Sashe 25
A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sharadi na daban kafin ta barta ta gansu,wannan tunanin ya sanyata miqewa a nutse tana mamakin duka yau bata dauki wayarta bata kuma yi amfani da ita ba. Kai tsaye tasan inda ta aje wayar tata,can ta nufa,ta daga wajen da zummar dauka,saidai kuma wayar tace daukeni inda kika ajiyeni. Mamaki kadan ya kamata,amma sai ta share tana tunanin qila ta canza mata waje ne ta kuma manta inda ta ajjiyeta,don haka ta fara bincikawa guraren dake daura da nan ko a nan ta ajiye din. Guri hudu duka bataga wayar ba ba alamarta,ganin zata gajiyar da kanta saita ajiye wannan ta koma laluben wayarta ta asali data barta a handbag din da suka dawo da ita jiya dake ajiye saman mudubin nata tunda ta ajiye jakar. Kaf ta lalube jakar sannan ta zazzageta,saidai babu wayarta babu alamarta a ciki. Mamaki yadan sanyata ja da baya,nan ma zuciyarta ta soma ayyana mata wataqila itama ya canza mata waje ne,don haka sai ta fara jaye jayen lockers tana bincike dakin. Wasa wasa har closet dinta ta duba babu wasu alama na akwai wayoyin. A hankali ta dawo tana zamewa ta zauna daga qasan carpet din da aka qawata gaban sofa bed din tana maida numfashi. "Ya akayi haka?,me yake faruwa?,dukka wayoyinta babu ko guda daya?" Ji tayi sam ta kasa aminta ko ta samu nutsuwa,sai kawai ta fadada bincikenta har zuwa kitchen dining area waiko ta barsu a can,saidai babu komai kamar dai yadda ta gani a dakin. A parlor din ta zame ta zauna,tana jin wani shakka da kokwanto na shigarta. Kota wacce fuska bataga waje ko wani sarari da wani zai samu daman shigowa gida irin wannan ba.....me wasu irin madaukakan katangu da kuma gwabza gwabzan security irin wadannan ballantana tayi tunanin wani ya hauro ya shigo musu...... Da sauri ta zauna sosai tana qanqance idanunta sanda wani tunani ya fado mata. "Idan har haka ne shine kenan ya dauke wayoyin?,yaushe?,garin yaya?,a ina kuma ya samu damar aiwatar da hakan?" Tambayoyin dake danqare a kanta kenan data dinga juyasu. Idanunta ta maida tana duban sashen da stairs dinsa suke,zuciyarta na bugawa kadan kadan,tana jin kamar ta tashi ta haura ta sameshi a can,taji meye hujjarsa na daukar mata wayoyi,bayan hakan ba huruminta bane?. Bata fahimci cewa gidan ba kowa ba......ita daya ke rayuwa a cikinsa duk girmansa ba sai da sha daya na dare ta gota a idanunta. Sai a sannan taji wani irin tsoro ya soma mamayarta sanda zuciyarta ke bata hasashen ita daya ce qwallin qwal a gidan. Wani irin karyewa zuciyarta tayi,tsoro yana sake shigarta sanda take qudundune cikin duvet dinta. Bata taba kwana ita daya ba koda cikin dakinsu ballantana a gidansu gaba daya ba.....wanne irin azzalumi ne shi da zaya fita yabarta a gidan da yafi qarfin zaman mutum hudu ma yace ta kwana ta rayu ita kadai?.....ba wayar da zata kira wani ballanta taji sassauci......koda ta duba wayar girke dake parlor din da zummar ta sadata da security din da suke waje taji ko zata samu aron waya daga hannunsu cikin rashin sa'a ta samu an yanke sadarwarta,ba zata iya yin magana da kowa ba banda dakunan dake cikin gidan. Kanta ta cusa cikin pillow din tana jin yadda bugun zuciyarta ya qara tsananta sanda karen dake wani sashe daban na gidan ya tsananta haushinsa. Bata taba tunanin akwai halittar tsoro a qirjinta har haka ba sai yau.....ashe dukka jarumtar da take zaton tana da ita ba jarumta bace.....ko tace ta tsaya ne kadai ta bangaren saita maza daukan darasin rayuwa da sanin ciwon rasa wani abu da xukata suke tsananin so da qauna. Batasan ya akayi ba ta samu da qyar wani takurarren bacci yayi awon gaba da ita. