Sashe 50
A Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sharar bane kawai da ba'ayi ba ya sanyata haka,akwai wani abu na daban da ya bata mata rai,wannan ya bata sassauci sai ta miqe tana sake bata haquri ta bude qofar ta fita gami da rufe mata. A qasan ranta tana tafe tana addu'ar "Ubangiji ka qara mata damuwa fiye da damuwoyin data sanyawa zukatanmu.......ya rabbi ka shagaltar da ita da damuwarta ta yadda zata zame mana mu kuma hutun da bamu taba samunsa cikin gidajen mazajenmu ba". *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Daga abi sa'eed RA yace:manzan Allah S A W yace; "idan dayanku yazo masallaci,ya duba takalminsa,idan akwai qazanta ya shareta ya kawar da ita daga jiki,yayi sallah da takalminsa_ *_halal ne sallah da takalmi a qafa,na haramci a ciki muddin ba najasa ko dauda a jiki_* Ta furta har tsakiyar ranta tana jin ciwon bautar da suke ciki,wadda basusan ranar fitarsu a ciki din ba,sunfi kyautata zaton wataqila sai ranar da surukar tasu ta kwanta dama. Ajiye wayar maamah tayi a gefanta tana duban laila da hawaye ya yiwa fuskarta shabe shabe "Lafiya laila?,me yake faruwa?" Ta maimaita tambayar tana riqe hannunta "Hamma fu'ad ne maamah......ya koreni". Fuska ta ya mutse tana duban lailan,tashin hankalin da take ciki a yanzun bata jin yakai korar laila daga gidan fu'ad,duk kuwa da cewa hakan da yayi taji ya tabata ya kuma qara bacin ran da takeji a ranta. Ya nuna bata isa ba kenan kamar yadda ta saba.....amma yanzun ba shine abinda ya kamata ta damu dashi ba.....tanason tasan ina yaran?.......ina suka shige?,meye manufar yarinyar?,meye takunta na gaba?. "Kina da buqatar ki koma gidan?" Maamah tayi mata tambayar kai tsaye,don son tabbatar da maganar da sukayi da hajja a yanzun. Shuru lailan tayi,tana jin tamkar kowanne tsari na zuciyarta da kuma tunani na qwaqwalwarta ya birkice,tsare tsarenta......burikanta dama duk wani abu dake gabanta sai takejin yana sauya muhalli. Tanason fu'ad sosai......tana kuma jin soyayyarsa.......amma sai takejin zama da maamah yafi mata zama da fu'ad dadi......hakanan ko me maamah ta furta shine umarninta,to tabbas zata iya aikatashi komai tsanani da tsaurinsa. "Inason hamma fu'ad sosai,inaso na aureshi.......kuma hajja tayimin alqawarin sai na aureshi....." Maganar sai ta zowa maamah banbarakwai,tayi mata saukar ba zata,ta xubawa laila idanu tana mamakin furucinta tare da tantamar lafiyar qwaqwalwar laila din. "Tayi miki alqawari?,yaushe kenan laila?" Maamah data tattara dukka hankalinta akan lailan ta fada cikin tsananin mutuwa da kuma sanyin jiki. "Tun sanda ake shirin auren hamma fu'ad.....ta kaini gidan na zauna don na karanceshi tsaf,sannan ta bani ayyukan da zan bashi yaci saboda jawo da hankalinsa kaina da kuma siyan soyayyata......wanda daga qarshe takeson ya dawo hannunta gaba daya". " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Maamah ta fada tana jin saman kujerar yayi mata tudu da yawa,ba zata iya zama a kai ba duk da laushinta,sai ta sulale ta zauna sosai a qasa. Ta sake zubawa laila idanu sosai maganar na ratsata,amma kuma tana cike da tantama da tunanin cikakkiyar lafiyar kwanyar laila. "Tabbas laila ta fara shaye shaye" Shine abinda maamah ke ayyanawa a ranta. Ba yadda za'ayi hankalin laila daidai......lafiyarta kuma qalau ta dauki babban sirri da labarin cikakkiyar cin amana irin wannan ta gaya mata. "Don Allah kada kiyi fushi dani.....kome kike buqata zan miki maamah" Laila ta fada alamu na bayyana kuka