← Book details Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 18

Sashe 1

Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🎍🎍🎍🎍
     🎍🎍🎍
          🎍🎍
               🎍
🎍 *ZAUNJUN MAJNUN* 🎍
(Miji mahaukaci)

*BOOK 2* 1️⃣to5️⃣
🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍

WRITTEN BY

🎍 *AMINA UMAR FARUQ* 🎍

OR

🎍 *MEENAL*🎍

Marubuciyacer

*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUNJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*TASEERI*
and now
*ZAUNJUN MAJNUN part 2*

_SADAUKAWAR GA_

Iyayena abin alfarina ina godiya bisaga tarbiyyar dakukai mu, dan haka ina rokon Allah yasaka maku  da alkairi yakareku daga sharrin mutum da aljani, ubangiji yasa kugama da duniya lfy ameen ya rabbi.

Wannan littafin na kudi ne akan farashi me sauki, 200 naira only zaku iya turo kudin tawannan account no 0047769671 Amina Abdullahi A., sannan kuturo shaidar ku ta hanyar yin screen short ta wannan no 08161850024, Idan kuma katine sai ku tuntubi wannan lambar 09022880912, sai naji ku.

✍🏼

_Bismillahirramanirraheem!_

""""""Cikin bugawar zuciya tace tarbiyyar damukai maki kenan?..tafadi tareda sha'kemata wuya, cikin mugun bacin rai tasake cewa nace" irin tarbiyyar damukai maki kenan eye?... tambayarki nake, tana me sake  sha'ke mata wuya sosai tamkar zaka fitar mata darai.

"Aikam tuni kyakkawan idonun *Beenazar* din sun fito waje saboda sha'kar da *Ammu* tayi  mata wanda bana wasa bane, cikin mugun bacin rai had'eda daka tsawa tace zaki fad'amun kosai na illataki eye?....

"Kai *Beenazar* din take girgizawa yayinda tuni hawaye sun wanke mata fuska, magana takeso tayi amma takasa domin ko kad'an *Ammun* bata batadamar yiba asalima cikin mugun bacin rai take sake sha'karta, dafad'in wlh ko kifad'amun wanda yai maki wannan cikin naji kinki ko na kasheki,

domin garaki mutu dadai na cigaba daganinki d'auke da wannan abin kunyar dakike jawo muna, konace kika jawo mun tunda ubanki yana kallo amma yakyaleki dayake shid'in na mijine be damu abin kunyar dakika jawo manaba kai!.

Innalillahi'wa'inna'ilaihirraju'un ni Fatima wai cikin shegen ke jikinki *Beenazar* tabd'ijam wato kenan duk tsawon shekarun damuka dauka muna baki tarbiyyar, shine rana d'aya kika tsaya "wani yarud'eki da banzayan kalamashi" kika watsar saboda ked'in shashashace wacce batasan ciwon kanta ba ko?...

dan haka kifad'amu! fad'amun!! nace" ki fad'amun "wanene wanda yaimiki wannan cikin shege eye?.....takarashe fadi tareda sake shaketa sosai tana me jijjigata da karifin, idan kuma har bazaki fad'amun wanda yai maki cikin shegen nanba ko to wlh yanzu zan kasheki nahuta domin bazan iya daukar wannan bakin cikin ba.

"Daidai lokacin da *Abbu* yashigo kasan cewar tin lokacin da *Ammun* takira *Beenazar* din suka shiga daki sai yaji hankalinsa be kwanta ba, dasauri yakarasa gurinsu yana fadin Subhallahi fatimata kisan kai zakiyi?...,tareda kokarin kwace *Beenazar* din daga hannun *Ammu* yana sake fadin haba Fatima kasheta zakiyi bakiga halinda take ciki bane eye?...

yakarashe fadi tareda kwace *Beenazar* wacce tuni numfashinta yakusan barin jikinta...zaunar da'ita yai agefen gado aikam ta tafi luuuu! zata fad'i, dasauri yarikota yarungeme agefensa sai kuma tafara tari sosai cike da tausayinta yake fadin, sannu *Beenazar* tareda daukan ruwa dake gefen gado acup yabata tasha sai sauke ajiyar zuciya wahala takeyi,

"Yayinda *Ammun* takoma gefe tana sauke numfashi cike da tsanani bacin rai taname banka masu hharara shida *Beenazar* din.

Cike da bacin rai yace haba fatima wannan wani irin d'anyan aikine ki keshirin aikatawa eye?..., saboda Allah fa idan kikai masu illah itada abinda yake cikinta fa sai kice Allah yakawo kome eye?...cikin mugun bacin rai tace abinda dai kaceso kace mun kenan, wato shi wannan shegen cikin najikinta Allah ne yakawo ba sakacin kaba ko?...

kallonta yai fuska had'e yace fatima me kike nufi ne?... cikin bacin rai had'eda fad'a tace *Abban* *Beenazar* kenan aikasan abinda nake nufi, cikin shegen dake jikinta nake magana akai wanda konayi rantsuwa bazanyi kaffara ba sakacinka ne yasa tayishi.

Kai ya girgiza tareda cewa humm! Allah sarkin rashin sani yafi dare duhu, haba Fatima taya kike tunanin zanyi sake har haka tafaru da *Beenazar* eye?...kuma ke kanki kinsa airin tarbiyyar damukaimata babu yanda za'ai hakan tafaru saida idan kaddaran ubangiji wanda babu wani mahalukin dazaya ta'ba kauce mata.

