← Book details A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 60

Sashe 33

A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Daga wannan ta yanke wayar. Zare wayar daga kunnenta maamah tayi tana kallo. Wani irin mamaki da tsoro yana kamata,wacce irin yarinya ce wanannan?,wadda bata tsoro ko shakkar duk wani abu girman tsoron dake tattare dashi?. Gabanta yayi mummunar faduwa sanda ta tuna zancan idan taso za'a sanar da jana'izar fu'ad din a gobe. Ta motsa da wani irin hanzari ta miqe sai kuma ta koma ta zauna. Waye zata gayawa?,shi fu'ad din?,tace yakula da za'a iya kasheshi?,to waye zai kasheshin?,ya kuma zatayi masa bayani akan yadda akayi ta sani?,ya daina cin abinci?,wannan kuma shine burinta babba a yanzu ya karbi abinci daga hannunta don samun cikar burinta,ta yaya zata sanya idanu akan wani abu daban da zata shirya wanda zai sauka daga kan tsari da kuma muradinta?. Zuwaira ce ta fado mata rai,sai taji tana samun sassaucin tsoron da kuma firgicin da take ciki. Hannunta dukka biyun ta sanya ta dafe kanta. "Huda,ya kula da ita ya bata magani tasha?,who's she?" Abinda ta dinga maimaitawa kenan. Hudan da har yanzu take ganin tana buqatar therapy tana buqatar counselling akan mikin da nasir yayi mata.......yanzun kuma tana shirin sake fadawa wani abun na daban?,kanta da zuciyarta kuwa zasu iya dauka?,ya kamata ta ciyar da d'anta ta kowacce siga muradinta.....idan yaso in taga dama bayan ta mallakeshi ta yayyankashi ta cinye. Abu daya ta kasa jurewa ya kuma gaza barin zuciyarta huda,ta yaya zata ji muryarta?. Bata taba jin dauke wayoyin ya dameta ba irin yau,ta dinga jin kamar tayi hauka idan ta tuna ba wata sauran hanya da zata iya samun damar magana da huda. Sosai tayi qoqarin ganin amna bata gane komai akan fuskarta ba. Ta kama mata aikin sukaci gaba dayi,tana ci gaba da mata hira tana bata labarin fu'ad. Kwata kwata bata jinta ma ballantana ta fahimci abinda amna din ke fada,a haka suka kammala amna ta fito tabar mata kitchen din. Sosai ta zazzaga dukkan abinda ya kamata ta sake juya abinci ya koma ainihin launinsa. Ta tsaya kaman ko yaushe ta zubawa abincin idanu zuciyarta na wani yamutsawa,mafi rinjaye na zuciyarta tana jin kamar wani yanayi mara dadi,wani yanayi da yafi kama da rashin jin dadi?,rashin kyautatawa?,ko aikata abinda ba daidai ba?. Itama bata sani ba,bata taba zaton da hannunta zata iya ciyar da kowanne dan adam abinda bai kamata yacishi ba......saidai abu daya ta sani shine....itadin guba ce ga duk wanda yace zai kawowa innocent rayukan nan guda uku farmaki. Takun da taji dake alamta mata an shigo kitchen din shine abinda yayi bala'in razanata. Da sauri a kuma birkice ta daga kanta tana duban me shigowar. Zuwaira ce fuskarta da murmushi ta qaraso cikin girmamawa. "Afuwa,dama cewa nayi bari nazo naji ko akwai aikin da za'a kama miki?" Tayi maganar tana duban warmers din da a gaban idanunta tana labe sabreen din ta cika aikinta tsaf. Idanunta ta lumshe tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,sannan ta tattaro dukka qarfinta ta bude idonta akan zuwairan "Wannan shine kuskurenku na farko,bana buqatar ki sake shiga wani guri a cikin gidan nan ba tare da kin tsaya kin nemi izini ba an kuma baki" Kai ta rusunar "Ayi haquri bazai sake faruwa ba in sha Allahu" Bata iya amsa mata ba,sai kawai warmers din data mata nuni dasu "Ki kaisu kan dining" Tayi maganar tana dosar qofar fita a kitchen din,don sam bata da qwarin tsaiwa ci gaba da magana. Tana sanya qafafunta da zummar fita tana sako tata qafar abinda ya sanya suka kusa karo da juna,yatsun qafarta suna caki na sabreen haka gwiwarta saita tsaya cak bata ja baya ba bata kuma koma ba. Tsaiwa cak itama sabreen din tayi tana danjin qafarta na dan radadin kadan saboda qafafunta akwai alamun tana ajiye farce. Shirun da sabreen din taji ya sanyata daga kanta ta sauke dubanta akan