‘ya mace ta Uwarta, Da namiji na Ubansa.

Suna daukar lokaci ba su je Yamai ba, amma in suka je din suna jimawa. Suna kuma zuwa Kano wajen dangin Mummy, saboda mugun hali irin na Zulaiha ko nata dangin ba ta ja a jikinta, ba ta taba daukar wani nata ta kai inda ta ke ba. A haihuwar Basma ne shi Ishaq ya biya wa mahaifiyarta da Yayarta da Inna Bintou suka je, Inna Kasisi ta ki zuwa, don ba ta son duk wani sha’ani da zai hada ta inuwa daya da Zulaiha, zuciyarta ba za ta dauka ba.
*****

3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price 1&2 N400
6/28/21, 7:31 AM - Buhainat: 🌹 *Aalimah**🌹
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI**

07030137870

FREE PAGES 3

MANSOUR RAAZEE
Sanda Yayansa Ishaq ya koma gida Yamai, shi kuma jami’ar ta rike shi don ya yi mata aiki bayan kammala hidimar kasarshi. Ya je ya ga iyayensa, ya kuma gaya musu samun aikinsa a inda ya yi karatu, atafau Inna Kasisi ta ce ita ba ta yarda ba, tunda babu Ishaq ya dawo gida ya nemi aikin ya yi aure. A nan yake gaya musu ya samu mata a Zaria abokiyar karatunsa. Nan ma Inna Kasisi ta yi tsalle ta dire ta ce ba ta yarda su kara yo mata wannan auren ba, ga Zulaiha nan da aka auro ba dadinta suke ji ba.

Mansour, ba shi da abin da zai ce da mahaiafinsu a duniya sai Allah ya ji kansa, ba don ya mutu ba. Yadda yake din bai yi karatun zamani ba, amma wayewarsa da rayuwa da yadda yake tafiyar da tsarin rayuwarsa babu matsi babu takura ga ‘ya’yansa, in har ba addini suka kauce wa ba, wane wani Farfesan. He is very soft on them (shi mai tausasawa ne a garesu). Shi ya tsaya masa ya auri ‘Aseeya’ diya ga shugaban jami’ar na wancan lokacin.
Aseeya ‘yar ajinsu e wadda ta fi duk ‘yan ajin kankantar shekaru. Babanta V.C, uwarta Dr. duk a jami’ar Ahmadu Bello. Asalinsu ‘yan Maiduguri ne daga kabilar Margi, aiki ya kawo mahaifinta A.B.U Zaria inda mamanta ta yi doctorate dinta a Microbiology, ta fara lecturing a nan itama, shi kuma yana matsayin V.C.
A nan cikin A.B.U aka haife su ita da Yayanta Suraj, ajinsu daya ita da Mansour Raazee a tsangayar aikin jarida.
Da fari haduwar jini ce tsakaninsu da aron note da yin tutorial in jarrabawa ta matso wanda ya rikide ya koma soyayya tsantsa. Tun abin bai yi nisa ba iyayenta suka so su dakatar kasancewar Mansour bakon haure. Suna tunanin watarana zai dauke musu ‘ya, ya mayar kasarsu.
Amma da Malam Ibrahim Sarhamu Razee ya tako da kansa tun daga Niamey shi da manyan ‘ya’yansa Oussama da Edrissa suka zo har Maiduguri nema wa dansu auren Aseeya, Prof. Kashim, kasa badawawannan farin ba’abzinen dattijon mai kama da Larabawan Hijaz kasa a ido ya yi, sabida haiba da kamalarsa. Ya kuma yi duk iya binciken da zai yi a kan Mansour, inda ya tarar asali kam sai dai ya gaya wa Aseeya, tun kafin zuwan Malam Ibrahim.
Ba da jimawa ba aka yi auren Aseeya da Mansour, suka tare a gidansa da jami’ar ta bashi, shekara na zagayowa ta haifi Da namiji, ya sa masa suna Aboubacar.
Sai da Aboubacar ya shekara bakwai aka haifi ‘AALIMAH’, ita ma sai da ta shekara biyar aka fara yi mata kanne; Sultana, Suhaima da Sabrina.
Har inda yau ke motsi Baban Aalimah Malamin jami’a ne mai matsayin Dr., Amma sun bar Zaria sun koma jami’ar Bayerota Kano bayan rasuwar mahaifin Aseeya, wato Prof. Kashim, mahaifiyarta ta koma Maiduguri cikin danginta.
Wannan ya tayar da hankalin Aseeya ta ce ba za ta iya ci gaba da zama cikin A.B.U ba, tana kallon kofar gidan da iyayenta suka rayu, hakan yana dawo mata da memories na rayuwarta tare da su. Har sai da ta samu matsala a kwakwalwarta (anxiety). Duk son da Mansour ke wa A.B.U haka ya barta ya koma Bayero don kwanciyar hankalin maidakinsa.
A sannan ne suka fahimci wani babban jigo nasu a Nigeria ya fadi (Prof. Kashim), ta ajiye aikinta da ta ke yi a gidan talbijin, sai abin da Mansour ya kawo, kusan komai da ta saba na rayuwarta dainawa ta yi. Da aka raba musu gado ta yi wa nata adani sosai a banki da wani kuduri a zuciyarta.
Yana kai ta Maiduguri akai-akai wajen mahaifiyarta da danginta, kuma suna zuwa Yamaiwajen nashi iyayen a duk sanda suka samu hutu.
A sannu Inna Kasisi ta fahimci Aseeya ba halinta daya da Zulaiha ba, they are totally opposite in every aspect.
Sonsu ta ke da zuciya daya, tare da girmama ko da kare ne in dai daga Nijar ya fito, sabida son da ta ke wa mijinta,. Yayanta Suraj ya bar kasar tun mahaifinsu na raye, tun daga zuwa karatu a kasar Canada ya yi zamansa a can musamman da mahaifinsu ya rasu, mahaifiyarsu ta koma Maiduguri, bai kara sha’awar dawowa Nigeria ba.
*****

