← Book details A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 60

Sashe 44

A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

madeena" "Direct entry zanyi hamma.....i can't wait to see my family". "Alright....ka kula da kanka" Ya furta cikin kulawa "Na gode hamma" Ya ambata suna ajiye wayar. Wayar ya zubawa idanu yana tuna wasu abubuwa da suka shude..... Ita rayuwa dukanta tana komawa tarihi ne watarana......bai taba zaton a rintsin da suka fuskanta shi da musaddiq ba akwai ranar da zatazo kamar haka komai ya wuce ba......yadda kula da musaddiq da bashi rayuwa me kyau ya sanya hannuwansa sukayi kanta.....tunaninsa ya dimauta,kwanyarsa ta kusa jirkicewa da daina iya tuna kome me kyau.....ambaton sunan maamah ya zame musu kamar wata jarabawa. Hannunsa yasa ya shafi fuskarsa yana son ajiye tunanin a gefe.....yanzu yanzu zai iya rasa kowacce nutsuwa tasa,ya kuma rasa duk wani courage na aiki daya fito dashi a yau din. "Gidan maamah zai fara tsayawa" Yace da saddiq don ya shaidawa driver din shi kuma ya sanar da ayarin motocin. Yayi hakanne don yasan muddin ya shiga gidan maamah a yanayin da yake ciki na tuna munanan abubuwan data aikata baga rayuwarsu kadai ba......anni itace zata zamewa zuciyarsa yayyafin ruwan sanyin da zai wanke duk wani baci da ransa yayi. Kamar kullum da qafa ya taka daga inda suka ajiye motocin zuwa cikin gidan. Malam sa'adu ya matso da sauri yana bude masa qaramar qofar kasancewarsa shugaban masu gadi na gidan a yanzu. Tunda aka mallakawa maamah din wannan gidan yafi qarfin gadin malam sa'adu shi kadai,dole sai daya hada mata da security,amma kuma kowa yana qarqashin malam sa'adun ne wanda shike da permanent chair. Har kullum burgeshi hali da dabi'ar muhammadun takeyi,ya taka dukkan wani matsayi da bawa zaizo ubangiji ya kaishi a rayuwa,amma bai dauki hakan a bakin komai ba. Gaisawa sukayi kamar kullum,sannan ya taka yana shigewa cikin gidan da ma'aikatan dake bakin aiki kowa yake zubewa yana gaidashi. Daidai sanda yake sallama a falon daidai sanda take fitowa daga kitchen din gidan,Hannunta dauke da qatuwat warmer kamar ma rinjayarta takeyi. Huda ce,ta bishi da kallo tana amsa sallamar tasa cikin kallon baqunta. Yadan sake dubanta kadan,sai yake jin kamar yasan fuskar,amma kuma sai ya kauda wannan tunanin yana neman wajen zama,daidai sanda take gaidashi cikin ladabi daya zame musu jiki tun tale tale "Ina kwana?" Ko daya maida dubansa kanta sai yaga har ranqwafawa tayi irin na ban girman nan "Lafiya la....." Amsa gaisuwar ta katse saboda yadd warmer din taso subuce mata daga hannunta. Cikin zafin nama ya isa ya karba yana fadin "Kibi a hankali......" Sai ya taka yana kaita saman dining din ya ajiye. "Maamah ko?" Ta tambayeshi qasa qasa kaman me tsoron tambayar,don itadai yana mata kama da mijin adda sabreen din su. Kai ya jinjina kadan a ransa yana mamakin ina kuma maamah ta samota?. "Bari na kira maka ita" Ta fada da dan saurinta,can qasan ranta yana cike da murna,yau kam taga wani daya danganci addansu.....ko gaisuwa ta aike mata tunda yawan lokuta maamah tana cewa ta kira basa kusa. Wayar hannunta da maamah ta bata kuwa da komai akai,hasalima suna waya kusan kullum da momma bahijja,amma batasan me yasa number adda sabreen din kota kira sam sam bata shiga ba. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 A step na biyu taga maamah din tana saukowa daga saman,hannunta cikin na haneefa daketa bata labari. "Yammatana ya akayi?" Ta tambayi huda tana dan sake mata murmushin nan nata da kusan sun sana dashi. "Baqo ne kikayi" Ta fada tana dan waiwayawa inda fu'ad ke zaune,hannunsa dauke da remote yana sauya tasha,bawai kuma don yanason kallon bane aah....sai don kawai bayason kallon fuskar maamah din sakamakon abubuwan daya tuna da suka motsa ranshi. "Muje to" Ta amsata har qasan ranta tana jin dadin yadda huda din ta kasa gane wanene. Tanason sanyata ta koma daki don kada suyi wata magana da zata fahimci wayeshi a wajensu?,amma kuma ta rasa wanne uzurin zata bata tunda dai abinci zataci akan dining. Uwa uba kowanne motsi nata da maganganunta tana yinsu ne a ankare,bata bari tayi wani abu da zai sanya shakka a ransu ko ta gaza juyasu yadda takeso. Tunda suka sauko din haneefa ta zubawa fu'ad ido. Tabbas shine mijin adda sabreen,ta ganshi har sau biyu bata kuma mance ba,sannan bata sake ganinsa ba sai yau. Saman kujerar maamah ta zauna,haneefa ta zauna a gefanta still idanunta suna kanshi ta kasa daukewa. Sanda ya gama gaida maamah din sai nasa idanun suka sauka akan yarinyar. Kamanninta suka fusgi idanunshi sosai,ya sake ganin wata kamar ta daban bayan wadda ya baro dazu tana me komawa falo bayan sun hada idanu. Murmushi haneefa ta sakar masa sanda taga shima ya dan kafeta da ido. Ya murmusa kadan tana shirin janye idanunsa sai yaga ta zame tana fadin "Ina kwana mijin adda sabreen?". Kallon mamaki yake bibta dashi,mamakin da bai gama sakinsa ba tace "Sunana haneefa nice autan adda sabreen,'yar mitsisiyar dakinmu". Baisan ya akayi murmushi ya ratsa miskilar fuskar nan tasa ya bayyana ba,ashe masu son sarautar autancin suna da yawa. Yanayinta sak sai ya tuna masa da yanayin amna. " Ya isa haka haneefa....kije kuyi break ko ki koma daki wajen nadra ku kalli cartoon" Maamah tayi hanzarin dakatar da tattaunawar tasu. A nutse ya cira kansa yana duban fuskar maamah din,haka kawai sai yaji yana da buqatar ci gaba da magana da yarinyar. "Qyaleta muyi hira maamah....she's very smart" Ya fada da wani irin tone a muryarsa,wasu abubuwa da wani irin gudu suka fara bijiro masa,yayin da gumi ya fara tsargawa maamah ta cikin rigarta. Ta sani,tafi kowa ma samin haneefa she's very smart,fiye ma da zatonta,wannan ya sanya tafi janta a jiki da kuma kaffa kaffa da ita. "Indai surutun haneefa ne saika gaji dashi......ni kuma magana nakeso nayi dakai,next time idan kazo sai kuyi hirar" Ta fada tana dan hade rai gami da gyara zama. Sake dubanta yayi a karo na biyu,abubuwa biyu suka hade masa waje guda. Har yanzu dabi'ar nan tata tarashin son yara tana nan?,banbanci qarara me kuma fadin gaske na farko tsakaninta da anni. Indai haka ne yara uku ne cikin gidanma kenan?,akwai daya a cikin daki?. Me ya kaita dauko yara har uku?,ita da basu dameta ba?. Meye abun damuwa don yana hira da yarinya qarama?. Agogonsa ya kalla,sai ya maida dubansa ga fuskarta. "Ba damuwa ai,yau muna da enough time sama da kullum". Kafin ya sake cewa wani abu haneefa tace " Zaka kaini naga adda sabreen?......don Allah hamma kada kace aah" Ta fada tana narke murya. Maganar taja hankalin huda dake saman dining,itama saita ajiye spoon din abincin da takeci ta maido hankalinta kansu. Gumin dake tsatsatsafowa maamah din ya sake yawaita,da sauri kamar ana tankadata tace "Aah fa haneefa......ni da kaina mukayi zan kaiku haka ne?". "Eh amma