← Book details A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 60

Sashe 29

A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Cikin kwanakin har ruwan jikinta takeji kaman ya qare saboda tsabar wani irin kadaici da dumbin tunani da yake cike a kanta. Sati hudu cur tana a cikin gidan......ba motsin kowa ba gilmawar kowa,ba hira da kowa,ba waya,daga ita sai tv sai karen gidan dake haushi nesa da muhallinta. Ada ko parlor din bata fitowa tana qunshe a daki,daga bisani ta fahimci depression na loneliness zai iya kamata,don haka da kadan da kadan ta fara fitowa tana zama.
Saidai daga zaman sai bacci,sai wanka sai wata kwanciyar. Gyaran gidan kansa bai wani dameta ba,don tana ganin ba wani muhalli bane da zata damu kanta a kansa,hasalima a nata ganin waje ne da lokaci kawai take jira ta barshi. Abu biyu take gyarawa,bedroom dinta sai kitchen din da ba wani abun arziqi take dafawa ba. Tun ranar da tayi abincin safen nan rabonta da tayi wani cikakken abinci ta sawa cikinta,iyakar yunwa idan ta ciyota ta soya qwai guda biyu... Kota dafa indomie guda daya kota soya potatoes taci shikenan.
A kwanakin tana jin yadda qirjinta yake riqewa amma taqi damuwa da wannan bare takai hankalinta kai,abu daya kawai take jira ya dawo,tayi duk yadda zatayi ta cika aikin maamah ta samu freedom. Ta sani tana da wata fitinanniyar ulcer data kusa sanyata tabi bayan mahaifi da mahaifiyarta bayan rasuwar ummensu. Ulcer data samo asali daga matsiyaciyar yunwar da tayi mugun horasu,takaita matakin da take xubda aman jini. Ta jima rabon data tashi,tunda ta samu sassaucin rayuwa suke iya ci su qoshi,amma a kwanakin nan da take bata alamu taqi maida hankalinta sam sam.

"Alhamdulillah" Shine abinda ya furta lokacin da ya fito daga toilet wanda ya barshi wata guda cur kenan.
Shirya kansa ya fara yi cikin butter milk color pyjamas yana tunanin kiran me sunan malam da ameh gobe kowa ya dora aikinsa a inda ya tsaya. Sam har ga Allah ya sha'afa da ita,abinda ya sameshi ya shafe abubuwa da yawa a kansa.
Gidan duka ya masa datti a yadda yake tsantseni da tsananin tsafta,ya kammala shirin nasa sai ya kasa saukowa saboda gajiya,ya bude freezer dinsa dake dining area dinsa na sama yana fatan samun wani abun.
Wuta ce 24/7 da kome zaka ajjiye a fridge din zaka sameshi fresh. Damammiyar fura ya ciro wadda ba komai cikinta daga nono din sai furar da aka markadasu suka hade jikinsu sosai. Furar daya samu ta masa daidai,don abace dame relaxing jiki da bada bacci me kyau da daddare saboda sinadaran da gero ke dauke dashi. Ta masa sanyi,baya kuma shan abu me sanyi sosai har haka,wannan ya sanya ya ajiyeta ya koma ya kunna tv don ya rage mintunan da zaiyi jiran furar.
Kadan kadan takejin kamar wani baqon sauti cikin gidan sanda take baro kitchen inda ta soya qwai guda biyu,tana taraddadin ci ma saboda maiqon dake jiki amma kuma batajin tana da wani abinciii bayan shi.
Fargaba taji tana cikata,wani irin matsanancin tsoro ya saukar mata. Sound ne tabbas wanda bata tantance na meye ba. To ko haurowa gidan akayi?,ko wani ne ya shigo ciki ya boye ba tare da sanin securities din ba?. Duka ba kalar tunanin da batayi ba,jikinta na rawa ta qarasa dakinta ta maida qofar ta rufe tana maida numfashi. Jin still da sound din sai tsoron yaqi barinta,ta taka da hanzari tabi duka windows din ta kulle sannan ta dawo tsakiyar dakin ta zauna tana raba ido tare da sauraron koma meye daga inda zai bullo.
Sai data masa daidai sannan ya kashe tv din,ya dauketa ya hada da cup da spoon ya wuce daki.
Sake kasa kunnenta tayi da kyau,a yanzu ba sound din,saita lumshe ido tana qoqarin saita nutsuwar kanta. Bata taba sanin kadaici masifa bane sai yanzu,bata taba sanin haka yake taba ruhi da rayuwar mutum ba sai yanzu. Wasu hawaye suka biyo ta lumsassun idanunta suka gangaro kan fuskarta. Gaba daya ta koma wata raguwa a kwanakin,zuciyarta kwata kwata ba wannan qwarin da tsaurin sai wani irin rauni da ya sake cikata,sai kawai ta kifa kanta saman pillow din ta saki siririn kuka,fried egg din da bata iya ci ba kenan.
Chapter 29 · 0% Book details