← Book details A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 60

Sashe 54

A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shuru ne ya biyo baya duk da wayar tana riqe a kunnenta. Dukka bayanan zuwaira ta gama saurara wadanda suka gama bata tabbacin lallai da gaske yaran sunyi nisan da ba wanda zaice ga inda suke......uwa uba kuma yarinyar tana ci gaba da harkokin gabanta hankali kwance kamar ba wani qalubale a gabanta. "Ni kaina yanzu komai na taba ko nace zanyi mata dakatar dani takeyi,waccar munafukar me aikin da ameena ta kawo mata yanzu da ita takeyi,munafuka me shegen iyayi da bariki,idan kikaga yadda takeyi mata zaki rantse da Allah sabreena ce babba ba ita ba". Wani tattauran yawu maamah ta hadiye,tsananin bacin rai yana sake cikata "Ki saurara,ki sanya dukka kunnuwanki da hankalinki dama idanunki kan gidan......kada kice komai,kuma kada kiyi komai,akwai gagarumin al'amari da zai faru cikin gidan.....abu daya nakeso kiyimin,ki kasance me bibiyar diddiqi bayan faruwar lamarin" Abinda maamah ta gaya mata kenam ta kuma yanke kiran. Bin wayar tayi da kallo......har a sannan tanaji a ranta muddin tabar sabreen din taci galabar ci gaba da rayuwa tana shan inuwa da arziqin danta lalallai ba shakka bata cika mariya. Shekaru da gwagwarmar rayuwa da gogayya da tayi da kalar mata daban daban bai amfaneta da komai ba.....shekarun data kwashe ma a duniya basuyi mata amfanin komai ba,dole ta fiddota daga gidan......wannan shine zai bata damar yin walagigi da rayuwarta da kuma d'aid'aita rayuwarta kamar yadda ta d'ai d'aita mata burinta. Qarfe daya da rabi na rana driver din hajja ya faka motarsu qarqashin muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci. Koda ya tsaida motar ya kuma kasheta amma hakan bai sanya hajja fitowa daga cikin motar ba. Da idanu take bin kowanne sashe na ginin gidan da kallo tamkar yanzu ta fara ganinsa. Saidai sam a badini ba wannan bane damuwarta ba......ba kuma shi take kallo ba. Tana nazarin yadda ALKHAIRI ya juye izuwa SHARRI,ta gama tura mota tsaf tana shirin buleta da balbalin hayaqi maras dadin shaqa?,hayaqi mafi cutarwa cikin qofofin hanci da kwanyarta?.. Wata gauruwar ajiyar zuciya ta sauke,sannan ta balle murfin motar yau da kanta tana fitowa,sabanin a baya da sai driver ya fito da kansa ya bude mata sannan ta fito. Gyara yafen mayafinta tayi,kanta tsaye kuma take takawa zuwa hanyar da zata sadar da ita da ainihin cikin gidan. Duk taku daya idan tayi la'anar maamah take cikin ranta,tana ji a jiki ta jefeta a wata kalar musiba da batasan ranar fitarsu ba. Zuciyarta tana mata wani qunci da ita kanta batasan iya adadinsa ba......amma wani sashen na zuciyartata yana sake jaddada mata "Fushi ba naki bane.....nasara bata masu gaggawa ko saurin fushi bace!" Wannan shine abinda yaketa mata burki take hadiyewa da qyar. A jiya da qyar bacci barawo ya dauketa,cikin fargaba da tsoron fitar dukkanin sirrinsu daga bakin laila..... Yanayin aikin bokansu dabanne,a aikin da aka tanadarwa fu'ad harda na rariyar baki,wanda baida wani sirri na kansa sai abinda maamah ta buqaci ya sirranta,muddin maganin yayi tasiri a jikin laila kamar yadda aka tsara.....hakan yana nufin duk wani sirri nata yanzu a tafin hannun mariya yake?. Wannan tunanin ya hana mata cikakken bacci da safe,ta dinga qididdiga da lissafin wucewar sa'o'i don ta samu ta fito zuwa gidan mariyan. Tanaso taga yanayin fuskarta,abinda zai nuna shine zai zame mata amsa na abinda take zato da zargi. Duk da cewa na