har yanzu baki kaimu ba maamah,shi kuma hamma ma daga can yake ko?" Ta maida tambayar kansa. Kansa ya gyada a nutse yana karantarta. "Maamah ki barshi ya kaimu ko anjima ne,in yaso saimu dawo da kanmu" Huda itama ta saka baki,don da gaske sunyi tsananin kewar sabreen din. Sanda ta waiwaya da nufin yiwa huda din magana sai maganar fu'ad ta dakatar da komai. "Jeki dauki hularki kuzo muje nasa a ajiyeku" Yayi maganar kansa tsaye,maganar data daki tsakiyar kan maamah da wani irin ba zata. Har ga Allah kanshi tsaye ya fada kuma hankalinsa kwance,kawai dai a cikin zuciyarsa ya dade da rashin aminta da kowanne motsi na maamah din. Bashi da gamsuwa akan abubuwa da yawa sa suka shafeta,shi yasa a kusan komai idanu da zuciyarsa suna akai. Cikin qasa da minti uku sai gasu kowacce da mayafinta. Dab da zasu fita daga falon ta kirayi sunan huda da yanayin da tunda hudan tazo gidan bata taba gani cikin muryarta ko sautinta ba. Fuskarta a dinke ba fara'ar nan da suke kwana suke tashi da ganinta akan fuskarsu "Kada ku wuce ko ina,daga can ko dawo gida,zanwa driver magana zai biyo bayanku,karku wuce awa daya......." Idanu huda tadan zuba mata,sai kuma kawai ta gyada kai mamakin sauyawar maman tana kamata. Tasha musu alqawarin fa zata kaisu.......sai kuma daga baya tace ai wani uzuri ne ya taso sai bayan wani lokaci,duk da ta lura akwai permanent driver a gidan da yake zaune baya aikin komai. Yana zaune daga cikin motar saidai qafafunsa suna a waje ba'akai ga rufe masa murfin ba suka fito. Yadan daga kai ya kallesu,dukkaninsu suna kama da ita saidai qaramar ta fisu daukan kamanni sosai da ita. Mamaki kadan yana dan kamashi na ganin banbanci muraran tsakaninsu. Dukkansu da alama suna da sauqin hali da kuma tarbiyya sosai,don ba wanda ya gaidashi a tsaye a cikinsu saida suka rusuna "Ta fita zakka kenan" Ya gayawa kansa da kansa yana sauko qafafunsa qasa ya fito waje. "Abdulgaffar" Ya kirayi shugaban tawagar tsaron nasa,ya matso da gaggawa yana rusunawa "A cire mota daya a sakasu a kaisu gida" Ya bada umarni hankalinsa yana kan kiran fareeda dake shigo masa. Kaman yadda baya gajiya da qin dagawa hakanan itama bata gajiya da kiran nasa,yaja wani dogon tsaki yana komawa motar,ranshi yana tsananin baci da kalar wannan kiran nata da dukkanin numbers dinsa,kamar wadda batasan abinda ya dace ba,baisan ma ya akayi take da dukka numbers din nasa ba. "Soulmate" Sunan da tayi kiransa dashi kenan da wani irin salo na kashe murya da jan ra'ayi. "Why?.....ke bakya gajiya da kira ne?,it's so annoying.....please don't do it again.....stop it" Ya fada da sautin bacin rai a muryarsa. "Haba ka fahimceni mana" Ta sake fada da hanzari cikin tsoron kada ya katse mata wayar..... Kada ya ajiye wayar bayan ta samu dama ya daga wayar bayan dukka wahalar da tasha "Na fahimci me?....ke bakya ganewa cewa macace ke?,ke ya kamata abi bawai kibi ba?.....kina mantawa mace da kamun kai aka Santa?.....". Da sauri take girgiza kai "Indai a kanka ne bani da wadannan qualities din....." "Okay....then karki sake kirana....." Yaja qaramin tsaki yana yanke kiran hadi da jan dogon tsaki yana wurga wayar gefe. Gaba daya soyayya tana sake tona masa kanta a matsayin wani abu da yafi komai zama matsala da takura a rayuwa,shi yasa bazai bari ta kunno rayuwarshi yanzu ba har sai sanda ya shirya ya kuma kebe mata lokaci nayin nata. Idanunshi akan motar
Chapter 44 · 0% Book details