Aalimah tun suna kanana suka taso da fahimtar cewa, mamansu is a mental patient, sannan suka fahimci Babansu na tsananin sonta. Tana daukar lokaci lafiya kalau don tana kan shan magani, amma in abin ya tashi ba Babansu kadai ba su kansu suna jin jiki. Babu duka babu zagi sai kuka. Za ta kwana ta wuni tana kuka kamar ranta zai fita babu gaira babu dalili. Ta bar shiga komai nasu, ta bar yi musu girki. A irin wannan lokacin Babansu ke yi musu komai; wanka, girki, shirin makaranta, wankin uniform da dukkan hidimar da uwa ke yi wa ‘ya’yanta.
Da Aboubacar ya soma hankali shi yake kula da Maman. Baban ya kula da su ita da su Sultana. A haka suka taso da wata irin shakuwa matsananciya tsakaninsu da Babansu, Mamansu tana da tsauri a kan tarbiyyarsu, hakan ba ya nufin ba ta sonsu, amma tana da zafi. Ba su nemi komai sun rasa ba, amma ba su da wadatar da sauran ‘yan uwansu na Yamai ke da shi.
Babansu bai dogara da komai ba sai albashinsa, sannan ba shi da halin rokon ‘yan uwa wai don sun fi shi wadata. Ya dogara da kansa ya tsare wa iyalinsa komai na bukatun rayuwa daidai misali, irin na kowanne cikakken dan boko. A halin yanzu Dr. ne shi a jami’ar Bayero a tsangayar kimiyyar sadarwa.
Aalimah na matukar son zuwa Yamai, ta iya harshen mahaifinta sosai don kusan duk wani hutu mai tsawo a can ta ke yinsa. Inda za ta hadu da ‘yammatan family sa’anninta su Balkissa ‘ya’yan Kawu Oussama su yi ta dabdalarsu tun suna yara. Ko a cikin jikoki Aalimah ta daban ce a wajen Kakansu. Sakamakon ita kadai ya sanyawa sunan mahaifiyarsa.
Yana sonta son da ba ya iya boyewa, kowa ya kwana da sanin hakan a familyn, Aalimah ce ta gaban goshin Mallam. Kuma shi ya zaba mata wannan suna na Innarsa (Aalimah) wato mai ilmi.

‘Margi’ da ‘Abzin’su suka hadu suka haife Aalimah, don haka na bar wa mai karatu ya siffanta kamannin Aalimah Mansour yadda yake so. Babu wanda ya damu da yin wani abu wai shi auren zumunci a wannan family kowa yana kawo wanda yake so ne ya aura, don haka babu rikici babu rashin fahimta, kansu a hade yake kamar tsintsiya. Sai dan abin da ba a rasa ba, wanda ba ka rasa shi a kowanne extended family, shi ma ya fi yawa a tsakanin faccaloli (matan ‘ya’yansu), amma jikokin gidan da ‘ya’yan gidan kam kaf dinsu kansu a hade yake.

Haduwar Aalimah da Mahmoud ta faru ne tana ajin karshe a sakandire ta staff school inda ta yi sakandire. Mahmoud abokin Yaya Aboubacar ne, tare suka yi karatu a nan B.U.K. Mahmoud bakatsine ne, wanda ya fito daga karamar hukumar Kaita ta jihar Katsina.Da suka zo yin hidimar kasa aka kai shi wata makaranta da ke daura da sabuwar jami’ar Bayero.
Daddyn su Aalimah ya san irin abotar da ke tsakanin Aboubacar da Mahmoud, don haka da Aboubacar ya zo yana nemawa Mahmoud alfarmar zama tare da shi a nan boys quartersdinsu wajen mahaifinsu, Daddyn ya amince, amma kuma ya ce masa ya gaya wa Mahmoud dokarsa ita ce; karfe tara na dare yake rufe gida, in ya amince ya zo ya zauna babu laifi.

Zaman Mahmoud Kaita a gidan Dr. Mansur Razee zama ne na aminci. Ya samu iyalin Dr. mutane masu karamci, tarbiyya, tsantsar ilmi da son junansu. Dole duk wanda ke gaba da kai a haihuwa ka ce masa ‘Yaaya’, ka dinga respecting dinsa. Wannan ne babba abinda ya ja hankalin Mahmud ga son hada jini da iyalin Dr. Mansour Raazi. Tsakanin Daddy da yaransa auzinanci suke yi ko yaren Temachekwato harshen Inna Kasisi, Mama ce kadai ke musu Hausa da Turanci. Wani lokacin ma tana musu Margiduka ba wanda ba sa ji. Duka yaran gidan sun saba da shi, suna kula shi kamar Yayansu Aboubacar, banda Yayarsu Aalimah.
Chapter 4 · 0% Book details