Sashe 38
A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da gaske ya kusa tabbata din TAQI KADAN YA RAGE SU RABU. Hannu ta saka ta karbi wayar,sai ta tura qofar bedroom din ta rufe ta koma ciki. Tana takawa cikin idanunta suna kan fuskar wayar,yau din a matuqar tunzure take,so batason wani magana da zata sake hasala hali da kuma yanayin da take ciki. Gaban madubinta taja stool ta zauna,sannan ta kunna wayar ta sakata a hands free ta dorata saman madubin,sannan kuma a hankali ta maida idanunta saman fuskarta kamar me kallon maamah din zaune a gabanta. "Ina jinki" Ta furta a nutse yana goye hannuwanta a qirjinta. "Ina fata kina cikin lafiya da kuma aminci qarqashin kulawar d'ana?" Tayi maganar a nutse tana son kamo bakin zaren ainihin maganarsu. Kamar ba zata amsa mata ba,sai ta daga idanunta daga kallon dogayen yatsunta da gaba daya lallen da akayi mata na aure ya fice tas,tamkar ma ba'a taba digawa yatsunta lalle ba,ta maida oily eyes din nata cikin madubin daya bayyanar da fuskarta dinnan me shimfidadden kyau dake dauke yau din da wani irin kwantaccen fushi. Zubawa fuskar tata idanu tayi kamar yau ta fara ganin kanta da kanta,iya kallon kawai yana motsa zuciyarta gami da tuna mata a karan kanta wacece sabreen,wani sashe na zuciyarta ya motsa yayi aikin daya jima baiyi ba,taji wani abu ya darsu a zuciyarta wanda ta jima tana yunqurin daddago dashi amma yana komawa "Ki ajiye wannan a gefe.....yaya jikin huda?" Tayi mata tambayar da take kwana da ita tana tashi ba tare da tasan waye zata yiwa ita ya kuma basu cikikkiyar amsar da take buqata ba. "Jikin huda?.....alhamdulillah......saidai ban da tabbacin yadda ya kamata ya kasance". A hankali ta lumshe idonta tana son yiwa amsar tambayar tata fashin baqi. Bugun zuciyarta yana son ninka gudunsa saboda samun mabanbantan amsoshi daga mabanbantan lunguna da saquna na zuciyartata wadanda basuyi daidai da fatanta dama abinda takeso taji ba. "Mu ajiye wannan......zan dan yaba miki game da yadd kike qoqarin ciyar dashi abinda muka baki,saidai har yanzu kin gaza cimma manufar abinda kikeyi din......caring kulawa.....ba wata halitta da batasan kulawa.....dole ki fara samun zuciyarsa kafin ki samu cikinsa da jikinsa....." ".......ba wannan cikin jarjejeniyarmu.......wai shin..kina zaton ina da buqatar zuciyarsa?,ko ina da buqatar hanyar da zata sadar dani ga shiga zuciyarsa?". Tayi maganar kanta tsaye da wani irin tsauri,saboda zafi da a yau zuciyarta keyi mata,tana jin kamar wani abu me kama da gajiya da kuma fara jin takura yana mintsinin zuciyarta. Murmushi me sauti maamah din ta saki tana gyara zamanta "Bana fatan ki samu zama ko shiga zuciyarsa na dindindin,a taqaicema dai....banda yanayi irin na lalura banjin kinkai quality din da zan baki license na shiga zuciyar mutum me tsada,namiji irin muhammadu ba.....amma karki manta,dole ne ki sadaukar masa da komai don isa ga burinmu.....idan nace komai ina nufin komai da komai fa,na zabeki ne saboda ina da tsammanin zaki iya bada komai don cikar muradina.....koda kuwa jikinki ne...." "Ya isa!" Ta furta a tsawace saboda jin maganar tata ta fara shallake guri,uwa uba tana neman fin qarfin kanta. "Kibi a hankali......a yanzun duk da ban mallakeshi ba,amma zakisha mamakin abinda zai biyo baya idan har na shaida masa matarsa tana min shouting tana kuma dagamin murya....." Zafin radadin maganarta ta farko bata saketa ba,don haka bata maida hankali sosai