← Book details A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 60

Sashe 20

A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dukkaninsu haushinsu takeji. Bataga meye dalilin da zai zube qatti irin wadannan suna kewaye dashi ba kamar tsohon barawo ko wanda yaci kayan wani ba(a iya nata sanin na iya tsaron daya zama dole me harka irin nashi ace ya samu),me yasa bazaiyi rayuwa normal irin ta mutane ba?,da wannan kalar tasa rayuwar kenan itama yakeso ya tursasata ta zama haka?,tayi rayuwa irin nashi?,bazai yiwu ba kuwa. Daidaita zamanta tayi sannan aka maida murfin motar aka rufe mata,sai motar ta dauki shuru sai sassanyan qamshinsa daya danne nata,har ya zamana duk wani numfashi da zata shaqa tare da qamshin nasa yake zuwar mata hunhunta. Tsaki ta saki a boye yadda bazai ji ba,ta maida kanta daya window din da take zaune daura dashi. Batasan sun fara tafiya ba sai da taga motar ta fara sulalawa tana nufar makeken gate din gidan suna gilma shukokin da aka qawata wajen dasu. Basuyi nisa ba kira ya shigo masa,wanda shi ya zame masa abokin tafiya. Duka maganganun cikin harshen turanci yake yinsu da wani irin accent dake nuna zallar qwarewa gami da gogewa a yaren. Kusan fin rabin maganganun nasa ba wani fahimtarsu takeyi ba,don zuciyarta tayi nisa da wani tunani na daban. Ta wani bangaren kuma yadda yake lanqwasa harshensa ba kowanne word take ganewa ba a matsayin karatunta na wadda ya dakata daga aji biyar biyu na babbar secondary wato senior secondary school. Sanda motarsu ke qoqarin cusa kai ta cikin babbar gate din dake da wani irin girma da kuma jan hankali,a sannan ne ya katse wayar ba kuma don ya gama ba. Ya kashe wayar gaba daya tana kallonsa ta gefen idanu,ya zurata cikin wani dan abu daya matsa ya fito ya saka wayar ya koma ciki. Adan qaramin zamansu na mintuna ta karanci abubuwa daban daban tattare dashi,kusan kaman komai nasa na dabanne kuma daban yake,saita tabe baki sanda suka isa babban parking lot na alfarma da gidan ya mallaka. Qasa tayi da kanta tana jan mayafin data lullube kanta dashi sanda take hangar wasu mata suna bullowa daga wata qofa da tafi kusa da parking lot din,kafin takai gayin komai amna ta bayyana ta kama murfin tana budewa,abinda ya bata daman jin maganganunsu. Muryar amna ta fara ji "Inna uwaisha......ga addan namu.......ku fito mana da ita a hankali" Ta qarasa fada tana qaramar dariyar dake nuna zallar farincikinta "Kinyi qoqari auta sannu.......kin gama naki" Wadda aka kira da uwaisha ta fadi tana matsowa gaban motar "Kamar gaske" Sautin muryarsa ta fita a hankali ya furta sanda kan sabreen ke qasa tana jin wani fargaba haka kawai na haduwa da mutanen da batasan su kuma meye nasu kalar halin ba,sunan auta da taji an ambata sai ya sanya duka tsigar jikinta ya tashi,haneefa da tun da safe take kokawa da tunaninta ta fado mata.....ko yaya ta wuni?. "Zallar karamci da girmamawa da mutuntawa muke gabatar miki" Abinda inna uwaisha ta fada kenan kamar tasan abinda sabreen ke wassafawa qasan zuciyarta. Miqa mata hannu inna uwaishan tayi tana fadin "Sauko a hankali nayi miki jagora zuwa ciki,ki shirya don kowa na dokin jiranki". Bata musa ba ta sakawa inna uwaishan hannunta "Fatabarakallahu ahsanul kaliqeeen......da iya lallen nan ma kawai an tashi kaina yallabai". Inna uwaishan ta fada tana dariya dariya idanunta akan muhammad fu'ad dake qoqarin ficewa a motar sannan ta maida dubanta