← Book details A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 60

Sashe 13

A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sakemin irin wannan?" "Kiyi haquri" Ta fada kanta a qasa,saita janye kallonta daga kanta tana sake jan tsaki "Laila tashi ki kwashe kayan nan ki zuban a wardrobe". Sai sannan ta cire kanta ta kalli kayan "Kai.....gaskiya hajja sunyimin nauyi bazan iya ba.....saidai a barsu a nan,zuwa anjima idan na tashi na kwashesu daya bayan daya". Tsaki hajja din ta sake ja ta maida dubanta ga mansura din "Kwashesu kikai min wardrobe,kuma bance ki zauna ba bare ayimin bincike a daki". Itadai batace komai ba ta tsugunna ta kwashe ta wuce dasu. "Zaki ajiye wayar nan muyi magana ko sai na fasata?" Hajja tayi maganar da daga murya,abinda ya sanya laila kashe wayar ta ajiye agefe,sannan ta juyo wajen hajja "Gani" Sai data dire cup din hannunta sannan tace "Kaman yadda nasha gaya miki ina da plan ina da tanadi a kanki.....tanadina ba kowa bane face muhammad fu'ad jadda.....mamallakin jadda diamond chore resources.....dan qawata mariyah" "Ahhhhhh" Laila ta fada tana fidda idanu cikin tsananin mamaki da kuma gigita. Wani abune da bata taba kawoshi cikin kanta ba,hasalima batasan akwai qawance har haka tsakanin momynta da mahaifiyarsa ba "Wasa kikemin hajja?" Ta fada tana kallonta sosai gudun ganin samu da rashi "Na taba wasa irin wannan dake?" Maimakon ta amsa mata saita daka wani irin tsalle tayi kanta ra ruqunqumeta. "Wayyo Allah mamana......i love you so much mamana......you fulfill my dream" "Kinga shashasha zata karyani......da Allah zauna muyi magana dake don gidansu zaki koma da zama na wani dan lokaci" Ido ta sake watsowa waje,tana jin komai kaman cikin shirin film ko labarun hikaya "Serious?" "Ubanki" Ta fada tana watsa mata zagi da yatsu biyar,saita saki dariya ta koma tana zama din kamar yadda hajja ta umarta. Baki ta daga zata watsawa mansura kira sai gata ta fito "Yauwa saiki wuce ki tafi,ki rufen qofa.....ki gayawa madeena nan da minti talatin ta dafamin madara ta kawomin,wallahi kuma aka wuce haka sai ranta yayi mummunar baci". Kai a qasa ta amsa mata ta juya tana ficewa. Sai data fita din sannan ta maido hankalinta ga laila "Kina jina ko?" Sake duban lokaci tayi,sha biyu saura na rana. Tunda ta farka tayi wanka da sallolinta bataji motsin kowa ba,don hatta securityn dake aikin kula da gidan bakajin motsin kowa,sanin da sukayi cewa hayaniya da motsi me qarfi na daya daga cikin abinda boss din nasu bayaso. Uwa uba ma su dake first gate bata yadda na ciki kamarta zai iya jiyosu. Bawai yunwa takeji ba,amma a jikinta takejin ya kamata ta sawa cikinta koda ruwan dumi ne. Kaman ba zata fito din ba amma ta miqe,ta lalubi mayafi ta lullube jikinta sannan ta sanya plate shoe dinta na jiya ta fara nufar qofa ba tare da tasan takan gidan ba ko kuma daga inda zata fara ba. Rufaffen hallway din ta soma ratsawa,wanda aka qawatashi da wani irin wall led light na musamman,da wasu irin qananu masu haske da suka sake fidda ainihin kyan wajen. Tattausan runner carpet ne shimfide duka tsahon wajen tsakanin kowanne qofar daki zuwa na dan uwansa an qawatashi da wasu irin nature frames masu daukan hankali. Daga bangon dake facing naka kuma,babban console mirror ne da zai baka daman ganin kusan dukka jikinka har kusan cinyoyi. Akwai plants masu kyau