Sashe 12
A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yawan gift din da yake samu suna da alaqa da abu me qamshi,walau turare body mist ko makamancin hakan......farouq ya dade da sanin wannan,shi ya sanya ya saka company din da sukayi aikin shirya gidan suka tsumashi da qamshi. "Ko zata iya tsaftace gidan ya zauna a haka?" Ya raya a ranshi,sai ya tabe baki yana juyawa zuwa barin hannunsa na dama gami da jan qaramin tsaki. "Ruwanta tayi tsafta ruwanta kada tayi" Ya raya a ranshi. Abu daya ya sani shi din zamansa a gidan bame tsaho bane,don zuwa yanzu dole ya fara tabbatar da tsaiwar company dinsa na abuja da za'a bude kafin ya sakar musu. Wani abu kadan yaji ya taba ransa daya tuna yawan massages da yake samu na barazana akan company din "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Ya furta murya qasa qasa (Shin kinsan qarfinta kuwa?,kisan aikin da take yiwa me yawan ambatonta?,damuwa gareki?,ciwo ne?,ka maqiya suka sakaki a gaba?,ki kamata qamqam ki hada da salatin annabi kisha kallo,Allah ya bamu dacewa yayi mana maganin damuwoyinmu ameen). *******Ba zata ca ga sanda wahalallen baccin dake cike da mugun zazzabi ya dauketa ba,ita dai ta bude idanunta ne kawai ta ganta kwance daga bakin gadon,wanda ta tabbatar da tayi mugun juyi cikin baccinta ba abinda zai hanata fadowa. Tsoro gaba daya ba dabi'arta bane,amma kuma tun a jiya ta fuskanci yana neman samun wajen zama cikin zuciyarta da ruhinta. Tsoron abu guda kawai zata iya cewa ta fahimta.....girman gidan data tabbatar yafi qarfin zaman mata hudu ma da iyalinsu.....alamun motsi da shigowar motarsu dama fitar da motar ta sakeyi,daga haka bata sake jin komai ba amma kuma tsoron bai saketa ba. Idanunta ta maida ta lumshe. Ba ciwon kan zuwa yanzu,ba kuma zazzabin,saidai tana fatan rufe idanunta da tayi dinnan ta budesu ta samu komai ya koma mafarki......komai ya shafe tamkar bai faru ba. Saidai inaaa.....akace qaddara ta rigayi fata,koda ta bude komai yana nan kamar yadda yake,agogo naci gaba da tafiya ba tare daya koma baya ko na second guda ba,wannan shi ya bata tabbacin babu abinda zai canza din,don haka ta yunqura ta miqe da wata irin kasala tana sauka daga saman gadon. Qofa guda daya da tafi kama data bandaki ta nufa. A hankali ta shiga kamar me tsoron wani abu kada ya kamata idanunta nabin kowanne sashe na bandakin da kallo. Komai luxury ne kuma designer daya sanyashi yasha banban da toilets da dama. Sai data bata lokaci tana qoqarin tantance komai,sannan ta isa sashen wanka dake dauke da jacuzzi da bathtub,ta soma zare kayan jikinta. Ko ina na jikinta ya mata nauyi,sam ba dadi saboda nuqurqusar zazzabi,uwa uba kuma akwai rashin sabo na kwanciya ba tare da tayi wanka ba,don haka yanzun kai tsaye taji wankan tafi buqatar yi kafin komai. Sanda ta isa ga closet dinta kuwa sai taji gaba daya ta raina duniyarta ta baya,duk yadda taso abun kada ya burgeta amma hakan bai samu ba,dolen dole ma ya burgeta,komai a jere a tsare tamkar wani hamshaqin boutique daya amsa sunansa ta fannin saida komai da komai. Sai yanzu ta fahimci maganar da hadiyya takeyi bayan sun dawo daga gidanta,suturu ne da batasan iya sanda zata kammala sakesu ba,kusan komai ya cakude,kayanta na gida da wadanda ta taras a nan,bata ma iya ganin natan kwata kwata,duk yawa ta suturarta kuwa sun boye tsaf cikin closet din. Batason ta wahalar da kanta da yawa don bata da wannan energy