Sashe 52
A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daure da babban towel ta fito daga wanka,qaramin tana tsane doguwar sassalka sumarta dake a jiqe sharkaf da ruwa,alamu dake bada tabbacin wankesa tayi. Idanunta a lullumshe tana jin kalan nauyin da yayi mata saboda kukan da tasha a jiya. Duk da nauyin da zuciyarta tayi mata amma ta wani fannin sai take jinta sawai kamar wani nannauyan dutse dake danne da ita ne ya sauka. Tun daga jiyan data tabbatar ta miqasu hannun da bata haufi akan zasu cutu ko wani abu maras kyau zai samu riskarsu. Tana daga gaban madubin,kadan kadan tana hangen yadda iska take kada labulayen dakin,wata sassanyar iska me dadi kadan kadan tana ratsowa cikin dakin. Lumshe ido ta sakeyi sanda ta gama gyara gashinta ta matseshi cikin ponytail holder bayan ta lanqwasa jelarsa me tsaho sosai,fuskarta ta fito sosai,sai ta sake lumshe manyan idanunta da suka rusuna sosai. Zuciyarta ciwo takeyi idan ta tuna da tuhumar da yayi mata jiyan,tana jin wani zafi cikin qirjinta duk sanda kalmar "Wajen wa kika je?" Ta dawo mata a kunnenta "Me kikayi?" Tana sake sakata jin zuciyarta na matsew a qirjinta. Vibration din da taji daga gefanta shi ya ware zaren tunanin dake qulluwa cikin kanta. Maida dubanta tayi wajen,wayar huda data karba ce wadda ta sakawa charge tun da asuba,bayan wayar ta cika kuma sai ta kunna kanta da kanta kamar yadda tsarin wayar yake. Sunan MAAMAH data gani ya isheta bayanin wacece,wani matsiyacin tsaki taja tana janye idanunta daga kan wayar,sannan ta juya tana wucewa closet dinta don neman kayan da zata saka. Idan ta tuna abinda d'anta da ita sukayi mata,sai taji kanta ya cika da shawarwarin hanyoyin da zata dauki mummunar fansa a kansu kafin ta tattare tabar rayuwarsu. Duk da cewa nashi me sauqi ne,don baiyi yunqurin taba mata kowa nata ba,saidai ya taba mata zuciyarta da munanan kalmomin da koda tayi nesa da rayuwarsa bata jin zata iya mancesu. Har zuwa yanzu da take wannan tunanin ta rasa wanne kalar abu ya kamata ta yiwa maamah?. Abu daya tayi ittifaqi akai shine......tabbas zata banbance mata tsakanin aya da tsakuwa......zata kuma shayar da ita mafi girman mamaki. Tabbas inda tana da ra'ayin d'anta......lallai da zata mallakeshi a gaban idanunta ne,mallakar da babu boka babu malam.......mallaka ta ruwan sanyin da sai ta gwammace bata sanyata a shirmen shirinta ba. Har ta ciro kayan ta dawo ta shirya cikin Palazzo da blouse data kasance cif cif jikinta don bata buqatar kaya masu nauyi kiran bai daina shigowa ba,ta kammala ta feshe jikinta da turare . Scarf ta sanyawa kanta sannan ta taka a hankali tana isa inda wayar take sanda take dab da tsinkewa. Stool taja ta zauna bayan ta daga kiran ta sakashi a handfree ta kuma ajiye saman mirror table din tana tattara hankalinta akai. "Dawa nake magana?" Abinda ya fara fita kenan daga bakin maamah da wani yanayi na zaquwa da son jin wayar a hannun wa take?. Idonta ta lumshe sannan ta bude "Gaggawar ta meye?,kina tunanin wayar huda zata kasance a hannun wani qato ne?,ko a hannun wata sabanin halastacciyar 'yar uwarta data shirya sadaukar da tata rayuwar saboda tasu?". Maganar ta kama zuciyar maamah sosai,ta kuma saukar mata da matsananciyar fargabar data bata tabbacin KOMAI YA QARE saidai a sake sabon zubi da lale. "Naga alamar hakan......kin kuma yi qoqarin sadaukar da rayuwarki ma 'yan uwanki.....ni shaida ce,amma inaso kisan wani