← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 91

Sashe 29

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dattijo Ibrahim Raazee ya yi ajiyar zuciya. Ya dubi jikokinsa biyar da ke zaune a wajen ciki har da Aalimah. Sannan ya kai dubansa ga Basma wadda ta fi kowa kaifin baki cikin jikokinsa. Ya ce da ita cikin auzinanci, “He is not annoying, he is compassionateâ€. Ta daga manyan idanunta irin nasa da suka gado, ta dube shi, “Non Grand pere (a’ah Kaka), he’s annoying, and he don’t like usâ€. Sai ya yi murmushi ya kyale ta suka shiga wata hirar. Ya fahimci babu wanda zai kankare wannan belief din daga zuciyar Basma, na cewa, Yayanta mutum ne mai ban haushi, mara dadin mu’amala, sannan ba ya sonsu. A can dakin Inna kasisi ta gama duk sabgoginta ba abin da ya rage mata a tsakar gidan, dole ta koma dakinta ta yi alwala ta tada sallah. Duk Daddyn Basma yana zaune sunkuye da kai ya kasa cin nau’ikan abincin da aka tara masa a gaba. Sai da ta idar ta yi addu’a ta shafa, sai ta ci gaba da zama a kan sallayarta. Ya ga cewa wannan ita ce damarsa ta karshe, kada ta sake ficewa a dakin. Ya shiga rarrafawa a kan gwiwoyinsa har ya tadda ita. Hannayenta biyu ya kama ya rike cikin nashi, sai kuma ya kwantar da kai a cinyoyinta ya fashe da kuka. Cikin kukan yake rokonta ta yafe masa, ya gane dukkan kurakuran da ya tafka da kansa, ya yi nadama ya dauki niyyar gyarawa, in ma cewa ta yi ya baro kasar Amurka ya dawo gida zai yi mata wannan biyayyar. Tun zuciyarta na tururi har ta soma karyewa. Shi din ba karamin yaro ba ne ya ba wa hamsin baya, har da furfurarsa. Amma ga shi yana kuka cikin tsananin nadama, ta gode wa Allah da hakan ta faru da sauran numfashinta. Ta san kaidi irin Jai mazajensu jahannama a dalilin fushin iyaye. Lokaci ya yi da ita ma za ta nuna wa Zulaiha matsayinta na UWA mai cikakken iko a kan danta, ba ita da ba ta da ikon komai a kansa ba, shi ne ma yake da shi a kanta. “Mon pilsâ€. Ya ji ta ambata ayayin da ta kai hannunta cikin tarin sumar kansa. Mon pils na nufin DANA. “Na yafe maka duniya da lahira. Ka je wajen mahaifinka ya dawo tun dazunâ€. Dagowa ya yi idanunsa sharkaf da hawaye yana yi mata godiya. A yadda ya san taurin rai irin na Innarsa bai zaci wannan yafiyar ta gaggawa ba. Allah kadai ya san shekarun da ta kwashe tana kwankwadar damuwa da bacin rai a kansa. Dakin Malam ya nufa, nan ya tadda su Aalimah suna ta shan hira da kakansu. Kana jin tashin muryar kowaccensu tun daga bakin kofa ana ta auzinanci mai cakude da faransanci, amma ban da ta Aalimah. Da ya yi sallama ya shigo duk suka yo kansa da magana, Aalimah tana daga gefen daman kakan tana danna wayar hannunta, nutsuwar yarinyar da rashin hayaniyarta na burge shi. Sai ta tuna masa da dansa Mu’azzam, haka yake shi ma, in za ka ji muryar mutum goma a wuri ba za ka ji tashi ba. Wani tsananin tausayin Mu’azzam ya kara lullube shi. To shi Mu’az haka zai karasa rayuwarshi babu farin ciki babu future kawai don Allah ya dora masa lalura? Hawaye ya ji sun ciko idonsa, ya yi sauri ya dauke su da yatsun hannunshi, duk