din,dole ta zabi atamfa kawai riga 3quater da straight skirt ta saka. *******Tun daga daren jiya data dawo daga gidan maamah din wato mariya,bata samu wani cikakken lokaci daya haura mintuna talatin ba cikin tunani ba. Kowanne motsi da zatayi yana motsa mata da tsananin kwadayin cikar burinta,wato wanzuwar jininta cikin jinin mamallakin kamfanin sarrafa gold da diamond din. Ta sani......akwai wasu tsauraran hanyoyi daya kamata ace an sharesu fetal kafin takai ga haurawa izuwa nata bigiren......to amma shin.....mallakar fu'ad a hannun mariya kamar yadda takeso zai iya zama mataki kuma mabudin tata nasarar?. Amsoshi guda biyu ne wato eh da kuma a'ah. Eh idan har tayi nata aikin akan hajiya mariya tazo hannunta.....ita din zata zame mata tsani na mallakawa tata shalelen fu'ad. Aah idan har ta gaza samun mariya a hannunta ko kuma fu'ad ya gagara zuwa hannun mariya kamar yadda take buri......shin me zai hana tayi nata aikin itama daga gefe?,tayi amfani da tata basirar?. Wannan tunanin kadai ya sanyata yankar asubahi,bata kuma tsaya a ko ina ba sai a gaban babban bokanta wato BAHAGO. Maida foldable basket din me zip tayi ta rufe gami da zuge zip din,sannan ta maida idanunta kan zuwaira dake zaune a gabanta "Ina fatan kin riqe dukan baya naina......don a haka nakeso su shiga kunnuwanta tamkar ni nake bayanan......bana buqatar mantuwa ballantana ganganci ko kuma kuskure zuwaira.......zaki zauna kuma a iya matsayinki na 'yar aiki kawai" Kai zuwaira ta jinjina mata. Taji dadin wannan matsayin sosai da maamah ta dauka da danqa mata,ta wannan hanyar kawai zata nunawa hajja qarfin mulki da isarta akan maamah din. Saidai kafin tace komai anyi knocking daga waje "Waye ne?" Ta tambaya cikin qosawa,don ta fara gajiya da yawan baqin da suketa zuwa ganin gida. Jiya a daren bata kwana da kowa ba cikin gidan,tun a daren kowanne baqo ta sanya aka dinga dibansu ana kaisu gida,na wani garin tunda asuba aka debi hanya dasu. "Nice......baquwa kikayine tace na gaya niki" "Baquwa kuma?" Ta tambaya a mamakance,don bata tsammanin samun baquncin kowa a wannan lokaci,hasalima ta gayawa malam Sa'adu kada a sake bari kowa ya shigo,koda sun shigo ta barwa masu aiki sallahu ko waye a gaya masa tana hutawa ne. "Wacece baquwar?" Ta tambaya kai tsaye cikin bacin rai "Hajiya harira" Yarinyar ta amsa mata kai tsaye "Shigo da ita" Itama ta bada amsa kanta tsaye,saidai kuma can cikin ranta tana mamakin abinda ya kawota,don a jiya sun rabu ne tanata mata tsiya,ba zata kuma ganinta ba sai ta huta da kyau. "Kada dai ace har kin watstsake hutun kuma ya qare?" Maamah ta fada tana tsokanarta. Wani murmushi ta saki mai nuna alamun akwai damuwa. "Ina naga ta hutu mariya?,matsala ta tasomu gaba tun cikin daren jiya?". Idanu maamah ta fiddo tana matsa mata wajen zama "Subhanallah.....ni wallahi har kin sanya gabana ya fadi......matsala ko yaya take banson jin koda sunanta,me kuma ya faru?". Baki ta tabe tana zama kafin ta bata amsa "Waini harira za'a gwadawa iya shege?.wai qanin mahaifin laila ne yazo yakeson gwadamin qaramin shege ne shi.....lallai lallai wai ya bada laila.....aure nan da wata guda me zuwa". Ido maamah tadan fiddo a mamakance "An gaya masa a ina yanzu ake hakan?,ya akayi kika bari yayi wannan bunqasar hajja?". Kai ta girgiza irin kana cike da tsananin takaicin nan "Ki barni dashi......zan gwada masa tawa iyawar indai harira nake.....shi yasa