← Book details A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 60

Sashe 59

A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai yau da taga qarshensa. Duk da cewa ya bata mata lokaci sosai,don sai a yanzun sha daya saura na dare ta kammala......amma kuma ya haifar mata da wani irin nishadi a zuciyarta,nishadin da duk idan ta tuna yadda rayuwar stars din ta kasance a ciki sai taji ta saki dan murmushi kadan. Sam ita din ba ma'abociyar kallo bace......wannan shine film na farko data fara kara full kuma wai korean series. Idanunta ta lumshe tana shaqar iskar dake kadawa sosai take kuma yiwa kanta hanya ta windows din dakin da yawanci yakan barshi a bude saboda samun fresh air da tafi iskar ac artificial air dadi a wajenta. Gabanta yadan buga kadan,tayi kuma hanzarin bude idanunta sanda taji kaman motsin taba window din. Ta tsaya cak daga qoqarin fidda rigar jikinta da takeyi,tsahon mintuna biyar bata sake jin komai ba,saita matsa gaban windows din dukansu,ta bisu daya bayan daya ta zugesu,ta kuma sanya musu lock. "Sabreena kin zama matsoraciya" Ta tsokani kanta da kanta,ta kuma sakarwa kanta da kanta din murmushi. Ita kanta batasan yaushe ta koma hakan ba,saidai girman gidan koda rana ce ta take tsoro yake bata,duk da tassn cike yake da security musamman idan ma'u ta gama kai kawonta ita da ameh kowa ya wuce gefansa. Towel ta daura babba,har zata wuce toilet din taji kaman yau garin da iska,don haka ta miqa hannu ta dauki hijab din da tayi salla dashi ta zura a jikinta ta wuce bandakin. Tana wankan amma kadan kadan takejin gabanta yana faduwa wanda ita kanta batasan dalili ba. Yau din sai ta samu kanta da rage tsahon lokacin da takan dauka a bandakin,cikin qasa da mintuna goma ta kammala,tayi brush ta busar da kanta,sannan ta daura towel din ta maida hijabinta ta fara takowa tana fitowa. Sanda ta dora hannunta akan handle din gabanta ya sake yankewa ya fadi. "Hasbiyallahu wa ni'imal wakeel" Ta furta a hankali kaman yadda yanzu yadan fara zama a jikinta,don cikin jadawalin karatunsu da rumaisa akwai azkar sosai da addu'o'i masu yawan gaske. Jiki a sanyaye ta murda handle din ta jawo qofar ta bude sannan ta fito,kai tsaye ta soma nufar madubi. Abun mamakin yadda takejin baqon qamshi cikin dakin,tadan tsaya kadan tana buda hancinta still qamshin takeji,sai kuma tunanin iskar dake ratsowa ta cikin rufaffun windows din qilan ke debo qamshin daga waje zuwa dakin,don haka hankalinta kwance ta qarasa gaban mirror din tana duba fuskarta da jiya taqi wani qurji qwaya daya ya fito mata. Wutace tsaf ta dauke mata kafin wata mahaukaciyar faduwar gaba ta rufto mata,tun daga saman kanta har zuwa yatsun qafafunta da ganin fuskar dake tsaye a bayanta. Dagawa qirjinta ya shiga yi daga sama zuwa qasa cikin wata irin razana da takejin kamar tana shirin dimaucewa ne......sake matsota yakeyi idanunsa cikin nata,kaman yadda fuskarsa ke shimfide da shu'umin murmushin nan data saba gani a fuskarsa a shekarun baya. "Mmmm........." Ta dinga yunqurin fadin sunansa,amma sai taji kaman an sanya gum an manne labbanta na sama da qasa guri guda. *_TOFA!_* *_WAYE WANNAN?_* *_NACE WAYE WANNAN?_* *_MUHAMMAD FU'AD NE DA KANSA?_* *_KO KUMA WANI MUTUMIN NE NA DABAN?_* *_TURQASHI_* *_Allah yasa muna cikin masu rabon ganin ranar litinin lafiya_* *_karku yadda karki yarda aci gaba da sukuwa da zamiya cikin labarin nan ba tare dake ba_* *DA SAURAN KALLO!!!