Sashe 21
A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wannan rudanin tare da fatar a yau ta samu warwarewarsa,don haka ta buda dukka idanunta tana bin kowanne kusurwa da kallo tanason samun warwarar rudaninta. Cikin nutsuwa da girmamawa anni ta miqe tana dosar inda maamah ke a tsaye,fuskar annin shimfide da fara'ar data ratsa har qasan zuciyarta. Har yanzu gangar jikinta da ruhinta basu daina jin farinciki da alfaharin aurar da fu'ad ba......wani abu guda daya daya zamewa maamah tamkar dafi tsakiyar tsokar zuciyarta "Ameenatu ce ta aurar dashi" Kalmar da inda tana da ikon gogeta tsaf saita gogeta daga dukkan wata ma'adana ta kalamai. "Barka da zuwa......sannunku da zuwa......" "Uwa kuma mahaifiyar muhammad fu'ad jadda ba,ai haka ya kamata ne gabatarwarki ta fadi" Hajja harira dake tsaye gefan hannun hagun maamah ta furta da wata irin izza. Kallo daya anni tayi mata ta watsar da ita gami da bawa banza ajiyarta,idanunta suna sauka akan fuskar 'yammatan su uku da take ganin tamkar ta taba ganin fuskar a wani waje. Kallonsu kawai tayi suka fara gaidata daya bayan daya,ta amsa musu tana dafa kan kowaccensu da madaukakiyar fara'a da kuma kulawa,kulawar da ta sauka har cikin idanun sabreen wadda ruhinta gaba daya yana a wajen,saidai babban qalubalenta bata iya jin me aka tattaunawa akai. Tun daga tashin anni har tsaiwarta a wajen sabreen na tuna guraren data taba ganin fuskar matar ne. Indai da gaske itace anni......itace uwa ga fu'ad ba shakka ta santa......amma ta yaya haka ta kasance?,ya akayi yake da uwaye biyu?,me yasa anni data taba sani duk da alkhairi ya hadasu ba ita ta nema masa ita ba?,sai waccar baquwar fuskar da bata taba ganinta ba kafin faruwar wannan abun kaf tsahon rayuwarta?. "Barkanki kade Ameenatu.......sannunki da hidima" Maamah ta maida mata da wani irin salon murmushin da ya sanya anni tajishi har cikin jinin jikinta. "Ina tayaki murnar aurar da fu'ad da kika samu damar yi......wannan babbar dama ce da zata zame miki tarihi kuma abun tunawa watan watarana.......ina aka tanadarwa mahaifiyar fu'ad domin ta zauna ita da qannen matarsa?" Tayi tambayar kai tsaye cikin isa...... "Ai albarkacin kaza qadangare kansha ruwan kasko mariya....muhalli har sai kin baiwa wani" Anni ta fadi duk da rabin hankalinta yana kan yaran abubuwa masu yawa suna yawo a ranta. Waiwaya tayi ta yafito muhsina inna uwaisha dake shirin wucewa "Itace mariya.......a cikata da irin karamcin nan da aka gada,koda zata cika hall dinnan da jama'arta.....a tabbatar an gamsar da buqatarsu,a nuna mata dattako da dattijantaka" Dukka anni tayi maganganun da kai da bakasan komai ba zaka dauka zallar magana ce kai tsaye,saidai gasu hajja da maamah din dukkaninsu sunsan magana ce akayi musu me harshen damo. Juyawa abinta anni tayi tana komawa cikin jama'arta,maamah tabi bayanta da kallo tana jin zafin jirwayen datayi musu me kama da wanka. Zafafan baqaqen maganganun data fahimci kowaccensu,amma kuma saiga murmushi yana subucewa daga saman fuskarta "Kwanaki kadan suka ragewa izzarki ameenatu.....na rantse koda pant din dake jikinki da kudin muhammadu aka siyeshi saikin zareshi kin miqomin.......na rantse sai na sanya fu'ad ya gaya miki maganganun da zasuyi silar ajalinki......maganganun da zasu zame miki dafin da zuciyarki zata buga ta tarwatse pieces " Tayi dukka maganganun ita da zuciyarta tana me cike da alwashi. Duk da wadannan abubuwan data samu ta kuma aiwatar zuciyarta ta kasa samun nutsuwa