← Book details A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 60

Sashe 2

A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse ta daga kai tana kallon hajjan "Na tsani matsala ko akasi hajja......musamman a wannan matsayin da nake kai a yanzu......me zanyi da ita ballantana na buqaci sharhi a kanta?,bana buqatar dukkan wani jawabi da zai alamta min FADUWA ko MATSALA akan cikar burina a yanzu.......inaji a jikina da raina cewa......zan iya kauda kowacce matsala da zata tunkaro muddin na samu nasarar tsallake wannan matakin da muke kai a yanzu......da qwanjina....da kuma fikirata". Jinjina kai kawai hajja keyi.......tanason taji wanne tanadi da tsari tayi akan hakan?,amma kuma bataso ta zafafa tambaya akai har maamah ta zargi wani abun,saita tattarewa ranta komai tana jiran lokaci.....domin kuwa ta san cewa qwace goruba a hannun kuturu ba abu bane me wahala ba. ********Abune sananne a wajen kowa......sharar biki da yawan maganarsa a bakunan mutanen mu ya ta'allaqa da suna da sharar iyali dangi ko zuri'ar da za'a gudanar da bikin diyoyinsu. Hakan itace ta kasance akan MUHAMMAD FU'AD JADDA mamallakin JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES. Daga qishin qishin zuwa samun tabbacin tasowar maganar aurensa,wanda tabbacin ya samu ne daga yadda farouq musaddiq saddiq da uban family alhaji hamza kibiya sukewa bikin shiri na gasken gaske. Daga abokansu saddiq maganan ya fara yaduwa,kafin kace meye wannan labarin ya fara kewaye kowacce kafar sada zumunta. Duk da a qurataccen lokaci labarin ya fasu.....to amma labari ne me dumin gaske daya bawa mutane da dama mamaki.......ya girgiza zukata da zuciyoyin 'yammata da dama......musamman yaran masu kudin da suke kwana su tashi da mutuwar sonshi......suke kuma da qaqqarfan hope din samun shiga a wajensa kodon matsayi da mahaifansu ke dashi......walau na dukiya ko na siyasa......ko kuma kasancewarsu abokan kasuwancin gold da diamond dinsa. A gefe guda kuma wajen 'yammatan da suka hada duk wata sura kyau da isa.....wadanda sukasan basu da wani tsanin isa zuwa gareshi......saidai sunyi mutuwar murus akan mayatacciyar soyayyarsa......abun ya sake bude musu topic of discussion......qarqashin kowanne posting na labarin bikin dake dauke da qawataccen IV na bikinsa da aka qawata da zallar ruwan gold,yake kuma wani irin sheqi da daukan idanun da zai gaya maka bikin ba na yaro bane......tarin cincirindon comments ne da mabanbantan kalamai masu yawan gaske. Da yawansu suna fatan inama zasu samu hotunan amaryar?,ina free wedding pics da sauransu,saidai ko daya basu samu ba face kunji kunji da shaidar zur daga wasu daga cikin commentators na qarya,sai luguden labba da tsabar kyan IV din bikin da aka kashesu dashi.......sai videos na lefen da aka samu wadda ta qwarewa gulma da munafurci ta ba bajesu dashi......abinda ya sake hura wutar tattaunawar. Sam wadanda ake abin dominsu basusan anayi bama......daga angon har amaryar ba ma'abota social media bane........idan kaga ta qulla abota da waya to akwai sabon mission a gabanta........data gama ta ajiye wayar dama layukan da tayi aikin dasu,wani ta karya ta zubar.......wani kuma sai bayan wani zamanin.......yayin da oga fu'ad sam sam ayyukansa basa ma bashi damar tunawa da wani media......koda WhatsApp dinsa idan ka ganshi akai wani abune ya kama da lallai yake da buqatar hawa yayi a can din. Koda yana free ma ko yana annual leave dinsa.......yanayin tsaro da dukka rayuwarsa ke buqata ya sanya ya sake nesa nesa da duk wani harkoki irin