abu guda.......kina wasa da baqin kumurcin maciji ne daya shirya dukka dafinsa da xummar harbi ga duk wanda yabi ta hanyarsa" Wani dan murmushi ta sakarwa maamah din tana murza hannuwanta,har yanzu tana jin bata gama dawowa ainihin sabreen dinta ta asali ba......amma kuma da alama komai yana bisa hanyar saituwa "Shi wannan macijin.....idan har yayi sake halittar data fishi sanin kogon da yake kwana yake kuma tunqaho dashi.......tabbas akwai yiwuwar a cimmasa har inda yake......a kuma sanyashi ya yanke wannan kan dake dauke da dafin da kansa da kansa ba tare da yasan hakan ta faru ba....." "Ke dakata qaramar alhaki!" Maamah ta furta bayan dukkan haqurinta ya gaza da yadda yarinyar dake qarqashin igiyar auren d'anta ke iya maida mata magana me zafi haka kanta tsaye......ba shayi ba fargaba,yarinyar da a haife dukka cikin 'ya'yanta ba sa'anta. "Shshshsh....." Sabreen ta fada tana dora yatsanta akan lips tamkar maamah na zaune a gabanta. "Meye na saurin fusata haka?.....ina cewa abun baiyi zafi har haka ba?" Ta furta da alamun murmushi cikin muryarta. "Yaro man kaza......yaro baisan wuta ba sai ya taka..." "Your royal highness......har yanzu bansan meye dalilin wadannan zafafan kiraye kirayen ba da safennan". Iya maqura a rainin hankali maamah tana jin sabreen tayi mata shi,ta dinga qoqarin tausa kanta da daidaita kanta kada yarinyar ta tunzurata furta abinda batayi niyya ba. "Yaro yaro ne.......sabreena......kina da masaniyar cewa nice na tsugunna na haifi fuad?" Dan murmusawa tayi kadan sannan tace "Haka naji labari!" "Amma kina da yaqinin ni na daukoki ko kawoki cikin gidan na maidaki sunan matarsa?.......idan naso qasa da awa biyu rak! Zaki rasa wannan damar?" . Qaramar dariya ta saki ma maamah din,ta gyara zamanta sosai tana kallon kanta a madubi. A yau hirar nishadi take bata a maimakon razani da take samu a kwanakin baya da suka shude. "Kina zaton kina da wani makami da zaki iya fiddani daga gidan yaron naki?........kiyi haquri da abinda zance......amma ko shaidan a yanzu bai isa ya fiddani daga gidan yaron naki da kike tutiya ba........bana son danki ko kadan bazan kuma taba sonshi ba......amma yadda kika sakoni cikin rayuwarku......kika maidani matarsa da qarfin qwanji dana kudi.......to haka fitata daga gidansa da rayuwarku zata kasande bisa zabin kaina a kuma duk sanda nayi niyya......so kibi a hankali,bawai sonshi nake ba.....infact ma baiyimin ba.......amma bazan fita daga rayuwarku ba har sai sanda nayi niyya" "Qarya kike....baki isa ba!" "Dama bance na isa ba......amma zan gwada saiki tayani tabbatarwa...." "Kina kirawa kanki ruwa!,zaki iya rasa rayuwarki ta dalilin haka fa!" "Bari na fara raba naki d'an da rayuwarsa tukunna ki fara ganin kalar wannan baqin cikin kafin ki aiwatar a kaina......zan shayar dashi ruwan guba a ruwan shayinsa na yanzu a maimakon tsubbace tsubbacenki....." Tana kaiwa nan ta kashe kiran tana ma kashe wayar gaba daya. Murmushi ta dinga yiwa kanta a madubi,hirar ta sanya mata nishadi sosai,ko ba komai ta dasa mata tsoro da fargici tabbas na mintunan data ambata. Da gasken haka shine ya faru. Wani irin gumi ya fara tsatstsafowa maamah da wani irin kalar tashin hankali. Zuwa yanzu bata da tabbas akan yarinyar.......tana ji a jikinta zata iya aikata komai da tace din. Kasa zama tayi,jikinta yana rawa ta soma lalubar layin fu'ad tanason gargadarsa akan ya kaucewa komai da zai fito a yanzu