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _ZAFAFABIYAR_ 26 Kwana daya kwana biyu haka awanni suka dinga juyawa da ita cikin gidan,cikin wani irin matsanancin shuru kewa da kuma kadaici. A hankali ta dinga jin wani matsanancin takura,ta yaya zata zauna irin haka ba waya ba gilmawar kowanne dan adam?,tv kuwa sam taqi ta kalleta bare ta gwada kunnata. Da farko ta dauka zata iya jurewa,amma sannu a hankali saita fahimci ashe mutum rahama ne a kusa da kai,koda kuwa ba wata mu'amala da zata hadaka dashi. Tayi dukka juriyar da zata iyayi sai taji haqurinta ya soma gazawa. Wani danqararren bacin rai ne yake cinta game dashi wanda qilan inda yabar mata wayar ma a wannan karon batajin akwai abinda zai mata shamaki daga kiransa ta zazzage masa abinda yake cikinta. Ta yaya ita din da ta kwashi shekara aqalla biyar zuwa shida,ba wata ranar banza da zata fito ta fadi bata fita ba.....yanzu kawai rana tsaka ta wayi gari da mummunan kulle irin wannan?. Ko a baya batata ji a ranta akwai wani lokaci da zayazo a sanyawa qafafunta irin wannan sasarin ba,ba lissafin aure kwata kwata cikin kanta shi ya sanya bata kawo yiwuwar afkuwar hakan a kanta ba koda sau daya. Ranar data cika kwana na hudu,tun qarfe goma na safe taji takai maqurar da ba zata iya jurewa ba. Sha daya da rabi daidai ta kammala shirinta cikin atamfa. Ta taka a hankali zuwa inda take da tabbacin ta ajiye kudinta data shigo dasu cikin gidan,ta bude locker din ta zura hannunta don debosu,don ta gama tsarawa kanta zata taka ta fita ta samu napep duk kuwa da cewa tasan area din kwata kwata yana da wahala kaga abun hawa na haya.....to amma ta gwammace tayi tattaki zuwa babban titinsu tayita jira cikin rana har ta samu abun hawan da zai kaita gida. Zuciyarta da tunaninta gaba daya yana kan taje ta binciki lafiyarsu huda.....kowanne dare dasu take kwana dasu kuma take tashi,suna cikin aminci ko kuwa aah?......da qyar ta iya jure wadannan kwanakin suka shude ba tare da tasan komai game dasu ba. Ta dauka yadda ta dokanta ta fita ne idanunta suke mata gizo sanda ta hangi babu ko burbushin kudi a wajen,amma data bude sosai sai taga gaskiya take gani.......ba komai a ciki kamar yadda ta gani da farko. Mamakinta ya ninku akan mamakinta na kwanaki hudun da suka shude........ta sulale tana sake zama a saman stool din dake kusa da ita. "Wai wa yake da alhakin aikata haka?" Ta sake tambayar kanta tana jin tantama akan tabbacin zargin farko da zuciyarta ta bata. Duk wani karsashi na fitar saita rasashi......yaushe ya samu damar shigar mata daki?,dame dame ya bincika mata?,me zaiyi da wayarta?,dame dame zai bibiya cikin wayar?. Wadannan tunanin su suka sakata a gaba,ta kasa tuna komai ko abinda ya dace tayi,har sai da agogo ya alamta mata sha biyu dai dai na rana. Cikin qarfafawa kai gwiwa ta koma toilet ta sake wanke fuskarta,ta dawo ta wuce closet ta dauki