Sashe 4
A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ta sakashi a kunnenta "Kicemin kun dawo titi don Allah,kicemin ayshatu ta warke" "Na warke adda......na samu sauqi" Muryar yarinyar ya saukar mata a kunne. Wani hawaye me sanyi ne ya kubce mata,kullum da lamarin yarinyar take kwana take kuma tashi,daga yadda taji muryarta tasan cewa tabbas lafiya cikakkiya ta samu a gareta "Muna cikin sabon gidanmu yanzu aunty.....na gayawa titi bazan yarda na fara ganin kowa ba sai ke". "Yanzu kuwa zaki ganni ayshatu" Ta bata amsa kai tsaye kaman ta manta a wanne yanayi ita din take.....kaman ta manta rabonta da taka qasar waje wasu kwanaki ne masu yawa. Da wani irin excitement ta ajiye wayar,ta zura qafafunta qasan gadon da hanzari zara miqe da nufin shiryawa,sai kuma ta dakata cak saboda dawowa hayyacinta da tayi. Tayi imanin wadannan mutum mutumin har yanzu suna tsaye a qofar gidansu suna gadinta,yawan mutanen dake kai kawo a gidan bai sanyasu sun tafi ba......don ko dazu ita iya jiyo baqin tsagin abbansu suna tambaya a kansu. "Saina fita kota halin qaqa wannan karon......ko meye zai faru saidai ya faru" Ta fadi tana qarasa saukowa,ta kuma fito kai tsaye zuwa ga falon tana nufar doguwar veranda din dake saman wanda tacan zata samu hanyar gangarawa qasa ta koma ainihin dakinsu. _DUNIYA TA na kudi ne_ 08187255862 Page 06 Batasan gidan ya fara daukan mutane ba sam sai data sauko din. Gomayyar idanuwa sukayi kanta caaa ana qare mata kallo. Kowa da nashi tunanin cikin ranshi,wasu na kallon tsantsra kyan data qara saboda gyaran jiki na musamman data samu tsahon kwanaki daga wajen qaararriyar me gyaran jiki......wasu kuma na mata kallon sha'awa suna fadin inama su ko 'ya'yansu keda wannan sa'ar ta auren irin mijinta?,yayin da wasu nasu kallon na bin qwaqwafi ne hassada da tarin tambayoyin ta yaya KARUWAR GIDA.....WADDA TA GAMA RABA MUTUNCINTA WA MAZAN TITI TA SAMU BABBAN MUTUM.IRIN MUHAMMAD JADDA DIN?. Miskilanci da shariya kusan cikin jininta suke,don haka tayi kaman bata gansu ba ta wuce dakinsu kai tsaye.....ballantana kusan dukansu tana cike dasu. Ba wanda yabi takan rayuwarsu.....qaqa suka kwanta qaqa zasu tashi?,amma sai gasu yanzu zube da sunan sunzo auren yarinyar da basusan yaya ta girma ba?,me taci har takai wadannan shekarun?. A gaggauce ta shirya cikin wata luxury Egyptian abaya datayi masifar karbarta,wadda inda cikin nutsuwarta da hayyacinta take itama ya kamata ace taga yadda rigar ta karbeta. Tun daga nesa kana iya ganin mugun kyan da fatarta tayi,wani irin haske da glowing kawai takeyi,saika rantse da Allah diyar wani hamshaqin ce. Qaramar handbag kawai ta dauka ta jefa wayarta a ciki da dan canjin da zata riqa saboda mota,ta fito daga dakin a nutse tana isowa falon,daidai sannan momma bahijja ta shigo rungume da dinkakkun atamfofin da tasa aka dinkawa su haneefa duk da tarin suturunsu. "Ina zuwa kuma?" Momma din ta jefa mata tambayar tana kallon yadda take komai a gaggauce. Batasan da wanne harshe zata yiwa momma bayanin aysha da muhimmancinta a wajen ta,don haka a taqaice tace "Dubiya zani momma...." "Zuwa ina?.....kuma dubiya a irin wannan lokacin?" Kai ta langabe kadan tana fargabar kada momma din ta hanata fita,don a irin wannan lokacin ita kadai takejin zata hanata fitar ta hanu "Ba niss momma.....ba jimawa zanyi ba". "Nadra ta rakaki,kuma kada ki wuce awa daya" Ta fada tana qarasawa tana zube dinkunan hannun nata saman kujera. Mayafi kawai ta figowa nadra,ta sanya wasu plate shoe nata sannan suka fito. Sam bata damu da yadda idanuwa keci gaba da binta da kallo ba,har wasu na qoqarin gaisawa da ita,a haka ta doshi qofar gidan nasu tana tsara yadda zata kaya tsakaninta da qedarun da aka tsaida a qofar gidan. Tana takawa zuwa qofan tana jin fargabar yau dame zasu zo mata?,don dai yadda takeji a ranta yau koda sama da qasa zasu hade sai ta fita.......don ba wani mahaluqi daya taba saka mata dokar zama cikin gida har haka tsahon rayuwarta......sai yau gashi sama ta ka wani mutum can