← Book details A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 60

Sashe 32

A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta shiga,ta kuma maida key din ta rufe tana jin kamar zai sake biyota ne. Wani azababben kuka ta saki tana jin yadda labbanta ke wani irin zugi kamar zasu cire daga saman bakin nata. Tako ta ina tun daga saman labban nata har zuwa fuskarta dama qirjinta ba abinda suke fitarwa sai wannan mayataccen qamshin nasa. Ta jima tana kuka gami da murza lips din,tana fatan zugin da takeji ya ragu.....har batasan iya adadin lokutan data shafe a haka ba. Qarar agogon dakin ya sanyata maida idanunta da sukayi mata nauyi saman agogon,lokaci yaja.....saita miqe da dan hanzari ta zauna. Kaman yadda jikinta bai daina rawa ba haka zuciyarta da labbanta basu daina mata zafi ba. Duka hannuwanta ta saka ta rufe fuskarta dashi tana ci gaba da sauraren bugun zuciyarta. "Ba lokacin wannan bane sabreen.....ba lokacin bata lokaci bane wannan,kina sake bawa maamah damar kasancewa da 'yan uwanki ne kawai a kowacce daqiqa....lokacin aiki ne tuquru yanzu don qwatar kai.....ki daina bari normal halittan namiji kamar saura yana firgitaki......wanne iri ne baki gani ba?" Taji ana gaya mata daga can wani sashe na zuciyarta. Abinda ya zaburar da ita kenan ta fara zame kayan baccin jikinta ta daura towel ta wuce bandaki. Wanka tayi ta dawo ta shirya cikin atamfa doguwar riga,ta gyara ta matseshi cikin hair tie masu wani irin adon stones masu garai garai a jikinsu dan madaidaita. Bata saka komai a fuskarta ba,amma tayi wani irin kyau duk da ramar da tayi,saidai kuma fatarta tayi fresh saboda zama waje daya da rashin bawa rana damar qona fatarta,uwa uba har yanzu mayataccen gyaran jikin nan yana nan baibar jikinta ba,batasan wanne irin rantsatsen hadi bane annin ta biya kudi akayi mata. Duk da yunwar dake qwaqular cikinta amma sai taji sam ba zata iya zama ba,hasalima duka tasirin yunwar ya gushe,kitchen take da muradin shiga ta shirya abincin dare,wanda take fatan koda batayi na rana ba aqalla a samu na dare. Da dan hanzarinta take fitowa daga hallway din,hankalinta yayi gaba zuwa kitchen sautin muryarta ya dakatar da ita "Adda sabreen" Amna da shigowarta kenan ta fadi fuskarta cike da murmushi. Suna hada idanu ta sakar mata fuska da salon nata murmushin. Haka kawai tana tuna mata da huda duk da hudan miskila ce ba kaman amna ba,amma sai take mata yanayi da hudan. "Yaushe kika shigo?,afwan ban sani ba ina ciki ina wanka" Ta fada tana neman gefan wata kujerar daban ta zauna. Da murmushinta tace "Adda sai an miki uzuri,matafiyi ba'a rasashi da gajiya a jikinsa,ni har zan kunna wayata ma na duba wani assignment kafin ku samu fitowa" Kyawawan fararen idanunta sabreen ta fiddo waje. "Haba dai,ya zaki zauna kiyita jira,da kin qarasa kinmin magana ai". Bakinta ta rufe da tafin hannunta "Kinaso hamma ya ballan qafa?,ba'a shiga shiyyar dakinsa direct ai,BB farouq ne kawai ya isa". Tabe baki tayi a fakaice,can qasan ranta tana fahimtar tsananin izza gareshi da shegen mulki. Fara sako mata zancansa da tayi yasa sabreen miqewa cikin qarfin hali da son nuna komai lafiya "Bari na baki ruwa kisha" "Am full adda.....saidai na rakaki kitchen naga kaman kitchen zaki shiga" Kafada ta daga da murmushi "Alright.....muje" "Yau hamma za'ayi full da abincin addana.....yadda yakeson abinci me dadi na tabbatar adda na ba daga baya ba.....in fact ma tunda har kikayi nasarar samun hamma na na tabbatar komai kin hada" Tayi