data gani cikin flower vase masu wani irin daukan hankali,bata sani ba masu kyau ne ko ma decoration. Guri ne daya cika da hasken da koda allurarka idan ta fadi zaka iya tsugunawa ka dauka,ko ina fes da wani irin matsanancin tsaftar da babu qura ballantana ka saka ran samun wani abu waishi datti saman lafiyayyen marbles din dake lullube kuma shimfide a qasan wajen. Duk zuqar iska guda daya idan tayi da qamshi take kai mata har hanjinta,qamshin da sam bata da tabbacin daga ina yake fesowa ya karade kowacce iska dake kai kawo a wajen duk kuwa da a rufe hallway din yake. Idanunta kafe akan staircase din dake gabanta. Batasan ina bane bata kuma fatan sani,nan din inda aka ajiyeta ma kawai tana jin ya isheta harta kammala abinda zatayi tabar cikin rayuwarsu,fatanta daya shine idan ta isa staircase din ta samu wata qofar tsakanin hagu da dama cikin dan lugu biyu da take ganin alamunsa. Ajiyar zuciya ta sauke sanda take dab da bakin stair case din,akwai wasu qofofi hagu da dama,saidai ta daman tafi mata kama da qofar da zata sadaka da wani gurin. Solid wood door ne me qofar biyu data dace da kalan gidan gaba daya dake bata kalan gold and off white,dayan pivot door ne wanda tafi kyautata zaton wani gurin na daban zai sadaka dashi,don haka ta nufi hannun damanta,ta sanya hannu ta murda handle din ta bude qofan a hankali kamar me tsoron wani abu. Wani irin tsararren parlor ne da kana kallonsa zakasan ilimi hankali da dukiya duka sunyi amfani. Well designed parlor me wani irin sassanyan yanayi me jan hankali. Babban swarovski crystal chandelier din dake tsakiyar falon ce kawai a kunne,amma duka fitilun dake zagaye da falon a kashe suke,saidai duk da haka hakan bai hana fitar ainihin kyau da tsaruwar falon da aka qawata da kujerun qasar Italy. Kutsa kai taci gaba dayi cikin falon kamar me tsoron sautin takunta,tako ta ina tsarin gidan yana dada kwance mata kai. Wani irin tsari dake da matuqar sha'awa da daukan hankali. Idanunta suka fada daya sashen falon. Glass door ne da zai baka damar hangen wani guri da aka qawata da wani irin shuke shuke masu launika daban daban masu daukan hankali. Wajen yafi mata kama da qaramin lambun da zai taya mazaunin falon debe kewa. Ta sake wurga idonta.....ba wata qofar a nan data mata kama da qofar kitchen,sai wata qofar shigen qofar farko data bude. Ita ta nufa kai tsaye,tana jin yadda qafafunta suke nutsewa cikin lallausa Italian Versace carpet daya dace ta kowacce fuska da kalar tsarin falon. Steps hudu masu fadi ta soma cin karo dasu,wanda ta nan zata taka ta sauka cikin wani falon na daban da yasha banbam dana farko ta kowacce fuska. Furniture din ciki girma da tsari,saidai kusan komai nacan akwaishi anan,illa na wannan falon yafi na wancan yawa da girma. Rukunin kujeru biyu ya dauka saboda girmansa. Sabanin wancan falon,wannan tafkekiyar tv plasma din da tafi qarfin Wall wooden TV stand din aka girketa samanta ce a kunne. Saudi qur'an ce kunne,saidai kuma sautin karatun sam baya fita. Lullube kowanne bango yake da tsadaddun curtain masu wani irin kwarjini da haiba,kowanne maqale jikin Drapery hardware,abinda zai baka daman ganin qifofin da sukayi saura ta wajen banda yalwataccen dining area da aka yiwa ado na musamman da roman shade curtain da zai baka daman kallon wani sashe na kitchen da glass door ya rabasu. Qaramin tsaki taja