* Tofa nayi qarqaf Allah ya bani ikon baku na ranar monday _Daga ummu habiba uwar muminai Allah ya qara yarda a gareta tace,naji manzon Allah S A W yana cewa "duk wanda ya sallaci raka'a sha biyu daga rana zuwa dare(bayan sallar farillai guda biyar),Allah zai gina masa gida dasu a aljanna_ _muslmin ne ya rawaito_ _raka'o'in nan sha biyu sune,biyu kafin asuba,hudu kafin azahar da biyu bayan azahar,biyu bayan magariba,biyu bayan isha'i saiki qara da wuturi_ _Sannan akwai hidisi me zaman kansa abdullahi bin umar ya rawaito,manzan Allah S A W yace ALLAH KA YIWA BAYAN DAKE SALLAH RAKA'A HUDU KAFIN SALLAR LA'ASAR RAHAMA_ *_IBADA DUK IBADA CE,AMMA MAFI SOYUWAR AIKI A WAJEN ALLAH DUK QANQANTARSA SHINE WANDA ZAKA DAWWAMA KANA YI,SAIKA DAUKI WANDA KASAN ZAKA IYA DOREWA_* Tana kallonsa ta cikin madubin yana ci gaba da kusanto inda take,saidai gaba daya ta kasa motsa koda yatsanta ne ballantana tayi tunanin abu na gaba daya kamata ace ta aiwatar. Shu'umin murmushinsa da kallon da yake dubanta dashi duka ba wanda ya fasa,yaci gaba da kusantota kowacce gaba ta jikinsa tana jin wani shauqi tare da dokanta ta sadar da kanshi gareta. Irin yadda ya fitinu da ita ba abu bane me sauqin fassarawa ba......sai kuma gashi a bagas zaice ko a banza wata hanya ta samun isa gareta ta riskeshi cikin sauqi,wanda zai iya kiran hakan da qatotuwar sa'a cikin rayuwarsa. "Mashkur!" Ta fusgi sunan da hanzari ta kirashi a tsawace bayan ta maimaita la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen har batasan adadi ba. Tsaiwar da yayi ita ta bata damar waiwayowa da wani irin hanzari kamar wadda aka fusga. Idanu ta zuba masa kaman yadda shima idanun ya zuba mata yake kallonta da dukka iyakacin kallonsa. "Me ya kawoka gidan mutane?......har dakin matar aure?" Ta fadi da wata irin birkitacciyar murya data cika da razani da tsoro. Wata irin dariya ya qyaqyace da ita,harda komawa ya fada saman gadon nata,sannan ya tashi ya miqe yana fuskantarta. Ya bude baki zaiyi magana a hankali sautin saukar ruwan saman farko ya baqunci kunnensu,shatin ruwan ya fara sauka ta glass din windown dakin sai ya saki murmushi yana dawo da dubansa kanta. "Kin gani ko?,.....ko Allah ma yana sona......ko Allah ma yasan kin cuceni....kuma ko Allah yasan kedin azzaluma ce,wannan zubar ruwan shi zai sake toshe kunnen duk wani da kike tunanin zai ceceki ko zai kawo miki dauki,duk da kuwa wannan ginin gidan naku dama kaman anyishi ne domin ni,yana riqe sirrin kowanne motsi yadda ya kamata". Ya fada yana kallon yanayin roofing na dakin yana sakin murmushi. "Nayi mamaki wai da kike tambayata abinda ya kawoni,bayan akwai basussuka na da yawa a kanki?". "Mashkur ka haukacene?,kasan gidan waye ka shigo?,gidan matar aure har tsakiyar dakin aurenta..... " Fara takowa yayi yana sake nufota yana dariya "Ina cikin gidan muhammad fu'ad jadda,the owner of jadda diamondchore resources.......sannan ke din sabreena ce,mata a wajensa.....bayanin yayi daidai?" Ya jefa mata tambayar yana dage mata dukka girarsa biyun bayan ya tsaya daga takowar da yakeyi. "Ko kina buqatar wani qarin bayanin?......kinaso ne na gaya miki da license dina na shigo gidan nan?,da license daga hannun wata mace mafi kusanci da me gidan?". Daukan tunaninta yayi ya luluqa wajen lalubar ma'anar abinda yake fada,da license daga hannun wata mace mafi kusa da me gidan?,wace kenan?. Kaman yasan abinda take tunani a kai yace "No dear......kada ki wahal da kanki wajen tunanin wace..... Ki bari na gama kashe qishirwata