ga amna data dage mata gira alamun Yes. Inna uwaisha na daya daga cikin makusantan anni da suka daukeshi tamkar d'a,duk da cewa tana da jika qwaya daya amma idan kaga suna raha da amna saika dauka yaya ce da qanwarta,hakanan suma ta daukesu duka mazan gidan. Bai iya cewa komai ba,sai dan motsawa da labbansa sukayi alamun murmushin dole kawai ya sanya qafafunsa ya fice daga motar. Kunnuwanta kawai ke iya jin surutansu amma idanunta suna a rufe. Batasan ina suke nufa ba saidai idanunta na iya kallon lullubabban luxury marbles din dake shimfide a wasu sassan na gidan,a haka taji sun isa wani daki da a nan inna uwaisha tace da ita "Fell free sabreen.....ki shirya amna zata tsaya dake,idan kun kammala zan dawo mu wuce wajen taron,kowa ke yake jira". Kai ta gyada a hankali,cikin ranta kuma tana zancan zucin wanne shirin kuma zata sakeyi bayan na jikinta. Sanda amna ta gabatar mata da komai na shirin shuru kawai tayi tana bin kayan da kallo......shin da saninsu wanne irin aure ne akayi suke wahal da kansu haka da kashe kudade da hidima?,ko kuwa kallo kawai sukewa abun irin duban bangon littafi ga idanuwan da basusan meye a cikinsa ba. Wata lafiyayyar Moroccan gown dake da wani irin ado na daukan hankali......saidai kuma duk da adonnan nata sam bata da nauyi ko kadan. Hade take da wani irin hijab dan qarami da yafi mata kama da na Indonesia ko Malaysia.....a ciki batasan wanne ne ba. Komai na kayan fari ne qal da wani irin haske me daukan hankali. Ita kanta bayan ta gama shiryawa batasan lokacin data dauka tana kallon kanta ba,sai take ganin kamar ba ita ba.....duk da kusan komai ma yana zuwa mata ne da wani irin ba zata da bata taba zato ko kawowa cikin rayuwarta ba. Amna ce ta fara shigowa wadda fiye da dazun a yanzunma ta susuce wajen yabawa sabreen din. "Inna Allah kwanan nan hamma zai manta da wani gold da Diamond" "Maza dai ya jiki" Inna uwaisha ta fada tana riqe hannun sabreen suna nufar qofar fita. Suna shiga wajen tasan sun iso,duk da kusan kowa na zaune a nutse ana sauraren jawabi daga bakin malamai. "Muna yiwa amarya barka da shigowa". Maganar data dauki amsa kuwa cikin hall din,ta kuma bawa maamah damar fara gyarawa tsaf don bayyanar da kanta a wajen. Ringing biyu wayar tayi ya daga yana sakata a kunnensa "Ya kamata ka qaraso wajen walimar fa.....akwai mutanen da zaku gaisa dasu" "Bana kusa" "Kaman yaya?" Farouq ya tambayeshi a mamakance "Eh.....kaman yadda kaji bana kusa,uzuri ya kamani nadan fita" "Why.....you know......" "Anni zata fahimceni idanma kai baka fahimta ba.....sai na dawo" Ya amsa masa yana katse wayar ya maidata ya ajiye. Shi a yanzun kasuwancinsa shine abinda yafi damunsa shine kuma gaba da komai,bai takurawa kowa ya matsawa kowa ba,don hatta da saddiq daya Kamata ace a yanxun suna tare suna duba al'amuran da suka taso musu bai masa magana ba,bai kuma ce komai dashi ba saboda yaga ya sanya kanshi cikin hidimar bikin sosai,ya bashi lokaci ya qare ya dawo hayyacinsa.....tafiya ce dai dasu tsakanin jibi da gata,kuma bazai dage masa qafa ba dole ya shirya su wuce. Girgiza kai kawai farouq din yayi,halin fu'ad saishi,baisan ma yaushe ya fita din ba bayan sun shigo cikin gidan tare. Ya sanshi sarai ya kuma sani,wani irin mutum ne shi da kasuwancinsa ke gaba da komai idan ka dauke shi anni abba da su saddiq,amma koma meye yana ji a jikinsa,yana Kuma fatan duk yadda yakai ga gujewa auren da bashi wani rashin