wadannan......don komai nasa a matakin rayuwar daya taka yanzu yana buqatar privacy. A daren da ya rage ayyuka sosai......abu daya tak ya rage masa ya kammala yabar qasar. Yana zaune saman bean bag chair,daga gefansa ruwan wolfberry ne me dumi yake sipping yana kuma chewing berries din idan sun shigo bakinsa. Haka kawai yayi shaawar shiga yaga me duniya ke ciki don duka schedule dinsa na yau ya kammalasu. Da wani personal account yake amfani,wanda bai taba ba baya kuma wallafa komai a ciki bare ka iya gano waye mamallakinsa. Akwai account na company dinsa kala daban daban dake qarqashin kulawar ma'aikatansu dake kula da wannan fannin,so amma ko su baya bi ta kansu tunda yayi imanin zasuyi handling dinsa ya dace da abubuwan da ya kamata ace an sanya din. "Ya salam" Ya fada yana miqewa daga relaxing din da yayi cikin bean bag din yana kallon yadda hotunan katinan daurin auren ke shawagi cikin media. Da farko ma bai fahimta ba,saidai daga bisani da suka yita jeho masa ire iren posting din.....kamar sunayi da gayya sunsan shike da alhakin abun har sai da hankalinsa yakai. Shuru yayi yana sauka gami da furzar da iska daga bakinsa. Yasan aikin mutum uku ne wannan farouq saddiq da musaddiq,sai amna ta hudunsu. Kamar jira akeyi ya gani kira ya shigo masa,a nutse ya jawo yana dubawa......farouq ne,kusan tun randa yace ya zaba kaya bai sake barin wayarsa yadda za'a sameshi ba sai yau,sai ya katse kiran,ya koma ya laluboshi video call. Ta signal ya shiga,amintaccen app din da mafi yawan manyan mutane ke ta'ammali dashi saboda samun cikakken tsaro. Shigan farko ya daga,fuskarsa ta fito tarwai kaman yana gabansa. "Hey...." Ya fada qasa qasa yana duban fu'ad "Don't tell me baka ma taso ba?" Yayi masa tambayar yana tsuke fuska tare da bata fara'ar fuskarsa "Zuwa ina kuma dude?.....bakaga abinda kuka jawo ba?,baka ga abinda ke trending ba?" Ya masa tambayar shima hana dan bata fuska kadan. Kai farouq ya jujjuya hagu da dama yana yarfar da hannu "Am asking you seriously fa.....where are you?" "Ask media users......farouq,you take it very serious fa.....wannan fa auren ba wani abu bane da za'a damu dashi har haka ba.....ba wani babban abu bane da zai zama ya yada ko ina ba......it's just a temporary......." "Kai kasan wannan......mu bamu sanshi ba......in fact ma idan ka matsa da yawa zan fiddo komai.....just ka dauko hanya gobe kawai......if not,bazan gaya maka abinda zai faru ba". Datse kiran farouq din yayi,abinda ya sanya fu'ad sakin murmushi ba tare daya motsa daga inda yake ba. Da alama farouq din a qufule yake dashi sosai,shi yasa yayi masa abinda yafi tsana kashe masa kira. Ya kasa fahimtarsa ne,shi sam baiga me yasa zai damu da abinda baida wani muhimmanci ba,baiga abun daurawa kai hidima har haka ba......already sun gama diban kudin komai da komai uban da 'yar,daurin aure kuwa ko aike yayi cikin ma'aikatansa za'a daurashi,gidan da zai ajeta ko ba yanzun ba zai iya bada umarnin tarewarta idan ya gama sabgogin gabanshi,for god sake zai bata lokacinsa ne da ranshi akai?. Bai sake bi takan farouq ba don yasan fushinsu da juna ba wani abu bane me dorewa ba. Saidai yadda farouq din yace idan bai dawo ba washegari baisan me zaya faru ba,yana tsaka da ayyukansa da yake sanya ran sune na qarshe kiran anni ya sameshi. Abdul_haleem daya daya cikin guard dinsa ya miqawa folder din hannunsa,ya koma gefan table din da yake ajiyar takardun ya zauna yana daga wayar. Cikin nutsuwar nan tata da ko yaushe take qara mata kima da kwarjini tayi masa sallama cikin tsantsar