a kan idon mahaifinsa. Duban yaran ya yi, ya ce duk su je su yi sallar la’asar lokaci ya yi. Ya rage daga shi sai Babansa. Sun gaisa sosai, da tambayar iyali da hidimomin rayuwa. Ya ba wa Malam hakurin tsawon lokacin da ya dauka bai zo gida ba. Ya roke shi ya taya shi kara bai wa Inna hakuri. Ya yi alkawarin canza tsarin rayuwarsa. Ya gane mutum komin matsayinsa a duniya shi ba komai ba ne in babu albarkar iyaye a tare da shi. Duk tsayin shekarun nan ba wai dadi ne ya boye shi ba, ko kwanciyar hankali. Sam ma zai iya cewa tun shekarunsa biyu a American rabonsa da kwanciyar hankali, wato tun haihuwar Abulkhair. Matsalar rashin lafiyar Mu’azzam bai taba barinsa cikin kwanciyar hankali ba, bai barshi ya tara komai ba, kawai dai ya fi karfin abin da iyalinsa za su ci da bukatocinsu, sai gidan da ya mallaka da abin hawa. Shi ma wani babban mai mulki a siyasar kasar da yake aiki a karkashinsa ne ya mallaka masa su. Komai na rayuwarsa a American da iyalinsa ya fede wa mahaifinsa, amma ya zaftare duk wani abu da ya shafi rayuwar Mu’azzam, saboda shi kansa ba ya son tunawa, kuma ba zai iya tattauna wannan al’amarin da kowa ba ban da Abulkhair, Zulaiha kuwa ba don rashin yafiyarsa gare ta da yin Allah ya isa gare ta a kansa zai kare ba, da sai ya yi mata. Hira ce aka yi tsakanin uba da Da irin wacce ba a taba yi ba. Malam ya fahimci rayuwar dan nasa sosai, ba wai daular duniya ta boye shi ba, shi ma a can inda yaken matsaloli ne dankare tare da shi. Ba za a sanya Ishaq Raazee matsayin attajirai a Amurka ba, amma yana da rufin asirinsa irin na diaspora. Kyakkyawan lodge da rantsattsun motocin hawa guda uku. Ga parmanent aikinsa a hannu. Sannan matarsa da ke aiki da babban bankin kasar Amurka ta fi shi tara abin duniya. Aikin Mu’azzam da kamfanin man fetur na CHEVRON CORPORATION ya kara taimakawa wajen rufuwar asirinsu. Kasancewar Mu’az din wani mutum da bai san dadin abun hannunsa ba, saboda ba shi da buri, ba shi da future planning a kan komai. Aikin ma yana yinsa ne don kar ya zauna ba ya komai, yana kuma biyan kudin hayar mansion din da yake ciki. Shi yake biyan kudin makarantar Abulkhair baki daya, duk da cewa abin da yake biya din babu yawa kasancewar Abulkhair dan kasa ne, a can aka haife shi, duk cikinsu shi kadai ne mai nationality din Nijar, ba zai iya manta wahalar da Daddy ya ci a kan nasa karatun ba lokacin yana consulate officer karkashin ofishin jakadanci na kasar Nijar a kasar Amurka, lokacin Daddyn ba shi da hanyar samu mai yawa. Don haka zai iya cewa yana da buri a kan DADDY, ya kasance cikin wadata shi da wadanda suka shafe shi da kannenshi. Bayan wannan ba shi da wani solemn buri a rayuwarsa. Daga sanda ya fara aiki da Chevronya dauke wa Daddy hidimar lafiyarsa. Sai da suka gama hirar suka soma labarin ‘yan uwa na nan kasar da Mansour da ke Nigeria. Mahaifin nasu ya tambaye shi ko shi ne ya sanya Mansour ya ba shi rikon Aalimah? Nan ya yi masa bayanin yadda komai ya kasance. Cewa, Mansour din a kan-kansa shi da maidakinsa suna da burin Aalimah ta yi karatun a Boston jami’ar da