ko qanqani.......sam farincikinta har yanzu rabi ne......daga sanda ta iso bakin qofar mansion House din Alhaji hamza kibiya duka sai taji ta raina nata gidan kwata kwata. Batajin akwai wani gida ko gini da fu'ad zaiyi mata komai kyau da dukiyar da aka narkar ya zauna mata a rai muddin zai zamana muhallin Alhaji hamza kibiya yafi nata......indai zai zamana matsugunnin ameenatu zai d'ara nata. Daina fahimtar komai tayi......daina fuskantar duk abinda ake gudanarwa tayi,dukka idanunta dama hankalinta suna kan 'yan uwanta,suna kan kowanne motsi da kai kawo nasu. Hankalinta taji yana tashi,bata qaunar kowacce mu'amala ko alaqa kome qanqantarta tsakanin maamah dasu,saidai yadda taga tana jansu a jiki,ta wani.mugun sake musu ko ita batajin ta sake musu haka. Haneefa duk girmanta tana saman cinyarta tana wani lallabata,irin lelen da haneefa din keso a matsayinta na auta take kuma qishirwarsa. Cafko hannun amna tayi wadda ta zuge tata jakar ta fara fiddo sabbin 'yan dubu dubu kaman ba'asan ciwo da zafinsu ba.....kamar ba wasu abu masu muhimmanci ba tana zubewa sabreen din. "Kiramin su nadra.....kice suzo yanzu yanzu injini". Dubanta amna tayi duk da bata iya ganin fuskarta sosai. "Su waye?" Ta tambayeta don bata gane ba. Ajiyar zuciya ta sauke tana qoqarin saita kanta,sai sannan ta tuna amna din bata sansu ba "Sun shigo yanzu su da......." Ta dakata tanason tuna sunan da ake kiranta dashi "Su da maamah" Kai amna ta daga tana hangensu daga nan inda take,kwata kwata bata qaunar abinda zai hadata da matar,bata qaunar kallon da take binta dashi irin kallon dake fita daga idanuwanta zuwa kanta,amma zuwa aiken sabreen ya zame mata dole "Okay" Tace da ita "Na gode" Sabreen ta fadi da sauri saboda jin dadin zatayi mata abinda takeso a sanda bata da damar tashi. Da ido take bin amna sanda take nufarsu,duk wani taku dake qara kusancin ama dasu bugun zuciyarta qaruwa yakeyi,ta kasa dauke idonta daga kansu daidai da second guda har zuwa sanda ta qarasa gabansu. Taga amna ta mata magana,ita kuma ta waiwaya tayi magana dasu kafin ta sake dubanta still ta gaya mata wani abu daya sanya amna din juyowa ta dawo mata. "Me suka ce?" Ta fara da tambayar amna din tun bata gaya mata komai ba "Zasu zo.....zasu taho tare da maamah din wai". Idanunta ta maida ta lumshe tana girgizawa amna kai kawai. Wani irin rikitaccen yanayi yana sauko mata,kada dai ace suna jin wani sauyi na daban akan maamah kamar yadda takejin wajabcin bin umarninta tako ina yana ratsata?. Tun daga wannan sa'ar nutsuwa tayi mata qaura,ta kasa debe idanunta daga kan 'yan uwan nata,duk wani motsi murmushi da kuma fara'ar fuskarsu ya tabbatar mata suna jinsu ne cikin sukuni da farinciki,har zuwa lokacin da aka bada sanarwar isowar mahaifiyar ango zuwa inda surukarta take. Tamkar mejin tsoron wani abu haka zuciyarta taci gaba da bugawa sanda maamah ke kusantota tana takowa wajenta dasu nadra gaba daya. Idonta ta lumshe da sake budesu akansu gaba dayansu tana me kyautata zaton saisun iso gareta ne kai tsaye kafin aiwatar da komai......saidai kuma akasin haka ne ya faru. Kamar kowa suma wajen zuba kudin suka nufa,kowacce ta dire rafas na dubu dubu sabbi guda uku dake hannunsu huda kuma ta zuba biyar. Bin kudin tayi da kallo,suka kuma tsaye mata a rai. "Wai ina momma bahijja?" Tambayar da bata da amsarta batasan kuma wanda zai gaya mata amsar ba. Ta tabbatar daga kansu har zuwa momma ba wanda zai basu wannan kudaden son suzo su zuba a wajen.....amsarta