maganar da dariya dariyar tsokana. Bata ce mata komai ba,tadai qoqarta sauke mata murmushi kawai. Sanda suka shiga kitchen din duk sai taji ta takura,ta rasa ta inda zata fara,saboda idan maganar qwarewa ake ta fannin girki tasan bata cikin jerin wadannan matan,infact ma ita ba gwanar shiga kitchen bace sam.....to ina ma taga time?,tana ta abinda qannenta zasuci susha su lulluba sutura,suyi magani idan lalura ta taso?. Tasan huda ta tsere mata sosai ta fagen iya girki,don tun tana fita tana barinsu hudan tana musu tsumburin burin har tazo ta qware. "Kaman ya kamata kiyi surprising hamma na ko?" Amna ta fadi da murmushi tana duban sabreen. Kallonta kawai tayi kallon dake nuna alaman tambaya,sai amnan ta daga kafada "Gift dina na yau zan gaya miki best food nashi da daddare.....but nima zaki bani tukuici ki gayamin sirrin skin dinki adda don Allah?" Ta qarasa fada a shagwabe. Abun dariya yaso bawa sabreen saidai batayi ba illa murmushi data saki,ta kalli fatar tata ta kalli amna,ita bataga wani kyau da fatarta tafi ta amna ba "Seriously adda kina burgeni at the first time dana fara ganinki.....kawai naji jinina ya hadu da naki" Ta fadi da gasken ta yadda a furucinta zaka fahimci da gasken take. Kusan tana zaune amna ta hada duka ingredients din na kalar abincin. Ta miqe tana daura apron data gani tana bawa amna daya,sai qararrawar dake kitchen din ta dauki tsuwwa. Amna ce ta duba,saita waiwayo ta kalleta "Kira ne daga bakin gate" Tayi maganar tana miqa mata wayar "Ki daga" Tace da ita,ba musu ta saka a kunne,bayan wasu sakanni ta dawo da dubanta kan sabreen "Wai baqi ne dake.....zuwaira daga wajen hajiya mariya maamah". Maganar taji ta bugu qirjinta don tazo mata kamar a bazata,sam ta mance da issue dinsu,sai ta fara zare apron din tana cewa "Kice a barsu su shigo" Yadda ta fada mata haka ta gaya musu,ta zare apron din ta ajiyeta ta soma dosar kitchen din tana cewa "Ina zuwa amna" "Ba damuwa adda" Ta amsata tana matsawa kitchen din don ci gaba da aikin. Kasa tsaiwa tayi daga cikin parlor din,ta taka har qofar qarshe wadda daga ita sai balcony din da zaka sauka zuwa farfajiyar gidan. Tsaye tayi kawai riqe da qofar,ba abinda ya hanata hango wajen sai lafiyayyen curtain din daya raba tsakaninsu. "Assalamu alaikum" Muryar zuwaira ta fara rasa falon kafin ta bayyana Laila na biye da ita a baya da luggage dinta dake da girma,tana takawa d'ai d'ai,tana sake ganin alatun da aka xubawa gidan,sai take ganin wancan zuwa bataga komai bama. "Wa'alaikumussalam" Ta amsa mata idanunsu yana haduwa waje daya dana laila. Wata faduwar gaba ta saukarwa lailan lokacin da idanunta ya shiga cikin na sabreen dake tsaye tana jiran shigowarsu "Kambu.....who's she?" Ta samu kanta da furtawa a qasan zuciyarta saidai kuma labbanta a sarari ma rawa sukeyi. Yanayin kallon da lailan ke mata sam baiyi mata ba,a nutse da wani irin jan aji ta debe kallonta daga kan lailan tana maidawa kan zuwaira dake qoqarin gaidata "Basai kin tsuguna ba......ta nan ga qofa nan a nan din akwai dakuna a ciki,ku zabi duk wanda yayi muku" Ta amsata a taqaice don ko tsaiwarsu a wajen sai taji bata qauna. Tasan da qofar ne cikin ranakun zaman kadaicin data dinga yi cikin gidan *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _ZAFAFABIYAR_ _Daga abdullahi dan umar R.A yace."manzan Allah S A W ya hana auren shigaari,shi kuwa auren shigaari shine,mutum ya aurar da d'iyarsa ga wani,bisa sharadin Shima wancan zai aura masa tasa 'yar,kuma