← Book details A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 60

Sashe 6

A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Zuwanta wajen aysha da dawowarta....farincikin data samu na ganin yarinyar ta dawo cikin cikakken hayyacinta da wata lafiya data sanya kumatunta cikowa shine ya haifar da sakewar fuskarta,ya kuma saka mata farincikin da ta kusa mantawa da abinda ke tunkararta a gobe.
Kallon masu kallo da idanun masu sanya idanu tun daga qofar gidansu da lafiyayyar motar ta ajiyeta bai dadata da qasa ba,har zuwa sanda ta isa tsakar gidan,ta kama matakala tana haurawa zuwa saman nasu.
Tana sanya qafarta sukayi kacibus da momma dauke da tray da lemuka da ruwa akai.
"Yauwa yanzu nake shirin kiranki......kina da baqi suna qasa,ki hanzarta ki samesu" Ta gaya mata tana rabata zata wuce
"Baqu momma?,su waye?,daga ina kuma?"
"Kinga duka wadannan tambayoyin ki adanasu idan kinje kyayi musu.....me lalle ma ke take jira tunda kika fita". Ambaton sunan me lalle saiya fara dagula mata lisssafi,bayan dirje fatar da aka dameta dashi na kwanaki kusan goma yanzu kuma wani me lalle ne na daban zata zauna yi?,salon a bata mata hannu da qafar da bata shirya diga musu komai ba?.
Ganin momma tayi gaba har tana gangarawa qasan stairs din ya sakata itama ta laqume dukka tambayoyinta tana wucewa ciki. Zuciyarta fal da saqe saqe ta sauya abayar jikinta zuwa wata sassauqar doguwar Riga cotton me gajeran hannu data zauna daidai jikinta,ta dauki qaramin hijab daya tsaya mata iya kafadu ta maqala ta juyo tana saukowa.
Dukkansu su biyun suka amsa mata sallamar idanunsu a kanta
"Tubarkalla ma sha Allah" Zuwaira da tayo rakiya ta qarfi da yaji don ba haka Hajja taso ba ta furta kyan sabreen yana bugar da ita. Duk yadda take jin hira da yadda aka tsara komai bata taba kawowa kyan yarinyar yakai haka ba,ta dauka maamah din nada tsananin wayo......zata dauko yarinyar da bata da cikakken siffa gudun juyewar reshe da mujiya. A iya sanin data yiwa halittar 'ya'ya maza masu jarabtuwa da kyakkyawar mace komai kamewarsu kuwa. Sanda suka iso gidan batayi tunanin gidan masu matsakaicin qarfi da gata irin wannan yana qunshe da kyakkyawar sura har haka ba,taci gaba da qare mata kallo yadda shape me qirar Coca-Cola ya fita sosai ta cikin rigar ta wajen qugunta.
Duk kallon da zuwaira ke qare mata hankalinta baikai ba,saboda hankalinta daya tafi akan hajja da suka fara hada idanu. Ta yaya zata manta fuskar matar?,bayan tana a wajen sanda sukazo da tallar qazamtacciyar hajarsu?,kuma kusan itace tafinta a wajen matar dake iqirarin mahaifiya take a wajensa.
Yadda sabreen din ta tsareta da idanu tana zama a dosane a hannun kujera irin yadda takeyi idan zuwan mutum magana ko mu'amala dashi baiyi mata ba
"Sannu ko?" Hajja ta fada tana qaqaro murmushin dole. Wani irin kishi me girma ya sauko mata akan Sabreen din. A haduwarsu da suka taba yi qwaya biyu hankalinta bai taba kaiwa kan sassanyan kyan da yarinyar ke dashi ba. Wani irin halakakken kyau dake boye a kowanne sashe da kuma halittarta. Anya wannan ba kuskure bane?,idan har tayi saken daya fadawa sonta rabasu kuwa zai zama abu me sauqi kuwa?.
Tabbas bata taba kula da wannan kyan ba,wanda inda tasan dashi tana da dukkan makaman da zata rusa tafiyar........a yanzu bayan komai yayi nisa ta yaya zata katse wannan wasan da bata taba ganin abinda maamah ta ciwa buri a kansa har haka ba.
"Yauwa sannu" Sabreen ta maida mata da salon yadda tace da ita. Haka kawai taji ba zata iya gaida matar ba,tun a waccar ranar duk wata kima martaba da kuma mutunci da ake ganin dan adam me girma da shekaru nasu duka su biyun suka kwaranye mata.
"Ya gida ya shirye shirye?" Hajjan ta sake dauriyar fada yadda sabreen din ke shan qamshi yana qara qona mata rai,amma duka wannan ba komai bane......tasan s nan kusa zata fahimci wace ita?kuma su waye su.