tsuburi ya mata alqawarin ba abinda laila zata iya gayawa maamah.....to amma tasan aikin bokansu daban yake dana kowanne boka. Sau daya tak! Yake maka aiki.....idan har yayi maka na biyu to tabbas ka taki sa'a,uwa uba yawan yawan ayyukansa basu da makari.....shi yasa ta jima tana murza zaren rayuwarta ta kowanne fanni.....a yanzu kuma bata fatan wata matsala tazo mata ta wannan fuskar. Idanunta akan parlor din maamah.....falon da kullum maamah din ke kusheshi da ganin tsadar kayan adon ciki bai kama qafar na gidan alhaji hamza ba.....Parlor din da ita kuma hajja harira kullum kwanan duniya ta daga kai ta kalleshi sai kishin zamowarsa mallakar mariya ya baibaye zuciyarta da wata irin hassada me tsananin qarfi. Iya bariki da qwarewa wajen boyewa koma waye yanayin da kake ciki ya sanya maamah din bata taba fahimtar komai ba. Takun da taji ana fitowa daga kitchen ya sanyata waiwayawa cikin tsammanin daya daga cikin masu aikin gidanne wadanda su zasu yiwa maamah maganar ta iso tana son ganawa da ita. Amma kuma sabanin hakan,laila ta gani a gaba,dauke da kwando cike da warmers kala kala,saman rigar jikinta kuma apron ce a daure. "Laila?!" Ta kira sunanta cikin qaraji da wani kalar madaukakin mamaki tana takawa da hanzari don isa gabanta. "Sannu da zuwa hajja" Lailan ta furta fuskarta shimfide da murmushi dake nuna ba wani abu da takejin ba daidai bane "Bari na ajewa maamah abincinta nazo mu gaisa" Ta furta tana wucewa dining din. A nutse ta shirya komai.....kamar ba lailanta diyar gata ba,lailan da idan taci abinci ko kwanon da taci abincin batasan ta janyeshi ba......lailan da saidai tana mimmiqe saman sofa ko gado ta zabi abinda take da sha'awar ci.....wannan lailan itace yau a kitchen da rigar 'yan aiki?. Sanda ta kammala shiryawar saita dago tana murmushi,suka hada idanu da hajjan tace "Ina wuni?,na kira miki maamah din?,Allah yasa bata kwanta bacci ba don tace ko waye yazo kada a tasheta" "Gani nan laila baccin baizo ba....kun gama ne?" Maamah dake saukowa daga stairs din ta fada. Tare suka daga kai suna dubanta,sanye take da applique lace purple color da ya dan ciza kadan,dinkin doguwar riga da aka qawatata da wani irin dinki me daukan hankali. Shigar tabi jikinta....wadda ke bayyanar da zallar izzarta da isarta. "Kun gama laila?" Kai ta shiga gyadawa kaman mara hankali da sauri "Mun gama maamah ko akwai wani abun?". Ta fada a rusune. Murmushi maamah ta saki tana dafa kafadarta "Amma dai yau kin koyi yadda ake dambun gargajiya da kuma liver salad ko?". Murmushi ta saki kaman wata shashasha "Sosai ma maamah.....ai kin taimaken na gode sosai". Ta fada tana rusunawa a wajen. "Shikenan,yanzun zaki iya yin wanka,idan kin gama kiyi zamanki a daki kada ka fito yanzu" "To maamah" Ta amsa mata a ladabce tana juyawa ba tare data dubi ko bangaren da hajja take tsaye ba. Idanu suka hada da hajjan,wata tayi wata irin mutuwar tsaye. Gefe guda kuma taci gaba daya tamkar qwaqwalwarta ta daina aiki ne gaba daya. Wani qaramin shu'umin murmushi maamah ta saki,ta juya da hanzari bangare da laila ke tafiya "Au.....nikam nace kin gaida mamanki kuwa?" Kai ta girgiza tana fadin "Bakice ba ai". Fuska kadan maamah ta bata "Haba ke kuwa auta.....yarinyar kirki,zo ku gaisa mana....wataqila sanda zata tafi ai baki fito ba". Dawowa tayi ta rusuna har qasa tana gaida hajjan abinda bai taba faruwa ba kenan tsahon rayuwarta. Da fari idanuwa kawai hajjan ta saki tana kallon lailan,har sai da taji lailan ta maimaita gaisuwar sannan ta duqa