da baisan ciwonta ko darajarta ba......yanason yayi amfani da giyar kudi ya yiwa rayuwar karan tsaye. Tana tura qofar yana riqeta kana aka qarasa budeta. Fuskar kakkauran mutumin ta bayyana har abun yana bawa sabreen mamaki. Bata taba kawowa a lokacin irin wannan zata sameshi tsaye bakin qofar ba kamar wanda aka tsaiguntawa zata fita......waisu basa zama?,ko basa hutawa da jiddin suna tsaye suna gadin duk wani motsinta. "Good evening madam" Abdulgaffar ya furta cikin matuqar girmamawar nan da suka saba mata magana da ita saidai kuma a dabarance yana matse kowacce hanya da zata iya rabawa ta fice daga gidan. Ta gama karantar motsinsa kaf.......bata wani damu da gaisuwarsa ba ta azawa fuskarta wani irin halakakken bacin rai da kuma d'aurewa "Kiramin boss dinku" Ta bashi umarni nakai tsaye da wani irin sauti da babu wasa ko kadan a ciki. Tanaso ta gwada musu girman abinda zata iya aikatawa.......tanaso ta gwada musu basu ba......koda boss dinsu ma bata daukeshi da wani tarin muhimmanci ba. "Bani da connection dashi......idan zan kirashi saina jira anyimin iso kafin na samu magana dashi......amma ga jordan zai kira miki shi" Abdulgaffar yayi mata bayanin cikin girmamawa yana matsawa da baya. Can qasan ranta mamaki yake kamata,wanne irin girman mulki da izzar kudi gareshi da har yaransa ma ba kowa da kowa keda daman magana kai tsaye dashi ba "Good evening madam.......kiyi haquri ki jira kadan,yanzu in sha Allah zai amsa" Jordan ya fada yana rusuna mata. A ranta tanaso ta gaya musu ne a fili "Qattin banza.....kun zauna kuna yiwa mutum qwaya daya bauta saboda yana da dukiya" Abinda zataso gaya musu kenan ganin yadda jordan ke lalubar muhammad fuad jadda cikin girmamawa. A lokacin yana tsaka da hada duk wasu muhimman abubuwa nashi da kanshi,ba tare da ya bari hidiminsa ya masa ba wato me sunan malam. Akwai wasu abubuwan da da kanshi yake yinsu,duk da tarin hadiman dake gareshi. Yana sanye da fara qal din t.shirt me laushi Vshape neck,hannunta iya dantsensa wanda hakan ya sanya murdaddun damtsensa dake nuna girman daga qarfe da yakeyi suka bayyana,wandon jikinsa ma farinne duka duka tsahonsa iya qaurinsa,sai lausasan fararen flip-flops masu tsananin haske da taushi. Cikin kowanne irin yanayi tsarinsa na dabanne,kai tsaye zaka iya cewa gayu ya ratsa jikinsa da gasken gaske.....koda kuwa bacci zai shiga zaka sameshi neat....komai nashi kuma completed kai kace ba bacci zai kwanta ba. Yadda yake a nutse cikin wani irin tsari haka komai nashi yake kasancewa,waya.yake amsawa wadda ya sakata a hands free ya ajiye saman wani zagayayyen kujera me siffar qwallo dake a gefe. Kadan ya kalli wayar,sai ya fahimci kiran jordan keson shigowa amma yana buqatar izinin haka,don haka ya katse wancan kiran ya bawa kira jordan din dama "Barka da wannan lokaci sir" Jordan yayi maganar cikin girmamawan data bata ran sabreen,ta cika fal da mamakin wanne irin ban girma ne haka kaman yana a gabansa?,ya kasa miqewa da dukka tsahonsa ya amsa wayar. "Yauwa Jordan......ya akayi?" Ya tambayeshi kai tsaye. Sai daya dan daga idanu ya kalli sabreen din da idanunta ke cike tab da fushi,sannan qasa qasa yace "Madam daka tura a yiwa aiki ce keson magana dakai sir" "Madam?" Ya tambaya yanason tuna abun don ba komai yake baiwa muhimmanci ba "Eh sir....." "Bata wayar" Ya umarceshi kai tsaye don ya tuna inda zancan ya dosa. "Ka matsa a wajen idan ka bata" Ya sake fadiwa jordan don bayason yayi involving yaransa cikin abinda bai shafesu ba.....hakanan yana ganin ba girmansa bane su fahimci komai ba. Kaman ba zata karba wayar ba don tana jin kamar ta zuba a qasa data nema magana dashi......saidai kuma girma da martabar inda zataje din ya shafe komai a idanunta,don haka ta sanya nadra ta karbo wayar daga hannunsa sannan ta karba a hannun nadra din,ta taka a nutse tana dan komawa ciki duk da jordan ya matsa daga inda zai iya jinta. A kunnenta ta kara wayar,saidai har kusan shudewar mintuna guda tim ba wanda ya cewa da dan uwansa komai. 08187255862