"Alhamdulillah" Ta sake amsa musu. Kai tsaye hajja ta gabatar da abinda ya kawosun,da dukkan alamu sun nuna ba'a maraba dasu ata nan din
"Saqone daga mamarki" Hajja ta fadi tana turawa zuwaira akwatin,ita kuma tana sadar dashi xuwa ga sabreen dake binsu da idanu.
08187255862
Page 8
Duniya ta
Sai data qarewa akwatin me ruwan gold kallo,sannan a nutse ta aza kallonta akan hajja,don tayi yaqinin itace jagorar tafiyar kamar wancan karon.
Kallon kallo ne dake nufin ina buqatar qarin bayani. Da yake hajja din 'yar gari ce har ta fahimci ma'anar kallon,ta saki wani qaramin murmushi sannan tace
"Kusan duk inda akace ana arziqi tsiya guduwa takeyi.....lallai ba shakka kina cikin matan da sukazo duniya a sa'a da har tarihi zai baki daman kasancewa matar muhammad jadda.......wannan suturan ta lashe miliyoyin kudi.....kuma an tanadeta ne kawai saboda ki sanayata a ranar da za'a miqa ki zuwa gidan fuad,wannan shine burin uwar mijinki da kuma umarni na farko da takeso ki fara dauka cikin tafiyar ku......lallai ne muddin kika kasance me biyayya ina miki busharar keda sunan talauci kinyi adabo.... Aiki ne na qididdgaggun watanni,amma ribarsa zaki ci gaba da cin gajiyarta har qarshen rayuwarki data zuri'arki". Idanu ta lumshe a nutse sannan ta budesu. Tana jin wani murmushi yana taso mata daga qasan zuciyarta amma kuma batason bayyanarwa hajja dashi. Shin sun dauka ita din wawiya ce da har zata aminta da komai daya fito daga garesu?,sunyi tsammanin shirunta galaba ce a tare dasu?,ko sauraro da dakonta a kansu suna tsammanin alkhairi ne?.
Zamowa tayi a nutse daga saman kujerar ta zauna a gabansu gaba daya tana langwashe qafarta. Idanunta tsakiyar na hajja ta soma magana da nutsuwar nan tata dake qarawa maganarta kwarjini da fahimta a muryar me sauraro
"Ina zaton aikin data nema daga gareni zaya tsaya ne kawai iya kan danta.......aiki kawai tace zanyi mata na wata uku ko hudu......bata da hurumin komai cikin rayuwata.....kama daga cima ko sutura......" Ta tsaya iya haka tana maida numfashin bacin rai. Ranta ya fara dugunxuma na ganin yadda suke qoqarin maida rayuwarta tamkar gare gare tsakanin uwa da d'anta da suka zamo tsatso daya......abinda sam ba zata lamunta ba kenan,ita tayi mata......danta ma yayi mata?,shin ummeeenta su ta haifawa su?.
A mamakance hajja ke binta da kallo,bata taba zaton haka daga gareta ba,kallon hajjan ya isheta hakanan,dom haka ta miqe cikin rashin damuwa tana gyara lullubin kanta tace da ita
"Ki gaya mata damuwarta ta tsaya iya kan aikinta kawai......indai tace zata hada da shigar da rayuwar sabreen......komai bazai tafi yadda take tunani ba.....ni din tamkar wahainiya nake a wasu lokutan.....sawun keke da gane gabansa yake da wahala koda a wajen gwanaye".
*MAAMAH*
Idanunta ta runtse bayan hajja ta jera mata dukkan wadannan bayanan da sabreen ta aiko mata dasu ba tare data rage komai a ciki ba.....koda ta manta wani abun zuwaira dake gefe tana taso mata dashi. Ta bude idanunta cikin bacin rai tana duban akwatin da iya shi daya kawai kudi ta zuba masu yawa,banda kayan banda kuma aikin da akayi akan kayan.
"Yarinya ce qarama tabbas.....amma na yarda da gaske tana da hadari........tana kuma da wasu boyayyun abubuwan da bamusan dasu ba......iya kalmominta na yau sun sake zaburar dani akan dole na ninka shirina a kanta......amma ba wannan ba.......asarar data sani nayi tun a matakin farko yafi damu na....."
"Kada ki damu.......akwai mataki na biyu da nayi imanin ba zata tsallakeshi ba......saidai shi na biyun bangare daya ya qunsa.......bangaren cusa soyayyarta a zuciyar fuad ya saraya,saidai a samo masa wata hanyar ta daban". Ajiyar zuciya maamah ta saki tana jin sassaucin tashin hankalin dake sauko mata
"Wannan dinma wahalar da nayi a kansa bazai tafi a banza ba.....koda bataso sai tayi amfani dasu,ta hanyar da takeso ko ta hanyar da bataso bata kuma shirya mata ba". Daga haka ta jawo akwatin ta cusashi qasan lafiyayyen gadonta.
......
Chapter 6 · 0% Book details