laila. Tana tsaye cak ba alamun zata kauce mata ta bata hanya. Bisa dukkan alamunta tana jiran sabreen ne ta kauce mata,kota koma sai ita ta wuce. Cikin qasa da second biyu sabreen din taji wani abu ya saukar mata,wani abu me kama da izza da jin mallaka ya mamayeta. Ta lumshe idanunta sannan ta zubesu fes akan laila tana duban tsakiyar qwayar idanunta da wani irin kallo dake qure qarfin halin mutum. Da farko itama laila din ta zuba mata idanu,saidai a hankali wani kakkaifan abu ke ranqwafar da nata idanun. A hankali taji ta gaza jurewa,saita dauke dubanta daga kan sabreen din tana ja da baya,ba tare data sake dubanta ba ta rabata ta wuce a tsanake ba tare data sake duban sashen da take a tsaye ba. Da idanu tabi sabreen din har ta wuce,ta maido dubanta cikin kitchen din tana jin kamar yau karon farko ta tozarta......a karon farko taji wata 'ya mace tayi mata kwarjini,har kuma ta juyata ba tare data furta kowacce kalma daga bakinta ba. Hada ido sukayi da zuwaira,sai zuwairan ta tabe baki tana dauke kai. Cike take dama da lailan,cike kuma take da yadda maamah ta dinga jaddada mata ta girmama lailan,don gidan fu'ad a wajen lailan tamkar gidan mahaifinta yake,tammar kuma gidan yayanta da suke uwa daya uba daya yake. "Idan me guri yazo dai me tabarma nadeta yakeyi,nan din dai akwai macen data amsa sunan matar gidan,komai ayishi bisa takatsantsan". Sarai ta fahimci abinda zuwairan ke nufi,amma sai taga sam bata da lokacinta,don abinda sabreen tayi yafi tsaye mata a rai,yadda zaiyi handling nata. Da gaske komai na gidan yayi mata,da gaske zuwa yanzu tanaso ace itace mamallakiyar gidan. Ta cika gidan da izzarta da mulkinta da kuma ikonta kwatankwacin hajja,tako ina ta zama ME MULKIN gidan. Samun amna tayi tana shirin tafiya. "Har me?" Ta fada cikin nuna kulawa. Murmushi ta saki "Driverna na aje adda tun dazun fa,daga cewa anni zanzo na miki sannu da zuwa". Fararen idanunta da a yau take jinsu wani iri ta kada,bata da energy din dogon magana. Closet dinta ta bude kawai tayita fiddo abinda take ganin ya kamata ta bawa amna. Ta hada abubuwa cikin qaramar jaka me kyau da daukan hankali. Ido amna ta fiddo tana nuna tsananin murna da mamaki "Duka adda?" Ta fada da murmushi. Abun ya burge sabreen sosai,yadda amna din ta nuna,duk kuwa da cewa tasan tafi qarfin duka abinda zata bata din. Fitowar zuwaira da laila daga kitchen din ya danja hankalin amna dake qoqarin ficewa,ta bisu da kallo kawai kafin ta juya a hankali ta fara takawa tana fita daga falon. "Sai haquri ranki ya dade....laila kenan..... D'iyar hajja harira.....hajja harira 'yar majalissar zartarwa hajiya mariya maamah". A badini kyakkyawan masauki maganar zuwaira ta samu,hajja hariran da sukayi tattaki har cikin gidansu suka kai qudurin aurota don su cimma buqatarsu?,ta yaya zata manta wadannan fuskokin,ranar,dama abinda ya faru a ranar....har maamah din tana da qarfin halin ajiye budurwa irin wannan a gidan d'an data haifa?,wanne irin kwado ne wannan?,budurwar da babu wata alaqa tsakaninsu face ta zallar qawancen dake tsakaninsu?,a tsarin abota da mu'amala da zata fishshi dan adam tasu bata kan ko guda daya. Kai ta jinjina,information din ya mata kyau da ma'ana,amma kuma batajin zata sakewa zuwaira ko ta nuna jin dadin hakan. "Ya kamata ki dinga tsaiwa a iyakokinki kawai" Abinda tace da ita kenan tana takawa zuwa hallway dinta don komawa dakinta,duk da har yanzu ba wani cikakkiyar nutsuwa ko sukunin data samu daga uban tunanin dake addabarta,gefe guda kuma tana cike da fata da fargabar sanya abincin a bakinsa ya zarce zuwa cikinsa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _ZAFAFABIYAR_ _Daga nana Aisha R.A tace:manzon Allah S A W yace:Duk matar da tayi aure ba tare da izinin waliyyinta ba,to aurenta batacce ne,idan mijin ya tare da ita taci sadakinta saboda halastar farjinta a gareshi_ 33
Chapter 33 · 0% Book details