babu biyan sadaki a tsakaninsu(musanye kenan)_ _bukhari da muslim ne suka rawaito_ ___________________________ Tasan qofar ne cikin ranakun zaman kadaicin data dingayi cikin gidan da kuma Yanayin wajen kuma tasan guri ne baqi na kusa bayan boys quaters da gidan ya mallaka na musamman da yake daga can bayan gidan. Bata da matsala dasu,koda dakunan hallway suka zaba kuwa,don kowacce rana a lissafe kwanakinta cikin gidan suke. "To.....to madallah......bari mu qarasa" Xuwaira ta fada tana wucewa gaba laila tana biye da ita. Duk wani taku daya biyu na lailan saisun hada idanu da sabreen din wadda ke tsaye yana karantar yanayin kowanne a cikinsu. Dauke dubanta tayi,sai ta koma saman kujerar falon ta zauna kawai yanayin jikinta yana neman sauyawa. "Assalamu alaikum" Muryar zuwaira ta sake ratso falon. Idanunta ta daga a hankali tana duban zuwaira sanda take takowa falon riqe da waya a hannunta fuskarta a sake "Ranki ya dade.....hajiya nason ganawa dake" Tayi maganar tana miqa mata wani qaramin akwati da sabreen din ta kasa amsa sai binsa da kallo da tayi. Daya hannun waya daya akwati,kuma dukkaninsu idanun zuwaira suna gaya mata ana da buqatar karbar kowanne. Cikin kwanyarta taji ana umartarta data karba,ba wani laka a jikinta ta karba dukkaninsu "Sirri yana da matuqar muhimmanci......hajiya nason sirri matuqa" Ta tsinci muryar zuwaira tana gaya mata. Idanu ta waiwayowa ta zubawa zuwairan,sai kawai ta dauke kanta tana nufar hanyar hallway don komawa dakinta. Kaman ana jira ta shiga dakin wayar tahau kadawa,ta zubawa sunan da zuwaira tayi saving dashi wato hajjaju. Tattaro dukka wata dauriya tata tayi,ta hadiye wani yawu me kauri sannan ta daga kiran ta sakashi a hands free hana ajiye wayar saman cinyoyinta. "Ka kula da ita.....huda kuje ya baki magani kisha kafin ki kwanta.....sannu qawata". Abinda kunnuwanta suka fara jiye mata kenan wanda ya sanya tsigogin jikinta tashi. Ta runtse idanunta tanajin kamar an daukk guduma an kwada mata saman kanta. "Huda kuma?" Ta motsa labbanta tana furtawa a wahalce. Murmushin maama ne ya soma riskarta kafin tace "Eh,huda.....ko bazatayi lalura ba?......kowanne sakaci da zakiyi akwai sakamakonsa kan halittar da kika fi so fiye da komai da kuma kowa......" "Bani huda din" Ta fada kanta tsaye da wani irin yanayi me kaushi. Wata qaramar murmushi me kama da dariya ta saki "Da wuri haka?,zabin cetonsu ai yana hannunki tunda na gabatar miki da dukka kayan aiki.......bansan me yasa kika yanke sadarwar dake tsakaninmu ba.....saidai koma meye wannan ba damuwa ta bace......kowanne ganganci kuskure ko sakaci sakamakonsa rubutacce ne a nan......" "Idan kikayi kuskuren cutar da ko farcen daya daga cikinsu ne......to lallai ba shakka ba mallaka miki danki zanyi ba......zan sadar dashi da kabarinsa ne,zan mallakaws barzahu shi a madadin ki" Sabreen ta fada cikin tsawa da wani irin birkitaccen sauti daya ratsa maamah,taji kuma har cikin jikinta da gaske ta fadi maganar. Ta danyi jim kadan tana jin wata shakka tana ratsa ta,sai kuma ta saki wata dariya "Bismillah mana......indai har kina ganin hallaka mutum kamar muhammad jadda abune me sauqi....." "Akwai abinda yafimin wannan sauqi?.....aikinki ya ninka shi wahala sau dubunnan da bazasu qirgu ba.......idan naso a safiyar gobe za'a wayi gari da sanarwar jana'izarsa hajiya maamah.......saboda haka ki kula......akwai kadarata a hannunki......a nan kuma akwai ruhinki dama kadararki gaba daya a tare dani"
Chapter 32 · 0% Book details