nason qwace mata. Al'amarin ya sake jefa maamah a madaukakin mamaki "Me kikeso in sake baki labari?" Laila da gabanta keta faduwa cikin matsanancin tsoron kada ta batawa maamah ta fada tana durqusawa a gabanta. Mamaki ya sake kashe maamah,ta sake saka idanu ko zataga wani abu na tabin hankali ko hauka tattare da laila,saidai ko kadan bataga wannan ba illa tsantsar biyayya da faranta rai da takeso ta yiwa maamah din. "Ki nutsu mariya.....ki nutsu,makashinka tabarmarka......makashinka yana tare da kai" Wata zuciyar ta ankarar da ita,wannan ya sanya ta aje mamakinta da tunaninta meke faruwa?,ta maida hankalinta ga laila "Tashi ki zauna sosai muyi magana" Cikin hanzari ta miqe ta koma inda saitin inda maamah ke nuna mata ta zauna. "Me yasa kika yanke hukuncin gayamin sirrinku ke da mamarki?" Ta tambayeta da matsanancin mamaki. "Saboda ya zamemin dole na inyi miki biyayya.....inajin cewa ke din kamar uwargijiyata ce.....ni kuma baiwarki,inajin kamar dama can an halicceni ne don na miki biyayya,inajin komai zai iya samu na muddin ban miki biyayya ba......burina na mutu ina miki biyayya.....burina na mutu ina bauta miki". Ta qarashe maganar da zallar gaskiya da kuma yanayin da yake nuna cewa da gaske take furta maganar dake cikin ranta din. Kowacce tsiga ta jikin maamah sai data zuba,wannan shine kwatankwacin abinda take buri,take fata take kuma mafarkin taji ta kuma gani daga wajen fu'ad......ya akayi haka ta kasance akan laila. "Laila......akwai abinda aka dafawa fu'ad a gidansa baici ba ke kika ci?" Ta jefa mata tambayar da zallar kokwanto a ranta. Kai tsaye ta gyada mata kai tana dubanta "Eh.....kwana hudu da suka wuce,naci abincin dare a dining dinsu" "Shikenan!" Maamah ta furta tana runtse idonta,tayi tsam da ranta bata iya cewa komai ba. Tsahon wasu sakanni tana nazari a zuciyarta,kafin kuma a hankali taji kowanne tashin hankali yana sulalewa daga zuciyartata. Idanunta ta ware akan lailan "Meye shirinku a kaina.....meye shirinku akan fu'ad?" Tambayar data yiwa laila kenan tana da yaqinin da tabbacin zata gaya mata komai tiryan tiryan. Shuru maamah tayi tana biye da laila din har ta gama kwashe mata bayanin komai. Ba bayanin yadda lailan ta zayyane mata komai bane yafi daga mata hankali ba,qulli da tuggun da hajja ta shirya qarqashin nata shirin shine abu mafi tsoratarwa da razanarwa a wajenta. Don baje sirrinsu tasan zata samu information akan dukkanin abinda ya shafi hajja sama da abinda laila ta gaya mata ma a yanzu.....muddin wannan hadadden tanadin data yiwa fu'ad ne ya isa cikin laila.....to ko kashi lailan zatayi kuma take da buqatar ta shaida mata kafin ta yishi.....lallai ko bayan gida zai kashe laila ba zatayi ba sai da yarjewar maamah. Take dukkanin wani alhini da fargabar cin abincin da laila tayi ya fice daga zuciyar maamah. Baqincikinta daya asarar data jawo mata,gagarumin shirinta daya baci,wanda ta kashewa maquden kudade masu yawan gaske don ta samu fu'ad a hannunta,yanxu samun laila me zai tsinana mata?,banda kaya da zata zame mata?. Idan akwai riba guda da zata samu itace......ribar nunawa hajja kuskurenta na ha'intar qauna da aminci da tayi "Lallai zan mulki laila ko don na nunawa hajja itadin qanqanuwar maciyar amana ce.....zan mulki laila a gaban idanunta.....zan kuma bautar da ita yadda take bautar da d'iyoyin mutane cikin gidanta". Duk da takaici tashin hankali da baqinciki daya cika mata zuciya amma saita dubi laila da dan murmushi "Zaki zauna dani?" Da sauri ta daga