daga hannun yarinyar. Kira kusan goma tayi masa a jere saidai ba wanda ya daga,abinda ya sake tsananta tashin hankalinta kenan,ta dinga duban agogo tana qirga mitunan da yarinyar ta kwasa mata. Daidai lokacin ma shi ya jima a office. Ayyukane da yawa a gabansa da suka hade masa saboda jiya bai samu yin komai ba a office din yayi baqi da suka tsaidashi har zuwa dare. Daga jiyan zuwa yau komai zaiyi yana yinsa ne cikin wani irin fushi da zafin ran da hatta saddiq ya fahimci akwai abinda ke damunsa,kuma tabbas ranshi a bace yake. Ture file din gabansa yayi yana jan wani mugun tsaki. A duk sanda ya tuna ko abun ya fado masa a rai sai yaji wani mugun bacin rai yana lullubeshi. Tashi yayi daga kan ainihin kujerarsa yana takawa a nutse,yasa hannunsa yana sassauta tie din dake wuyansa cikin wani irin yanayi da yakejin kamar numfashin da yake shaqa yana masa kadan. "Why i cares so much?" Ya motsa labbansa yana furtawa da wani irin zafi. Ba kasafai yake sanya kulawarsa ko damuwarsa akan komai ba sai abinda yake da muhimmanci a rayuwarsa. Ya tabbatar a karan kansa she's nothing to him amma me yasa abun yake masa zafi "Igiyar aurena" Abinda yake da tabbacin shine dalilin tsaiwar abun a ransa. Sai daya sassauta tie din hade da belt din suspenders din jikinsa,sannan ya jsa ga dispenser dinsa ya tsiyayi ruwan sanyi ya rage sanyinsa ta hanyar zuba ruwan zafi kadan akai,sannan ya koma saman recliner chair din dake gefe wadda aka ajeta don gajeran hutu irin wannan ya zauna akai. Kadan ya samu sassauci sanda yasha ruwan,ya dire cup din idanunsa suna sauka kan wayarsa dake haske. Da farko ya share yana tsammanin fareeda ce data zama kaman wata mahaukaciya. Kusan kullum cikin canza layin da zata kirashi dashi gudun kada yaqi dauka. Layinsa nada wani tsari na hana baqin numbers shigo masa amma nata kiran ya tsallake wannan shingen bai kuma san dalili ba. Sabanin mamakinsa sai yaga maamah. Baya iya qin daga wayarta komai runtsi,duk da daga ita har anni zai wahala su kirashi a irin wannan lokacin,sai ya jawo wayar ya daga yana sanyata a kunnensa. "Kana ina?" Abinda ta fara tambaya kenan tana qoqarin daidaita muryarta "Ina office.....wani abu ya faru?" Ya tambayeta a mamakance "Daga yau wannan yarinyar......." Sai kuma ta dakata saboda wani qaqqarfan gargadi da aka watso mata daga can qasan zuciyarta. Dan jim tayi shima sai yaci gaba da sauraronta baice komai ba "Shikenan,ka kula dai da kyau" Ta yanke tunaninsu su duka biyun da fadin haka. Wani haushi ya cikata bayan ta aje wayar,ita yarinyar zatayi wa wasa da tunani irin wannan?,tabbas idan har ta bari yarinyar ta qara kwanaki uku a gidanma.......bata amsa sunan mariya ba. *_to masu karatu......me maamah zatayi da zai saka auren sabreen qarewa cikin kwanaki uku?.....wanne qwarin gwiwa ko tabbaci sabreen ke dashi wanda yasa taci alwashi ko shaidan bai isa ya kashe mata aure ba?.....muje zuwa jama'a,WANNAN ALQALAMIN NA HUGUMA ZAZZAFA NE_* *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Daga sumrah dan jundub RA,yace manzon Allah S A W ya kasance yana nemawa mumunai maza da mata gafara a kowacce juma'a_ _harda ni dake da kikazo a wannan zamanin kin shiga ciki,LALLAI HASARA DA TABEWA TA TABBATA GA DUK RUHIN DA BAISON ANNABI,ALLAH KA DAUKI RUYUKANMU RUHINMU YANA CIKE DA MATSANANCIN SONSA S A W_ Sai data fara lalubar number da take da muradin yin magana da ita sannan zuciyarta taci gaba da