← Book details Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 18

Sashe 9

Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     "Yayinda shikuma yake cigaba da har kokinsa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, bashida wata damuwa sai guda daya zuwa biyu wanda shine yakasance abu marar dad'i dayake faruwa agaresa tsawon watanni dasuka wuce, wato idan yana mafarkinsa da queen of the dream dinshi atayar dashi, sannan yaushe ne queen of the dream dinsa zata bayyana agaresa"?..

"Kamar yanda kullum take fad'a mashi cewa zata bayyana masa, kasam cewar tin bayanda yasamu lafiya kullum yakwanta barci sai yayi mafarkin kyakkawar black beauty girl, wacce sannu ahankali so da kaunarta yasamu gurin zama acikin zuciyarsa da jini da jijiyar jikinsa.

       "Wanda dalilin dayasa mata suna queen of the dream kenan, wacce ayanzu duk wanda yake kusada shi babu wanda baisan da zamanta azuciyarsa ba, daga *Dad* aunty *Bebe* da *papa* da *Bulama* harda *Mom* dake chan kano tasan da zaman sarauniyar mafarkinsa,  "Da farko *Dad* tsoro yaji atunaninsa ko aljanun ne suka dawo zasu aureshi,

  tunda ance ai aljanu suna auran mutum dan haka yafadawa malam inda yai istahara akai yagani basu bane "mutumce kuma ita ce" abokiyar rayuwarsa, dan haka hankalinsa yakwanta.

    "Yayinda itaka aunty *Bebe* taso ace ai aljanun nan ne data tura  masa suka dawo, itakam *Mom* dinsa dataji hakan azahiri tanuna masa hankalinta ya kwanta, saidai kuma abadili chan 'kasan zuciyarata bata yarda da maganar malam din ba, sai tanagani kamar duk shati fadine irin na malamai ne, dan haka akoda yaushe idan sukai waya ko idan sukaje gaida Ita sai tayi masu maganar suyi aure shida *Bulama*, 

haka man mana karsu tsaya jiran abinda basuda tabbas akansa lokacifa tafiya yake yakamata ace yanzu sunada mata harma da yara, saidai suyi murmushi dukansu inda *Bulama* yakance insha'allah zamuyi, yayinda shikuma *Blue* sai yace *Mom* karki damu *Mom* very soon my dream queen zata bayyana muyi aure, alokacin my guy yasamu mata sai muyi gaba d'aya idan kuma bai samuba sai nayi nabarsa, yana me kallon *Bulama* cike da zolaya, sai itakuma tayi dariya tace Allah dai yahad'aku damata nagari wayanda zasu kuladaku da kyau sai suce ameen.

********

*Bayan kwana biyu*

_Abuja_

"Hakan su *Bilal* suka cigaba da gudanar da rayuwarsu gwanin sha'awa shida *Bulama* "kansu ahade yake, ko su" *Dad* sai sunyi da gaske suke gane masu, bazaka tabajin fad'ansu ba sai aguri d'aya wato Idan *Bilal* yana barcin me dad'i dayake cike da mafarkin queen dinsa, idan *Bulama* yatadashi to yanzu zakaji ruwan masifa agurin *Bilal* din.

"Inda zakaji yana fadin _my guy_ bafanason walakaci saunawa zan fad'a maka idan kaga ina barcina kadaina tayar dani eye?..., amma saboda tsabar iskanci irin naka sai katayar dani ko?...yayinda shikuma zayaita dariya yana fadin "eh din natayar mijin sarauniyar aljana kawai.

     "To sarkin mafarkin aljanar mafarki sai aje ayi wankan tsarki domin dai yanzu nasan duk ka baci, dan natabbatar yanda kake fama da 'd'an guntuwar jarabarka, bazaka rasa d'an ta'ba wannan aljanar taka tamafarkin kaba ko?...inda yake kasara fadi tareda d'age masa gira d'aya cike da zolaya.

      "Yayinda shikuma idan yaji yace" haka sai yai tsaki mtww! cike da d'an haushi ya kyalesa, idan afalo yake kwance sai yatashi yashiga cikin bedroom ya cigaba da barcinsa, idan kuma yashiga wani lokacin baya komawa barcin saidai yai wankan domin kuwa, da gaske acikin mafarkin harda tarayyar auren yakeyi da "Ita.