kanta tana jin kamar an mata rahama ne "Zan zauna.....zan zauna dake maamah.....hakan yafimin komai dadi a duniya" "Da kyau" Ta fada a hankali,dan daga murya tayi sannan ta kira daya daga cikin masu aikinta na gidan tace "A bata daki" Ta bisu da kallo sai data tabbatar sun fice a falon sannan ta maida hankalinta cikin jikinta, Iska me zafi ta furzar tana lula kanta cikin duniyar tufka da warwara......babu babban target dinta a yanzu haka idan ba sabreen ba. Bata gidan ta fita.....shine abinda ta yita nanatawa tana shafa lips dinta da yatsantsa. Da sauri kaman wadda aka tsikara ta jawo wayarta,ta tafi kai tsaye izuwa ma'ajiyar lambobi ta zarce can qasa. A jere numbers din nasu suke,saidai kuma tayita kai kawo akan waye zata kira a cikinsu?,waye yafi zafin aiki?. Cak idanunta ya tsaya akan wata number da aka rubuta sunan HANZARI bata tsaya jinkiri ba ta danna kan number ta tura gaba izuwa kira. Bugu daya tak aka daga,da wata iriyar birktacciyar murya ake fadin "Allah yabar mana ke uwar dakina maganin kuka na". Wannan kirarin nasa yana fasa mata kai ainun,kuma ko a yanzun shi kadai ya bata tarin qwarin gwiwa "Nayi missing target hanzari.......ka shirya ko da kowanne lokaci zaka iya jin kirana......idan kiran kuma ya tabbata......babban aiki nake da buqatar ayimin wanda daga shi bani da sauran haufi ko matsala" "An gama uwar dakina" Ya fada da qatuwar muryarsa,bata jira komai ba ta kashe kiran,ta kuma maida akalar kiran nata zuwa ga number huda. Abu daya dai ake sake gaya mata,layin a kashe yake,saita saita lokutan da zataci gaba da kira daga nan har zuwa awa ashirin da hudu,ta aje wayar ta kuma shiga tunanin meye abunyi na gaba?. *MASHKUR* A hankali ya sake gilmawa da motar ta gaban gidan,ba kuma wai don yana da wani abunyi ba ko kuma lalura ke sanyashi wannan zirga zirgar da yakeyi ba......aah,yana yine saboda nazartar gidan da kuma dukka wani kai kawo na jama'ar gidan dama ma'aikatan dake aiki cikin gidan daga dare har rana. Wadanda suke shifting da kuma wadanda zamansu kenan. Yayi gaba,amma sai yaci gaba da kallon gidan ta rearview mirror yana kada kansa a hankali. Babba duk inda yake babba ne,gidan na daya daga cikin dream house dinsa daya jima yana tunanin idan har ya samu yadda yakeso a shekaru goma masu zuwa zaya mallaki irinsa. Hannunsa ya sanya ya daki steering din motar yana jin wani zafi cikin ransa. Yarinyar tasha dashi da yawa a rayuwa,banda wani abu daya rinjayi zuciyarsa tabbas plan A dinsa a yanzu shine zai zama plan B,plan B kuma shine a plan A,to amma duka wannan bazaiyi aiki ba......yana ganin gwara ya fara diban ganimar tukunna,idan yaso ko meye zai faru daga baya me sauqi ne. "Ina fata ka gama kallon komai?" Yayi magana da mutumin dake zaune a back seat wanda zai wahala ka iya fahimtar da mutum a gurin. Kai ya jinjina yana motsa system din dake saman cinyarsa "Na gani......aiki ne me bala'in hatsari da dukkaninmu zamu jefa rayuwarmu cikin hatsari........amma kuma,ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba.......let's try it......idan mukayi winning...." Sai ya saki murmushi yana rufe system din "Zamu kasance mutane mafi sa'ar zuwa duniya" Ya qarasa maganar yana dukan bayan kujerar dake a gabansa. Iya nasarar da yayi musu hasashe ta saka mashkur qyaqyacewa da dariya "Inaso naji dandanonta.....inaso naji ya take.....bansan adadin mafarkin da nayi a kanta,ban taba sanya kwadayina akan wata 'ya mace ba tunda na fara sanin 'ya'ya mata....wannan macen ta zullemin