akan maganarta ta biyu ba. Burinta shine ta furzar mata da abinda yake ranta,tana jin kamar takai maqurar da zasu dinga wasan tamaula da ita tsakanin ita da d'anta. "Zanci gaba da ci dashi kaman yadda iya abinda yake zayyane kenan a bisa yarjejeniyarmu......daga hakan banajin zan qara akan komai.....faduwarki ko nasararki ya ta'allaqa ne da yadda na samu tabbacin lafiyar qannena" Daga haka ta katse wayar kawai tana ajeta a gefe. Taso tayi tariyar maganganun da sukayi da maamah din,amma a yau sai taji gaba daya bata da buqatar tuna komai.....kawai tana jin ba zata iya ci gaba da zamowa kamar tamaula tsakanin su ba. Wani irin confidence takeji,saita miqe tana komawa bakin qofar da zummar ajewa zuwaira wayarta,ta dauka duk sanda ta dawo,don ko haduwa da ita bata sonyi. Ga mamakinta a tsaye ta sameta a bakin qofar kamar wadda aka bawa gadinta. Wani kallo ta jefeta dashi tana jin sam matar bata mata ba "Ba wani abu da ake buqata?" Ta fada da sauri bayan ta karbi wayar ganin sabreen din na zummar shigewa ciki "Babu" Ta bata amsa a taqaice tana maida qofarta ta kulle. Yadda yau yarinyar ke amsa mata magana a tsaitsaye sai takejin kamar akwai abinda ta taka,akwai abinda ya bata confidence a kanta. Ci gaba tayi da juya wayar a hannunta tunaninta yana yin nisa gami da rarrabuwa kashi kashi. Wani tunani ya kutso mata cikin kwanyarta "Me yasa ba zaki murza kambunki ba?,ki gwada qarfin iko da mulkinki ba har akan fu'ad din?" Wani sashen na zuciyarta ya bata shawara. Shuru tayi tana sauraren daya bangaren tare da juyar maganar cikin kwanyarta. Kai ta gyada tana bawa kanta tabbacin tabbas wannan din zaiyi aiki.....koda baiyi diki dari bisa dari ba to akwai yiwuwar samuwar galaba. Tana qoqarin kiransa ta shaida masa tana buqatar ganinsa sallamarsa ta mamayeta. Tana amsa sallamar farinciki na cika zuciyarta yadda Allah ya dubeta ya jefo mata shi,saidai a saman fuskarta ba haka bane. Ranta yan a hade,hakanan ta boye duk farincikinta don tanason ko meye zata gaya masa ya daukeshi da muhimmanci. Sai daya iso gabanta ya zame yana gaidata ta hanyar tsugunawa saman qafafunta. Bayan ya gama gaidata din shuru ya biyo baya,a nutse yace "Ba komai da ake buqata?,ba wani matsala?" Yayi tambayar data zame masa wajib duk sanda yazo gaidatan don qoqarin sauke haqqin Allah da yakejin ya zama wajibi ya sauke din. Kai ta girgiza fuskarta a daure. "Ba abind nake buqata.....amma matsala dai akwaita". Daidaita tsugunnonsa yayi kafin ya zame ya zauna sosai a gabanta. Duk sanda tayi wannan yanayin kota furta magana makamanciyar wannan zai wahala idan ba wani aikin bane zaya zameshi. Idanunsa yadan lumshe gami da budesu duka lokaci guda cikin qoqarin hadiye fargabarsa,yana tunkarar qalubale komai girmansa.....gaagwarmaya komai wahala da kuma taurinta,amma har yanzu zuciyarsa baya iya jure wadannan halayen da maamah din,dabi'unta suna kassarashi,ya kasa sabawa,baisan me yasa ba,ko don ita dinn wata jigo ce da abubuwanta ke tafiya ba yadda ya kamata ace sun tafi ba?. "Wacce matsala ce?,me yake faruwa?" Ya tambayeta a nutse. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ _Daga abi sa'eed RA yace:manzan Allah S A W yace; "idan dayanku yazo masallaci,ya duba takalminsa,idan akwai qazanta ya shareta ya kawar da ita daga jiki,yayi sallah da takalminsa_ *_halal ne sallah da takalmi a qafa,na haramci a ciki muddin ba najasa a jiki_* "Muhammadu" Ta kirashi da ainihin sunansa,ba tare kuma data bari ya amsa ba ta dora "Nikam bansan a rayuwa akwai wani abu da yafi haihuwarku da nayi muhimmanci ba" Idanu ya zuba mata yana jin tamkar ya tashi ya fita da gudu ya tserewa maganganunta,don yasan zai wahala ba kamar kullum bane,dora masa nauyi da mas'uliyyar da zai gaza dauka kota masa tauri. Kai ya girgiza,ya buda baki zai magana ta sake danneshi da kalamanta "Bansan wanne irin rashin muhimmanci nake dashi a rayuwarku ba da har zan zartar da hukunci cikin rayuwarka,nace kum ga alfarma ko abinda nakeso kayimin ka gaza yi din,ace har yanzu maganganun ameenatu da umarninta yana zama gaba da nawa?" Ta qarashe maganar tana jin dacin haka sosai har cikin zuciyarta. Batasan wanne tozarci ma ya kamata ameenatu ta fuskanta ba aduk sanda haqanta ya cimma ruwa,har yanzu idan tayi hasashen abinda zata saka ta fuskanta sai taga wannan hukuncin yayi kadan. Sam baya qaunar ta dinga sanyo maganar anni cikin maganganu da ayyukansu,don bazai iya tuna sanda anni ita tayi magana a kanta ba indai ba alkhairi ba. "Muhammadu.......yanzu ni da hannuna na baka amanar yarinyar mutane......na roqeka ka mu'amalanceta kamar kowanne miji da mata.......ka kyautata mata ma faranta mata,ka jata a jiki amma haka ga gagara?,ka kasa cikamin wannan alfarmar da zata bayya a irin kima da martabata a idon yarinyar?". Qasa yayi da kansa,shi maganar ma nauyi tayi masa sosai akai. Ta wani gefen kuma ranshi da zuciyarsa suma motsa. Yanzu har taurin kan yarinyar da tsaurin idonta yakai ace ta kawo ma maamah qararsa?,har da maganganu irin wadannan marasa dadin ji?. Sai data gama dukkan wani fada baice komai ba,har sai da tayi shuru sannan yace "Kiyi haquri,in sha Allah za'a sake yin qoqarin gyarawa da canzawa". Ya furta a taqaice. Har cikin ranta yadda ya amsa mata haka a sauqaqe ya faranta mata sosai "To Allah yayi albarka" Ta fadi kalmar da bazaice when last da yaji ta fada ba. Muryarsa a sanyaye ya amsa mata,sannan ya miqe yana mata sallama yana fita daga falon. Tun kafin ya qaraso Jordan ya wangale masa qofa,da wani irin zafi ya isa ya shige motar Jordan ya maida murfin motar ya rufe. Suit dinsa na sama ya fara ballewa yana zareta daga jikinsa saboda wani irin zafi da yakeji tun daga zuciyarsa har cikin fuskarsa. Iske me qarfi ya fesar daga bakinsa bayan ya zuqi wata "Wanne abune meqarfi da girma a tsakaninsu bayan wannan?" Ya jefawa kansa da kansa tambayar yana motsa labbansa. "Ita ta shiga jikin maamah ko maamah ce ta shiga jikinta?" Ya sake maimaita tambayar da ba wanda zai iya bashi amsarta. Yanzun har matsayinta da girmanta wajen maamah yakai ya samu sanyawar albarkar maamah din saboda dalilinta?,wanne aiki take mata haka me faranta rai bayan abinda yake suspecting?. Tunanin daya rakashi kenan har cikin office dinsa,ya kuma wuni yana tayashi zama,duk kuwa da uban tarin ayyukan daya samu suna jiransa. Duba documents da sanya hannu cikin wasu takardun,wasu takardun suna da buqatar hankalinsa da nutsuwarsa kafin yakai ga sanya hannu,da qyar ya hada hankalinsa bayan sallar la'asar ya soma duba wasun,bayan ya yiwa kansa matsayar matakin da zai dauka. Komawa tayi ta sake kwanciya bayan sallar la'asar din,tana lissafin nan da awa daya koda rabi zata shiga kitchen saboda shi.....saboda mutumin da ba ganin girma qima ko martaba sam sam tsakaninsu. Idanunta ta runtse,a yau tana jin wani zafi zafi na yadda maamah ta bautar da ita. Batasan me yake tilastata lallai saita