"Kamar yanzuma misalin karfe goma shad'aya da kwata na safer asabar, *Blue* yana kwance afalo yana barcisa cikin nutsuwa me daukeda mafarkinsa da yasaba sai ga *Bulama* yashigo sanye dawani shadda gold color me d'an haske anyi mata dinki zamani, kafarsa sanye da farin half cover shoe hannunsa rikeda wayoyinsa kansa ba hula sai tarin kashi irin wanda samarin yanzu suke bari,

saidai nashikam ba irin murd'ad'd'an nan bane nashi agyara yake sai walkiya take kamshi sai tashi yake aajikinsa me dad'i, sosai shigar tayi masa kyau.

Fuska cike da mamaki yake kallon *Blue* din wanda yake sharan barci hankalinsa kwance, duka yamaka masa akafa aikam ad'an forgive yafarka tareda kallon wanda yadukesa, inda yaga *Bulama* tsaye akansa cikin shirinsa tsaf sai taunan  chumgam yake  tareda sakar masa murmushi,

fuska yahade tareda tashi yazauna cike da masifa yace uhum! ainasan saikai my _guy_ me yasa kakeyi mun hala  ne wai eye?.., cikin kayataccan murmushi yace nayi din malam dall katashi kasan zamu fita amma kawani kwantawa,

kanata barci nan me dauke da wannan mafarkin nakada baya karewa so katashi kai wanka kashirya mufita, tsaki yaja mtww! tareda cewa bazan tashi din ba kajiko?..baka kuma isaba malam tashi yayi yashige toilet yana turo baki cike da takaici tashinsa dayai daga barci.

********

"Aban garan su *Beenazar* kuwa
suma cikin wayan nan watanni dasuka wuce arziki yasake ahabbaka sosai, inda har *Abbu* yasiyi mota sai yabarma *Bassam* mashin din suna hawa yakuma yasiyama *Ammu* mota, wacce suma sosai harkan siyar da bedshit din yakar besu.

  "Sosai *Abbu* yake kulada ahalinsa, haka zalika duk wani abinda su *Beenazar* din keso yana siya masu babu wani abinda yaragesu dashi, dan haka hankalinsu akwance yake sosai domin babu abinda yake damunsu, idan kagansu bataka taba cewa sun ta'ba shiga kuncin talauci arayuwars ba dan hakanan suma suke cigaba da rayuwarsu gwanin sha'awa wannan kenan .

*****
Pls sis *Beena* kiyi sauri kifito yah *Bunayya* fa yafita tin d'azu mu yake jira kinji?...., to sis *Basma* gani nafito muje sanye suke cikin boyal les ja me fulawoyi fari da baki, dinkin doguwar rigane dayai matukar karban jikinsu musamman *Beenazar* wacce sosai sharp dinta yafito,

  sai suka yafa fararan mayafi tareda saka jaka da takalmi duk farara sunyi kyau sosai gwanin sha'awa, nan suka jera suka fita.  Inda suka iske *Bunayya* cikin mota shida *Baffa boy* sai wasa yakeyi mashi shikuma sai kyalkyata dariya yake, wanda shima aka shiryasa cikin yan kayansa riga t-shirt baka da wando ja abu ga fari sai yai kyau gwanin sha'awa kamar d'an turawa,

yayinda shima *Bunayya* cikin shirinsa yake tsaf inda yasa riga t-shirt ja da wandon jeans baki, shima yayi kyau sosai gaba *Beenazar* ta zauna yayinda *Basma* tashiga baya idan *Baffa* yana ganinta yasa rigima wai zayaje gurinta, kasan cewar tuni yashaku da'ita da sauri *Bunayya* yamika natashi yana cewa to yimaza kaje yaron mom *Basmatin* umma, kar kayi mana kuka.

   "Cike da kauna takar'besa tana dariya tareda fadin Allah sarki yarona zonaji kaji wane yata'ba mun kai nai masa duka, aikam yafara bulbula dariya itama tanayi masa dai-dai lokacin da *Beenazar* tace eye lallai kenan yah *Bunayya* za'a daka?...,

cikin murmushi *Bunayya* yatada mota yana fadin ai zata iya indai akan *Baffa boy* ne, tace ah! lallai kam da alama yah *Bunayya* sabon shopping mall din me suna *LUFHAT CE* zaka kaimu yace ok ai suna kawo nagartattun kaya masu kyau.