ta fito sanda maamah ta cire wani rafas din ta bawa nadra da zummar ta qara a ciki. "To kuje ku gaisa" Maamah ta basu umarni sanda ta fara zube nata kudaden da suka ja hankalin mutane da dama. "Waye ya kawoku?, yaushe kukazo?,ina momma?" Ta damqe hannun nadra da tafi kusa da ita tana jera musu tambayar a gaggauce daya bayan daya. "Momma ta tafi yau....tun da safen mukazo,mun dawo gidan maamah......" "Tana da kirki adda.....kuma tace kema kina nan,zamuci gaba da ganinki.....kayanmu ma tace basai mun taho dasu ba......kawu yace muyi zamanmu zamufi samun kulawa". "Baki da hankali huda?" Ta fada da sauti me qarfi tana qoqarin janye lullubinta don ta samu damar saka idanunta cikin na huda. "Yi a hankali......idanun jamaa suna kanki" Maamah data sunkuya saman kanta tana maida mata lullubinta ta fada da murmushi akan fuskarta kamar wani abun arziqi take gaya mata. "Ku tafi mu zauna daughters" Ta fada da kulawa sosai a muryarta da cikakkiyar fara'a. Tana jin takunsu sanda suke sauka a wajen,ba damuwa ko wani abu cikin muryoyinsu,tana jin tafiyar nasu na buga zuciyarta sosai,tanaso qwalla ta fita daga idanunta komai qanqantarta ko zataji sanyi,amma ko daya bata samu wannan damar ba. Koda aka kirayi anni saita aike amna da wani qaramin akwati da ba wanda yasan meye a ciki aka ajiye cikin wani salo na siyan girma. *DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)* 08187255862 _ZAFAFABIYAR_ 22 Kafin a tashi tsaf ta rasa sauran nutsuwarta,wani irin tashin hankali takeji maras misali daga kowanne lungu da sashe na zuciyarta. Ba abinda ke gilmawa ta idanu da zuciyarta sai huda nadra da haneefa......ina momma bahijja?.....ina momma bahijja?,.....da gaske ne sun bawa maamah yaran?,ya akayi haka ta kasance?,ya akayi ta tafi ba tare da sunyi sallama?,ya akayi ta tafi ta barsu bata cika mata alqawarin data dauka akan 'yan uwanta ba?......zata sakene ta kalli rayuwarsu ta balbalce?,ko xatayi dukkan abinda ya kama tayi don ta tseratar da rayuwar yaran?. Wadannan sune tambayoyin da ta dinga yiwa kanta har a sanda take cikin kebantaccen qaramin parlor din da amna ta kawota bayan tashi daga taron,tace ta zauna zasu gana da anni. Dogayen yatsunta da suka sha lalle kawai take murzawa kanta a qasa,zuciyarta na wani irin zafi tare da jin qaguwar su koma gida ta lalubi maamah suyi magana ta sosai da ita.....koda tana jin kamar ta samu ikon sarrafa zuciyarta da bin umarninta cikin wani irin takura da takeji ana yiwa zuciyarta,.....to amma sam bata samu lago akan abinda takeji a zuciyarta game da 'yan uwanta. Qaunarsu darajarsu martabarsu da kuma soyayya da shaquwar data ginu tsakaninsu ba abinda ya sauya. "Assalamu alaikum" Muryar anni ta ratsa falon tana murza qofar ta shigo "Wa'alaikumussalam" Tada daga kanta kadan tana duban qofar gami da amsa sallamar. Kallon kallo suka yiwa junansu,kowanne a cikin su yanason tuna inda yasan fuskar dan uwansa. Sabreen ce tayi saurin watsar da qoqarin lalubo inda tasan fuskar annin,saboda gaba daya hankalinta ba'a nan yake ba,sai ta samu kanta kawai da zamewa daga saman kujerar tana gaidata,wata dabi'a data manta rabon data aikatata,amma a yau ta samu kanta da yin saboda wani kwarjini da taji matar tayi mata. "Koma ki zauna abinki daughter" Ta fada da kulawa amma saita kasa hakan,saita samu kanta da zama sosai tana tanqwashe qafafunta. "Na tsaidaki ko?,ga dare yana qara yi,duk da me babban sunan bai qaraso ba,uzuri ya taso masa daya saka dole ya fita" Kai ta