sosai sannan mu zauna mu tattauna..... I need you.....na azabtu da yadda asara biyu ta fadamin......babu ke ba kudina......come please" Ya furta yana kawo mata cafka. Batasan tana da tsananin zafin nama har haka ba sai data kufce masa ya kama iska. Sukabi hannunsa da kallo dukka su biyun shi da ita. Shi dariya ya saki yana jijjiga kai "Kada ki dauka kedin me sa'a ce ko da yaushe.......idan a wancan karon kin kubcemin...... Na rantse wannan karon baki isa ki kubuta ba,koda kuwa a gaban mijinki ne a yau sai na kashe qishirwar dake raina" Ya furta yana daga rigarsa,take ta hangi hancin bindiga daga aljihun trouser dinsa. Kaman an debo bulo an jibga mata haka taji wani matsanancin tashin hankali ya keto mata,bata gama sauke abinda ya taso mata ba ta ganshi ya taso mata yayo kanta gadan gadan. Wani irin qarfi ne yazo mata,ta tattara hijabin jikinta da batakai ga cireshi ba da kyau ta haura sofa bed din dake gabanta ta wuce tsakiyar gadon "Ka fita min a gida.... Ka fita tun ban tada security din gidan nan ba" Ta fada tana duban sashen da wayar girke take a dakin wadda zata baka daman kiran kowanne sashe na gidan. Ta shiga shock sosai sanda ta lura ya gutsire wayar gaba daya ya fasa kan,duka yaushe yayi hakan da ko alama bataji ba. Dariya ya saki yana cewa "Kinga abinda ya samu telephone din ko?....." Bata bari ya qarasa ba ta tattara dukkanin qarfinta ta kwarara ihu tana fadin "Wani ya taimakeni" Abinda ta dinga maimaitawa kenan har sai da taji maqoshinta yana wani suya da radadi. Dakatawa tayi hawaye suna cika idanunta,tana duban mashkur dake qyaqyata dariya. "Zan iya qara miki lokaci kici gaba da ihu......kiyita ihu har iya yadda kikeso". "Fuad!. ....fuad!!!!" Ta sake qwalawa kiran sunansa. Karo na farko da ta fara ambatar sunan nasa kenan. "Yana can yana bacci" Ya fada yana juyi kaman zai taka rawa "Na sakashi bacci,kuma bazai tashi yanzu ba,sai na gama hutawa da matarsa" Ya sake maimaitawa cikin yanayin nishadin da kana kallonsa zakayi imani yakai masa har qasan zuciyarsa nishadin da yake ciki. "Mashkur,........ka saurara haka,ya kamata kasan kuskure kake tafkawa ba qarami ba.......ketawa matar aure haddi mashkur?!" Ta furta a tsawace. Dariyar nishadi ya saki yana kallonta,ya kama button din rigarsa ta saman ya fara ballewa yana zareta ya yar. "Kada kiyi kaman bakisan komai ba.......kina tunanin yaune na farko dana fara kwanciya da matan aure?,na kwanta dasu har bansan adadi ba......kawai ke dince ta daban,kin kasa fita a raina......bazan miki qarya ba,koda na dandana yadda kike banajin zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da ke ba......shawara daya kawai zan baki,kada kiyimin gaddama.......ki bani kawai salin alin don na tabbatar kinsan komai,ba wani abu baqo a wajenki" Sasai kalamansa sukayi mata nauyi a qirji,ta tabbatar inda za'a tsaga jikinta ba za'a taras da jini ko digo ba saboda tsananin tsoro da fargici. Ranta yakai maqurar baci sanda taga yana yunqurin haurowa gadon "Har ka mutu mashkur ba zaka taba samun komai daga gareni ba.... Ko gawata tafi qarfinka mashkur bare gangar jikina a sanda numfashi yake busawa". "Well.....tunda kin zabi muje ta haka dake!" Da furucin da haurowarsa saman gadon duka lokaci guda suka faru. Wani tsalle tayi da zummar barin gadon,saidai kuma ya samu nasarar take qasan hijabinta da qafarsa ganin zata kufce masa,abinda ya sanyata data dira din bata sauka a daidai ba,hannunta ya daki side
Chapter 59 · 0% Book details