*******

    "Cikin nutsuwa su *Beenazar* ke siyayyarsu itada *Basma* datake rungumeshi da *Baffa boy*, wanda tun shigowarsu yaketa kiriniya hakan yasa tadauke shi tarike, shikam *Bunayya* tunda yasiya abinda yakeso yafita bayan yabasu kudi yace masu su iskesa amota, tunda su idan sukazo siyayya sai suyita nuku-nuku suna shiririta shikuma abinda yatsana kenan. dan haka yafita yabarsu

*********

    "Achan gefe kuma wani kyakkawan saurayi ne, sanye yakeda wata tsadaddan dakakkiyar shadda gold color da akaimasa dinkin zamani wanda yakarbi jikinsa, kamshin turare sai tashi yake ajikinsa tabbas shidin kyakkawane ajin farko, tsaye yake agaban gurin turaruka wanda kallo daya zakai masu kagane masu asalin kyaune da tsada.

"Ahankali yake daukan turaran yana dubawa waya yake amsawa cike da nutsuwa da kuma ladabi, wanda zaya nuna maka cewa wanda yake wayar dashi yanada matukar muhimmaci agaresa.

"Ahankali yajuyo fuskarsa dauke da kayataccan murmushi bakowa bane face *Bilal*, hannunsa dauke da wani turare yamikama *Bulama* dake gefensa yakarba
yasaka cikin basket din dasuke zuba siyayyar dasukeyi, cikin dariya had'eda sauri sauri yakarasa maganar dayake awayar dafadi *Mom*, nace maki very soon ok to yanzu muna shopping ne idan mun koma gida zankiraki yakatse wayar kitttt. 

         "Sannan ya kalli *Bulama* yana murmushi shima murmushi ne akan fuskarsa yace *Mom* ce ko?..kai ya gyad'a masa alamar "eh sannan yace duk tadamu muyi aure, yace aitanada gaskiya hakana *Mama* take damuna wai ko sai mun tsufane tukunna zamuyi auran.

Nace" mata a ah insha'allah zamuyi dazaran lokaci yayi, kai kuma dan Allah kafita maganar "wannan tacikin mafarkin munemi "yammatana gasuna birjik mu aura kaji?.., harara yabanka masa tareda cewa to bazan nema din ba "kai kaje kanema mana, ok to shikenan kada Allah yasa kanema din kuma bari kagani kwanan nan zanfara neman matar aure eheee!, domin nagaji da soyayyar nan tashan minti.

      "Cikin dariya *Blue* yace nikam ina ruwana dama kaine kaga zaka iya wannan soyayyar tawani shan minti cha, haka kawai sai kayita rungumar kowace kazamar "yarinya tareda had'a bakinka danata kilama wata ko brush batayi", har kaje ka kwashi warin baki cike d'an jin haushi yace "eh din ina ruwanka.

  "Cikin dariyar zolaya yace aidama baruwana din domin nikam idan kaga nasha bakin "wata to na my queen ne" kagane?.., so sai mutafi ko domi dai nagama nawa shopping din kaifa kagama naka ne ko zaka siyama yammatanka na shan sweet ne?...,yakarasa fadi tareda d'aga masa gira d'aya cike da zolaya.

"Yace malam aikasan nagama sarai sukuma ko na siya masu ai ba laifi bane, dan haka mutafi idan kuma zaka tsaya yimun iskancine to sai katsaya ni nayi nan, yawuce yanufi gurin biyan kudi yayinda *Blue* yabi bayansa yana masa dariyar zolaya,

bayan sun biya sannan me k suka fito suna isa gurin mota *Mom* tana sake kiran *Blue* murmushi yayi tareda amsawa yashiga motar yazauna, yana cewa *Mom* nace maki idan muka koma gida zan kiraki dai-dai shima *Bulama* yashiga ya zauna tareda ja suka bar harabar shopping mall din.

    "Fitar su *Blue* keda wuya su *Beenazar* suka isa gurin biyan kudin, kasan cewar shopping mall din babban gaskene yasa harsu *Bulama* suka gama siyayyar suka fita, batareda su *Beenazar* din sun gansu ba hakanan suma su *Bulaman* basu gansu *Beenazar* din ba.

*Baffa* ne yafara rikici wai sai mamansa tadaukesa, hakan yasa takar'besa tana fad'i kai! Babana Mom*Basma* ce kuma yanzu kake guduwa daga gurinta eye?.., cikin dariya tace ah! kyalesu aida mun shiga mota zayace gurina zayazo, nan *Basma* tabiya kudin suka dauki kayan suka fita.
Chapter 9 · 0% Book details