tana dagota daga tsugunnon da tayi "Ki dauko mayafinki kizo mu tafi gida" Ta fada muryarta na rawa amma tana qoqarin danne rauninta don bata fatan maamah din ta gani. Kai ta girgiza tana duban maamah wadda tayi kaman batasan abinda ke faruwa ba,tana laluben wajen zama hankalinta akan fuskar wayarta "Nafison nan hajja.....ni ki barni a nan" Ta fada tana zamewa daga jikin maamah din ta wuce abinta hankalinta kwance zuwa hanyar dakin da aka bata. "Bismillah.......zauna mana surukata" Maamah ta fada fuskarta a sake. Kalmar suruka din da maamah ta fadi shine ya sanya hajja jin wani abu tamkar wutar lantarki ta fusgeta. Cikin qasa da minti guda gumi ya fara tsatsatsafo mata ta kowacce kafar gashi ta jikinta. "Atika!" Maamah ta qwalawa me aikinta kira,wanda cikin qasa da minti daya ta bayyana,sanin da sukayi mata batason ta kiraka ka samu jinkirin zuwa. "Dauki remote ki kunnawa surukata A.c,karki saka da yawa kada kuma ta saukar mata da zazzabi" "To hajiya" Atika ta fada da rawar jiki tana me aiwatar da abinda maamah ta umarceta. Zagayawa kawai kalmar takeyi cikin kunnuwan hajja.....indai har kalmar surukuta zata fita daga bakin maamah a wannan yanayin,lallai ne ba abinda bata sani ba kenan. "Ki maida hankalinki jikinki hajja......har mariya ce zata firgitaki har haka?". Wani sashe na zuciyarta ya bata qwarin gwiwa har ta samu qarfin halin tattara 'yar nutsuwar jikinta tana neman wajen zama gami da fuskantar maamah. "Mariya......zuwa nayi na duba lafiyar laila.....ya kuka tashi?". Murmushin nan dai ta kuma saki,sannan ta ajiye wayarta a gefe tana bada hankalinta gaba daya a kan hajja "Laila tana lafiya......kuma zata ci gaba da kasancewa lafiya sumul a hannuna......kinsan na iya riqon 'ya'yan jama'a" Ta fada hankalinta kwance. Murmushin qarfin hali hajja ta saki,sannan ta jinjina kai "Ai na sani mariya......mun tashi lafiya?" "Lafiyarmu sumul qalau hajja....." Daga nan ta fada nazarin da wacce kalma zata tunkareta. Idanunta ta daga tana duban maamah. "Muna magana jiya sai kuma Kira ya yanke....." "Eh wannan case din na gama solving nasa,saura fitar result" "Zancanmu fa kan laila da fu'ad?" Hajja ta jefa mata tambayar kai tsaye,duk kuwa da cewa ita kanta me bawa wani amsa ce.....saidai tanaso takai mariya inda take buqatar aje. Buda baki maamah tayi da nufin cewa wani abu......amma sallamar jarma daya daga cikin masu gadin gidan yayi sallama daga can bakin qofar falon. "Malam jarma ya akayi?" Maamah ta buqata sani sanda yake duqewa a wajen "Baqi gareki hajiya......ban sani ba zasu iya qarasowa ko a maidasu?". Fuskarta da dan mamaki take dubansa "Baqi kuma?,daga ina?" "Diyar ambassador Khaled mustapha ce,haka tace a gaya miki". Wani madaukakin mamaki ya cika maamah din,ba ita kadai ba,hatta da hajja sunan yaja hankalinta qwarai da gaske. Miqewa maamah din tayi tsaye tana dubansa "Maza ayi mata izini ta shigo......na tabbatar koma meye ya kawota nan,silar haihuwar ALKHAIRI ne fu'ad" Ta furta tana jin wani irin alfahari da haihuwarsa fiye da kowanne lokaci. Uwa uba tana yine da biyu,don ta tabbatar gaba daya hankalin hajja yana kan abinda yake faruwa. Sanye take da wani matsiyacin yadi da aka narkar da kudade masu nauyi kafin siyansa da yagalgalashi,aka kuma yi masa dinkin fitted gown data zauna a jikin laila......kai kace a jikinta aka dinkashi. Yadda dinkin ya zauna mata a jikinta.....hatta da dagawar numfashi daga cikinta da qirjinta kana ganin gudanarsa. Ba mayafi a jikinta,sai dankwalin
Chapter 54 · 0% Book details