mahaifin maidakinsa ya yi ce. Ya gaya masa tun kafin hakan ya sha rokon Mansour ya ba shi yaran guda biyu (Aalimah da Aboubacar), amma ya ki. Sai kuma ga shi shi da kansa ya neme shi ya gaya masa ya samo mata scholarship a garin da yake. Malam ya jinjina son boko irin na Mansour a wasu lokutan har ya fi Ishaq muhimmanta ilimin boko. Kamar daga sama mahaifin nasa ya jefo masa tambayar da ta birkita shi. “Me ke damun takwarana Mu’azzamu? Kun dade kuna ce da ni ba shi da lafiya, amma daidai da rana daya daga kai har shi ba wanda ya taba bude baki ya gaya min hakikanin me ke damunsa. Ban taba ganinsa da wasu kamanni ko alamomi na mara lafiya ba. Karewa ma duk ya fi ku kyakkyawan tunani da tsinkaye. Ya fi ku son zumunci da muhimmanta shi. Rashin lafiyar me ku ke cewa yana yi da har ya sanya ku yi masa wani irin aure da har gobe ba mu ji karshensa ba? Sannan me ya hana shi yin aure a halin yanzu a wannan gabar ta rayuwarsa?†Gumi (zufa) Daddy Ishaq ya shiga tsattsafarwa daga kowanne sashe na jikinsa, ya kuma kasa amsa tambayoyin mahaifinsa. Malam din ya tsura masa ido, ya kuma fahimci halin rudanin da maganganunsa suka jefa dan nasa. Take wasu tunaninnika marasa dadi suka shiga darsuwa a ransa. Ya kaurara murya ya ce, “ISHAQA!†Ya dago a hankali ya dubi mahaifinsa. “Mu’azzamu kanjamau gare shi ko (yana nufin acquired immune deficiency syndrom)?†A firgice Ishaq Raazee ya ce, “A’ah, non, quite non, pereâ€. Yana ganin yadda mahaifin nasa ya sauke wata boyayyar ajiyar zuciya, ya lumshe idonsa irin na samun kubuta daga tunanin da ya dade yana wahalar da mutum. Sannan ya ce, “Gaya min gaskiya, shi ba namiji ba ne to?†Cikin yamutsa fuska da rashin fahimtar hausar ya ce, “Malam, kamar ya ya shi ba namiji ba ne?†Sai Malam din ya sauya harshe, ya yi masa bayani yadda zai gane da abzinanci. Yana nufin wanda ba zai iya biyan bukatar auratayya ba. Ya fada masa gaskiya, in wannan ce matsalar Mu’azzam ba wani abu ba ne, babu irin maganin da bai sani ba a rayuwarsa, in ma shi bai sani ba, to ya san inda zai kai shi a yi masa maganin lalurar a Tessoua. Daddy ya rasa yadda zai yi. Bai san wane bayani zai masa ya fahimta ba. Lalura ce irin wadda bai taba sani ba a duniyarsa, kuma za ta yi masa wuyar fahimta. Nan dai ya tabbatar masa wannan ba ita ce matsalar Mu’azzam ba, sannan ya yi ta kame-kame. A karshe ya ce, likitoci suna kan bincike da sun fadi sakamako zai gaya amsa. Amma ya tabbatar masa ya kwantar da hankalinsa, Mu’azzam ba ya tare da ko daya daga cututtukan da ya ambata a sama. Suna haka sauran ‘ya’yan Malam suka soma shigowa shigifar daya-bayan-daya daga gidajensu, daga unguwanni daban-daban da suke zaune a nan Niamey (Yamai). Daga ‘yan cikin Innarshi zuwa na Inna Bintou abokiyar zamanta. Kai ka ce Larabawan Kuwait ke shigowa suna zazzaunawa. Musabiha ce ta rika gudana tsakanin Ishaq da ‘yan uwansa, sai tambaye-tambayen lafiya da iyalin juna. Su goma sha tara cif! Sauran shidan mata ne a gidajen aurensu. Mansour da ke Nigeria ne kawai babu a cikinsu yau. Cikin su mutum biyu ne
Chapter 29 · 0% Book details