handbag da shoe da zai dace da shigarta sannan ta soma barin dakin tana jefa atm dinta a jaka da zummar idan ta fita ta samu wani guri ta cire kudi daga account dinta. Wannan ce ranar farko kuma karan farko data fito daga cikin gidan a yanayi irin wannan. Faffadar haraba yalwatacciya me wani irin tsari me jan hankali. Kusan gurare da yawa an qawatashi da koriyar ciyawa a maimakon tiles marbles ko concrete da akafi yawan amfani dashi. Sai wasu irin fararen stone da aka zuba a wasu daga cikin hanyoyin da zaka taka ka wuce zuwa haraba ta biyu. Idanunta suna iya gane nata wasu qofofi da babu qofa a jikinsu face wani irin design da aka musu wanda batasan ainihin inda zasu sadaka dashi ba. Sosai harabar ta qawatar da wani irin yanayi da zakayi tsammanin ba cikin qasata nigeria kake ba.....saidai wutar dake can qasan zuciyarta ta danne burgewar da wajen yayi mata,taci gaba da tafiya cikin confidence zuwa qofar gate din da take da tabbacin zata sadata da waje. Tsaye kawai tayi don bata fahimci ta inda zata ratsa ta wuce ba,sam qofar ba irin qofofin data saba gani bane. Gajiya tayi da tsaiwar ta kuma gaji da kallonta da tunanin ta inda zata fita din,don haka ta saka hannu ta soma knocking da tunanin zasu iya jinta. Tun tana knocking din a hankali har ta fahimci ba kowa ke jinta ba,ta qara dada qarfinsa saidai a banza don ba wani motsi da taji da zai bara hope din wani na kusa zaiji ya kuma budeta,wannan ya qara hasala mata zuciya,ko a kurkuku take bangaren muggan laifin kisa ko fashi da makami iya horon da za'ayi mata kenan,don haka ta sake maida kai wajen buga qofar da kyau ba tare da tunanin cewa babu me jinta ba. A hankali wani sashe kadan daga saman qofar ya zuge kanshi da kanshi. Fuskar jordan ta bayyana wannan karon sanye cikin uniform din daya zama kayan sawa ga duk wani ne aikin tsaro dake cikin gidan. "Good afternoon maa". Ya furta da wannan matsananciyar girmamawar da yake mata wadda ba abinda take sawa zuciyarta sai wani irin qarin takaicinsa. Fuskar jordan fuskace da ba zata manta da ita ba ko kadan "Open the door" Ta fada adan fusace tana kallonsa,tana jin kamar ta miqa hannu ta zabga masa mari. Cikin rusunawa da girmamawa kaman yadda ya saba ya fara mata magana da hausa "Am sorry maa......boss bai bada umarni ba,idan ba damuwa ko zaki kirashi kuyi magana tukunna?". Idanunta ta janye kawai daga kan jordan din bacin ranta yana ninkuwa,abinda yayi mata a wancan lokacin shi ya maimaita mata kenan?,waishin me yake daukan kansa ne shi?,don yana da kudi?,yana da dukiya shi yasa yake tunanin zaiyi duk abinda yaga dama?,zai taka wanda takeso a duk sanda yaso?,zai wulaqanta mutane sannan kuma ya kwana lafiya?. Ta ina zata nemeshi bayan babu ko waya guda daya a tare da ita?,ta ina zasuyi magana bayan ya yanke sadarwar gidan gaba daya?,koda ma komai yana nan a muhallinsa ta rantse ba zata kirashi ba. "Kawu ne ya jawo miki" Amsar data dawo cikin kanta kenan. Idan ma kira ne shine mutumin daya kamata ace ta kira,har yanzu tana ji a jikinta kan ta inda ake hawa ta nan ake sauka,kawun shine ya bada ita ya kuma saida mutuncinta.......don ta nata bangaren ba'a kan muhammad fu'ad bane farau shallakewa maza masu kudi da kuma hadari......don haka don shi kadai bazai