muhimmanci ya zame masa silar shiryuwa da saituwa kaman kowanne magidanci. A nutse farouq ya ratso cikin mutane ya yiwa anni rada. Kai kawai ta gyada sanda idanunta suke kan sabreen dake zaune waje daya bata ko qwaqwaqwaran motsi. A iya haka tana iya hangen nutsuwa a tare da ita,sannan haka kawai takejin qaunar yarinyar cikin ranta. Tana iya hangen wasu abubuwan ta cikin mayafin dake lullube saman kanta,a sanda walima tayi nisa..... Kai kawo na mutane ya qara yawa tata zuciyar cike take da lissafe lissafe kala kala. Lumshe idonta tayi sanda aka fara gabatar da miqa gudunmawa ga amarya,wato kowa zaizo ya zube mata tasa gudunmawar adan wani babban qwarya dake ajiye a gabanta maimakon yin liqi,wanda daga nan za'a fara gabatar da lectures akan zaman aure. Numfashi ta sauke daga can cikin hunhunta,duk cika da batsewar mutanen dake a wajen bata hangi wani nata ko mutum daya ba. Sai takejinta bare a wajen da wani irin rashin sukuni da takura. *DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)* 08187255862 _ZAFAFABIYAR_ 21 A nutse aka fara zuwa daya bayan daya ana zube sabbin 'yan dubu dubun fil a miqe cikin bundles dinsu a gabanta. Ta rasa tsakanin burgewa da rashinsa wanne takeji cikin zuciyarta?,duk da ta hangi tarin nutsuwa da kamala a komai na taron. Idanunta ta sake dagawa a hankali ta cikin mayafin tana kallon bakin qofar shigowa gurin dake facing dinta......tamkar abinda ake jira kenan saita hangi huda na shigowa. Da farko ta dauka kaman gizo idanuwanta sukeyi mata ko kuma me kama da ita ne,saidai shigowar nadra da haneefa ya qarasa kore mata dukka shakkun data soma ji cikin ranta. Wannan bai saketa ba taga abinda ya kusa doka zuciyarta saboda firgici.....maamah ce.......tana biye dasu da dukkan alamun da zasu gwada maka tare suke......tare suka shigo,don waiwayawa haneefa tayi da alama kiran sunanta tayi,sai taga ta riqe hannunta haneefa na mata murmushi tana maida mata sukaci gaba da takowa wajen tare. "A ina ta gansu?,a ina ta daukosu?,ya akayi taje ko sukazo wajenta?,tun yaushe?,me kuma take gaya musu?" Tayi tambayar sanda taga ta tsaidasu duka su ukun kuma kowacce ta tattara mata hankalinta. Sanye take cikin wata 'yar ubansun super embellished me asalin tsadar da jikinta ke bada wani irin santsi tamkar ba atamfa ba. Tun daga yanayin shigar zaka tabbatar da gaske ta dauki duniyarta dama rayuwarta gaba daya.....hakanan da gaske komanta yana mata dadi yana kuma tafi mata yadda takeso. Daga bayanta hajja harira ce data shirya kanta itama cikin applique lace ruwan sararin samaniya. Ita dinma duba daya zakayi mata ka tabbatar da halin yazo daya kamar yadda abotar tazo daya. Kai tsaye ta daga yatsa tayi musu nuni da kujerar da sabreen ke zaune a kai,sai dukkaninsu suka maida idanuwansu kanta. Fuskokinsu suka cika da farinciki duk da basa iya ganin fuskarta sosai,suka motsa kamar zasu taho zuwa wajenta,amma sai taga ta sunkuya tana magana dasu. Cikin qasa da second talatin taga sun maida hankalinsu gareta.......sun kuma juya suna binta a baya zuwa hanyar data nufa,daidai lokacin da me gabatarwa ke bada sanarwar "Mahaifiyar ango ta shigo......uwarsa kuma zata marabceta" Maganar data finciko hankalin sabreen daga shingen tunanin data afka sanda take binsu da kallo suna biye da maamah sau da qafa.....kai kace ummeensu ce ta dawo duniya. "Uwa?.....mahaifiya?,wacece?" Ta samu kanta da shiga
Chapter 20 · 0% Book details