← Book details A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 60

Sashe 26

A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

zame mata matsala ba inda anbi karatun yadda ta saba. Har taji kamar ta sare,sai taga idan ta bari hakan ta kasance yasha da ita,don haka ta matsa bakin gate din "Can you barrow me your phone?". Ta tambayeshi tana kallonsa. Jinin jikinsa yasha,yadan kalleta yana kokwanto. Yaya zata rasa waya tana a gida irin wannan?. "Afwan madam.....amma me zakiyi da waya?" Idanunta da suke mata zafi ta lumshe "Zan kira uncle dina ne.....i lost my phone". Dan jim yayi kadan,sai kuma ya amsa mata yana sanya hannu a aljihu ya fiddo wayar ya miqa mata bayan ya sake bude glass din ya qara girma. Yadda yake bata wayar kamar tana a kurkuku ya sake matsa zuciyarta ya qara yawan adadin bacin ran da take ciki. Wani sashe daban na gidan ta koma ta zauna saman wasu rukunin kujeru da aka qawata cikin wata rumfar bamboo dake bada iska me kyau da sanyi. Da qyar ta iya hada lambobin kawun don ba haddacewa ta taba zama tayi ba.....saidai kawai kira na yau da gobe daya bata daman kallonsu daya bayan daya suka kuma zauna a kanta. Bugu biyu kawun ya daga da cikakkiyar sallamar data kusa sanyata jan tsaki "Kamar gaske" Ta fadi a ranta tana amsa sallamar tasa a daqile. "Wa nake ji kamar sabreena?" Ya fadi da annashuwa cikin muryarsa,zuciyars na bashi tabbacin lallai zama ya soma miqawa,wataqila wani alkhairinma ta bugo tayi masa "Nice" Ta amsashi a hankali "Kai madalla Allah.....ma sha Allah,amma fa naji dadin kiranki kin kyauta diyar albarka,dama inata zube kunne naji kiran naki......" "Eh gashi na kira......na kiraka ne kuma na gaya maka.......wannan mutumin daka saida masa dukka 'yan cina da mutuncina ya kamata ka kirashi ka bashi labarin haihuwata akayi bawai a baiwa aka ribatoni ba.......ka fada masa abinda ke tsakaninka dashi daban da abinda ke tsakanina dashi,bazan iya daukan dukka wannan izzar tasa da izgilancinsa ba......ina da 'yance kafin zuwansa zan kuma ci gaba da kasancewa me 'yanci a rayuwata.....don har yanzu babu d'a namijin da zai dinga ruling dina yadda yaga dama ba tare da naso haka ta kasance ba". "Kai jama'a.....waike wacce irin yarinya ce ne me butulci?,Allah yayi miki wannan babban gamo da katar din da miliyoyin mata ke fatan samu amma ki zauna kina shashanci?,yo Allah na tuba idan ranka ya dade baiyi mulki da izza ba meye zaiyi?,kudi ne dashi fa?,arziqi garai irin arziqin da gwamnati ma wani lokaci biyayya takeyi maka.......ina gani malam rufa'i?,to wallahi bada ni ba.....hasalima ni bamu taba waya dashi ba,dan uwansa kuwa farouqu bazan dauki sirrin gidan ma'aurata nakai masa ba Allah bazai la'anceni ba,in zaki nutsu kiyi biyayya ki tara abinda kika tara karki mana buqulu to,amma wannan jan kunnen bada ni ba.....wane mutum inji mutuwa,Allah baki da hankali sabreena" Har ya qare maganganun idanunta suna kulle saboda yadda yake mata magan da qarfi da hayaniya,uwa uba ita bataga dalilin dogon jawabinsa ba. "Kawu" Ta kirashi a nutse. "Yaushe su huda suka zama cikin kayan gado da har za'ayi rabonsu zuwa ga wata mace da basu hada alaqar komai dasu ba?". "Wata mace?,Allah na yarda dai da gaske akwai sauran qarancin nunar hankali a tare dake.......kina magana akan hajiya mariyah surukarki?,mutuniyar kirki me yawan alkhairi da son zumunci?,yo wannan kika fadi mummunar kalma a kanta aisai Allah ya tsine miki albarka.......ni baza'a zageta dani ba,sai anjima sabreena" Kafin ta ankara ya yanke wayar,abinda ya sanyata a razani ta maida dubanta kan fuskar wayar tana kallonta cikin mamaki. A wannan karon duk yadda taso tare kukan sai da hawaye ya sauko mata bayan ta maida wayar wa Jordan. Sai kawai ta soma tattaki da sassarfa tana komawa ciki cikin yankewar kowanne tsammani. A falo na biyu ta zube don ta gaza isa bedroom din. Wasu irin hawaye masu zafi suka fara gangaro mata. Me yasa rayuwa zata juye mata da zazzafan yanayi irin wannan dare daya?,yanayin da ko s mafarki bata taba tunanin zaya risketa ba?. Ya cika mugu na gaske,ya rufe mata kowacce qofa ko hanya da zata samu sassauci......me ya rage ita kuwa tsakaninta dashi banda itama tayi duk yadda zatayi tayi nesa dashi?,me ya rage banda ta aiwatar da nufin maamah a kansa don ya gwada shiga halin mulkin mallakawa d'an adam yaji idan hakan da dadi?. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _ZAFAFABIYAR_ 27
Chapter 26 · 0% Book details