kika ganni gab da takewar rana.....ajiyar laila nakeson kawo miki". "Laila ai d'iyata ce.....wannan bazai zama matsala ba". "Shege ne fiye da yadda baki zato,shi ya kusan zamemin matsala zamanin zamana da abbansu.......inda zai yiwu kuma ba takura.....kiyimin wannan alfarmar ki ajemin ita gidan fu'ad,don na tabbatar a can dinne ko daga qiyama ubansa zai dawo bai isa ya shiga da sunan koda ganinta ba ballantana daukota......wadannan qedarun sun isheshi". *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_* 08187255862 15 Da farko maganar taso yiwa maamah din banbarakwai,amma koda ta tuna wacece hajja a wajen ta da kuma tata fafutukar da suka gama yi tare suke ma kuma kanyin sai taji wannan din ba komai bane.....ai rama halasci sai dan halak,banda ma plan din da take dashi batajin zai zama wani abun damuwa don laila zata zauna gidan. Ta tabbatar bata da matsala da laila,ko ita din tana iya zama me sanya musu idanu akan plan dinsu. "Kada ki damu hajja,ni ba abinda bakiyimin ba,kinfi qarfin haka a wajena.....hakanma qarin samun tsaro ne,don yau nakeson tura zuwaira ta zauna dasu ta dinga sakamin ido akan komai". Murmushin qasan zuciya hajja ta saki,bahago shu'umi ne fiye da yadda take zato,ya gaya mata,ya sake gaya mata dama ba damar musu......mariya ba zata iya musanta mata ba. "Na gode sosai mariya....Allah ya saka da alkhairi ya qara zumunci". Kai ta girgiza tana murmushi "Ba wannan tsakaninmu,kinfi qarfin komai a wajena......ko yau tana iya shiryawa sai zuwaira ta biyo ta dauketa su wuce,don banason magariba tayi basu isa gidan ba" Ta fada tana daga wayarta ta duba lokaci. So samu ace tun da safen nan ya karya da breakfast din yarinyar da zai zama lullube da makamanta,to amma sannu sannu bata hana zuwa saidai a dade ba'aje ba. Da wani irin farincikin samun nasara ta isa gida. Ta samu laila din zaune a falo tana kallo. Kusan tunda ta kammala karatu aikinta kenan. Hajja tayi tayi a samar mata aiki ta fara tace sammm ita ba zata iya yawo a gari kowacce safiya ba,hasalima ba zata iya barin baccin safe ba,idan ta barshi waye zaiyi mata shi?. Sai data sha ruwa sosai da lemo,sanyinsa ya sanyata ta fara dawowa hayyacinta sannan ta maida dubanta kan laila dake matse matsen waya. "Mansura ta kawomin kayan nan kuwa?" Kai laila ta girgiza alamun a'ah ba tare data dauke idanunta daga kan wayarta ba. Hotunansa ke matuqar jan hankalinta,kullum kwanan duniya ta kalleshi kota tuna dashi sai taji kaman bata tare da nutsuwarta. Tsaki hajja taja ta jawo wayarta tana mita ita daya "Yarinyar nan inajin sai taje gidansu tayi kwana biyu sannan zata shiga hankalinta". Dab da kiran data mata zai shiga sai gata ta shigo. Niqi niqi dauke da kaya wanki a wanke a goge a hannunta. Mansura daya daga cikin surukan hajja da suke rayuwa gida daya,suke kuma karban duk wani mulki isa da izza tata hannu bibbiyu don ba yadda suka iya,an dauresu da duk wani zaren sihiri da zai bata damar mallakarsu kamar yadda ta mallaki mazajensu. Ko sallamarta bata amsa ba sai harara data jefeta dashi "Uban me kika tsaya yi?,na baki wanki tun bayan asuba da kadan amma sai yanzu zaki gama don bakisan muhimmancin kayan ba?" Bata amsa mata ba saboda nauyin kayan har sai data zubesu. "Kiyi haquri hajja,sai dana sallami yara suka wuce makaranta,abbansu ya fita kasuwa sannan....." "Sannu dadi 'ya'ya dadi miji,bakisan aikina gaba yake da nasu aikin ba su duka?,kada ki