tana janye kallonta daga kallon kowanne tsari na parlor din. Finally bayan ta gama duk bulayin ta samo kitchen din da qyar,don haka ta taka a nutse tana hawa steps din da zai sadata da dining din zuwa kitchen din. Sak tayi canma tana kallon kitchen din,don wata aljannar duniyar ce da bata san ta ina zata fara ba. Komai a kitchen din baqonta ne,ba wani abu da zatace ta masa farin sani idan ka debe kayan amfani na yau da kullum da kowanne kitchen ake samu. Ya qawatu sosai da custom cabinets da aka sarrafa da wani irin gogaggen katako datayi imani badai daga qasar nan ba,yabi sauran kayan cikin gidan yazo ne daga wata qasar daban. Tunaninta ya dawo da baya,shin yaushe duka suka samu wannan kudin?,a ina?,da har aka samu daman zuba mata wannan uwar dukiyar cikin gidan?. Anya kuwa bayan mutunci da kawun ya saida mata ba hada harda 'yancin jere ga kowacce diya budurwa ba?. Iya wannan tunanin ya sake sanyawa taji komai na gidan ya fice mata a rai,baya kuma burgeta ballantana taba haskenshi. Taja qafafunta da sukayi mata nauyi tana nufan gas glass stove din tana fatan ta kunnashi daidai kama kowanne. Sai data bata lokaci shi kansa wajen gane kansa sannan ta saki ajiyar zuciya. Taja da baya tana baza ido don hango inda zata samu koda ganyan shayi ne,don dama cimar bata wuce haka. Daga can ta hango wata qofar,ta taka zuwa wajen tana addu'ar Allah yasa ta samu abinda takeso,don duka ta gwada duba cabinets din bata samu komai ba aciki,da alama shi kam banda kayan kitchen din da aka jera ba'a taba komai ba. Cikin sa'a ta tadda yalwataccen guri da yafi mata kama da store saidai na musamnan. Don ba abinda yake zube a qasa hatta kuwa da buhunhuna da kwalaye,kusan duka wajen shima an masa kanta sosai kamar kanti ko shago,an saka komai a bangarensa daidai da kwalayen maggi kuwa. Daga gefe babbar freezer ce wadda batabi ta kanta ba,don ko sha'awar budewa bataji ba,to ta bude taga me?,ba wannan ne a gabanta ba. Bangaran spices na tea ta nufa,ta bude ta debi kowanne daidai yadda zai isheta,daga wannan ba abinda ta qara ta dawo ainihin kitchen din,ta bare tukunya daya,ta nufi sink ta kunna famfo ta debi ruwa,sannan ta dawo ta kunna gas stove din ta dora bayan ta zuba komai. Minti goma tsaf ya tafasa,ta soma duba mazubin da zata juye ta wuce dashi,don sam batason zamanta kitchen din. Tea set ne kala kala,ta rasa ma wanda zata dauka. Taja qaramin tsaki still,komai na gidan ya fiya fi'ili da feleqe,tunda ta tashi komai ma sai tasha wahala take laluboshi,iya yau kawai.....neman kitchen da dafa tea ya zame mata alaqaqai?,ina ga sauran rayuwarta cikin gidan. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_* 08187255862 _zafafabiyar_ Qarshe dai wani Wedgwood tea set din qasar chaina ta dauka ruwan sararin samaniya,ta juye duka ta zuba sugar a mazubin sugar din sannan ta dauka tray na set din cak tana wucewa ciki dashi. A yanzun tafi fahimtar hanyar da take komawa ba kamar dazu ba. Tabbas duk yadda takai gason ta kushe komai ta kasa,duk.yadda takeso komai kada ya burgeta a gidan hakan ya gagara,dole ta sallama saidai still zuciyarta na gaya mata "Allah yasa da kudin halal akayi komai" yarinya tunda dai kin fara mora ai magana ta qare). Bata tashi tunawa da personal wayan da ta bata ba sai data kusa kammala shan tea din. Qarar wayar ya Haifa mata da wata
Chapter 13 · 0% Book details