kulawa da qauna irin ta uwa da d'a. Kaman ko yaushe shima,cikin tausasawa da matuqar bada kima ya amsa mata sallamar. "Barka da warhaka anni......anni ayyuka sun sani gaba,ayimin afuwa" Yayi riga malam masallaci wajen fada. Murmushi ta saki cikin nutsuwa tace "Anyi maka Muhammadu........ya aikin?,fatan komai yana tafiya daidai?" "Alhamdulillah anni.....komai alhamdulillah,saidai muna buqatar qarin addu'a" Ya furta maganar jerin saqonnin daya gani shekaran jiya suna fado masa. Ba'a raina kaidin maqiyi,kuma abokin adawa ko wanda bai sonka ba'a rainashi komai qanqantarsa. "Kullum a cikinta muke,ba abinda zai faru in sha Allah sai alkhairi......amma nayi zaton samun baquncinka a yau......tuntuni mun sauka a sabon gida.....duka duka jibi ne daurin auren nan......ga baqi a gidan kowa kai yake tambaya". Hannu ya sanya ya shafi sumarsa,har yanzu ya gaza gano abinda yasa suka daukaki sabgar nan haka.....har wani taron gayyar jama'a anni itama tayi kenan bayan ta maamah?. "Jibi din zan shigo in sha Allah anni" "Anni jibi yayi kusa.....gobe ko yau ya kamata....private jet ne,baida buqatar samun wani issue ko ya kawo excuse" Ya jiyo muryar farouq daga gefe tana shigo masa. Murmushi ya saki da sautinsa ya gaza boyuwa,wato zuwa yayi ya hadashi da anni kenan?. "Bani shi anni please" Ya fada da sauri,bata ce komai ba ta miqawa farouq wayar tana murmushi. Drama din fu'ad da farouq babu me shiga,idanma kace zaka shiga din kunya zakaji. "Definitely idan ka samu dama saika shiga tsakanina da anni......ka canza hali wallahi" Ya fada yana dan daure murya. "Kome zaka fada ka fada.....ina nan ina jiranka" "Kaci gaba da jira.....at last idan bakayi wasa ba kai zan daurawa auren nan da yarinyar......tunda naga ka damu da lamarin ta da yawa" Daga haka ya katse kiran yana dariya ciki ciki. Yasan ya kunno farouq din,don ba wanda zai rabashi da fannah dinsa sai Allah. Haka kawai ya samu kansa dason cika alqawarin daya yiwa anni,ya maida hankalinsa qwarai kan qoqarin kammala abubuwan da suke gabansa don ya samu isa nigeria kaman yadda ya alqawarta. Hannu anni ta miqa tana karbar wayarta daga wajen farouq dake mita. Duk da mitar da yakeyi din saidai ya kiyaye dukkan wani abu da zai saka anni ta fahimci akwai lauje cikin nadi.....boyayyen manufa da qudurin data hana fu'ad damuwa da dukkan wani lamari daya shafi auren. "Anni kina sauqaqa masa da yawa........hatta da friends dinmu gobe zasu iso.....amma ace shi yana can neman kudi?.....har yau ya kasa sanin kalmar hutu a rayuwarsa?.....ta yaya zai kula da diyar mutane?" Murmushi anni ta sake,yadda farouq din keta mita ke bata dariya "Banda abinka farouq.....na tabbatar ya fika damuwan ya iso fa.....sannan tunda kaga haka din ba yadda zai taho dinne,da yau gobe da jibin dukka na Allah ne,kuma kaman yau ne.......ina da saqo ma da nakeson ka miqawa d'iyata...." Anni ta fada tana yunqurawa ta miqe. "Ina amna ta shiga ne?" Farouq ya tambayi anni dake qoqarin bude wani side na wata qawatacciyar cupboard ta daban dake cikin aljannar duniyar bedroom din nata. "Tana bangaren beauty spa" 08187255862 "Okay" Ya fadi kawai a taqaice,don ita kanta yadda yaga alamun ta dauki bikin kamar yafi yadda kowa a gidan ya dauka. ******A duk bugawar daqiqa,wucewar kowacce saa da kuma bugawar agogo sake kusantar da ita kawai yakeyi zuwa ga duniyar mamakin abinda ke shirin faruwa da ita. Sannu sannu taga gidan ya fara cika da baqin fuskokin da da yawansu ta manta da kasancewarsu ahalinta. Wasunsu tun ana taron alhinin rasa
Chapter 2 · 0% Book details