Cikin takaici tace eh ai haka zakace amma tabbas idan bakai sakaci ba to ya'akai tasamu cikin shege eye?....duk irin tarbiyyar dana bata saboda Allah fa, yace a ah Fatima kidaina kiran cikin jinkin *Beenazar* shege domin ba shege bane, cike da takaici tace to idan ba shege bane to mene eye?..

Tabbas bashege bane kamar yanda kike tunani yanada uba kamar kowa ne d'a dayake da uba.

Cike da mamaki ta kalleshe tareda cewa *Abban* *Beenazar* me kake nufi, abinda nafada nashinake nufi cikin jikinta yanada uba da sauri cike da d'an tsoro tace *Abban* *Beenazar* kenan aure kayi mata ban saniba?....,yace kwarai fatima saidai kisani hakan Allah yakaddara tace kamar yayafa?..

"Ahankali yamike yanufeta tareda kamota yazaunar agefen gadon sannan shima ya zauna, ruwan yadauka yabata tasha saidai me fuska daure ta kawauda kai gefe alamar bazata shaba, cikin kwantar da hankali
yace yi hakuti fatimata ai bakitaba yimun gaddamaba dan haka nasan bazaki fara yauba ko?...

kai ta gyad'a idonta yana me cikowa da kwalla, yace yauwa mar'atussaliha karkiyi kuka har kizubar mun da tsadaddan hawayeki, nasan zuciyarki tayi zafi abisa rashin sabi dan haka kisha zuciyarki zatayi sanyi kinji?...kokarin karba takeyi yai sauri hanata tahanyar kafamata cup din abaki kad'an tasha takauda kai.

Yayinda *Beenazar* take kallonsu tana sauke numfashi ahankali, zuciyarta cike da kaunar iyayenta sosai zaman takewarsu take mugun birgeta.

Saida *Abbu* yatabbatar da *Ammu* ta nutsu sosai sannan sannu ahankali yafada'a mata komai tundaga ranan da *Blue* yabiyo su *Beenazar* gida, dazaman dasukai dashi saboda ganin halinda yake ciki natabuwar kwakwalwa,

har ranan da akaganshi sukazo nan gidan inda *Dad* yabukaci yaba d'ansa auran *Beenazar* din saboda tsananin shakuwar dasukai, inda shikuma yamemi jin tabakinta ta amince har akai auran wanda shine dalilin dayasa aka gyara mashi kafansa, sukuma aka biya masu kudin makaranta har kawo ranan da *Beenazar* din tadawo gida da kuka, wai sunce cikin jikinta bana d'ansa bane da zuwan dasukai shida *Bassam* saboda suji daga bakinsu, dayanda suka 'kekyashe kasa sukace sam bacikin d'ansu bane dayanda sukai dukkai saida yafada mata komai.

sannan yakarashe fad'a mata irin halin kuncin dasuka shiga saboda rashin dawowarta, har zuwan da *Beenazar* din tayi abuja dan ganin lafiya bata dawo ba dakuma rashin sanin halinda take ciki duk saida yafada mata.

Cike da bacin rai tace lallaima mutumin nan shikenan tunda d'anshi bayada hankali sai bazaya iyayin tarayya aure da mace ba?...*Abbu* yace humm!, Nima abinda nace kenan ai wannan ba hujja bane dan bayada lafiyarka kwakwalwa hakan bayana nufin shikenan, bashida lafiyar jiki bane dazaya hanashi tarayya aure da mace ba dan haka na kyalesu domin nasan inasha'allah gaskiya zatayi halinta,

cikin fushi tace shikenan sai ka kyalesu?...to fatimata idan ban kyalesu ba yazanyi masu?, cike da jinhaushi tace eh tunda "sun gwada maka finkarfi dole ka kyalesu" ko dayake kaima harda kai tunda kaje kai masu sakwasakwa, dole suyi maka haka amma da saika kaisu" kara idan sunfi karfinka ai basufi karfin hukuma ba, tunda abin nasu rashi mutunci ne da butulci dan haka ni zankaisu kara gurin "yaya idan yaso suyi bayani agaban alkali, tayanda cikin yazama bana d'ansu ba domin mudai munyima yarmu tarbiyyar me kyauta ta yanda bazata taba kwaso mana abin kunya har abada.

"Cikin murmushi yace haka ne fatimata gaskiya kika fad'a, saidai idan mukayi karansu munkoma irinsu" kenan wato butulu, fuska had'e tace eh mana bashikenan ba sai muzama d'aya.

A ah fatimata bazamuyi hakan na yanda nace haka za'ayi wato mu kyalesu inasha'allah gaskiya zatayi halinta kuma da izinin Allah sai sun neme mu dakansu, aranan zakiga abinda zanyi masu nayi miki alkhawarin, badan ranta yasoba tace shikenan amma zan fad'ama yaya duk abinda yafaru yace ba damuwa.

*********
"Sannan itama cikin sanyin jiki tafad'a mashin duk abinda yafaru tundaga ranan da taje abujan gidan kawu Mado, da abinda yaimata wato akasheta wanda dayake batada hakkinsa sai Allah be basu iko ba, tafarfado shine alkali yabigeta har tayai losing memory ta har kawowa kwatar mata hakkita da Abban yayi wato Alkali wanda take kiransa da yaya,

sosai *Abbu* yaji dad'in hakan tace yakumace yau zamu tafi dukka saboda haka saikaje kayi masa godiya cike da farincikin yace yanzu kuwa fatimata kai alhamdulillahi sannan yafita.

Wani irin kallo *Ammu* tayima *Beenazar* tareda matsawa gurinta wanda yada *Beenazar* jin mugun bugawar zuciyata y to Kallon *Ammun* cikeda tsoro, yayinda cikin wani irin yanayi *Ammun* tace......

Muje zuwa

*LUFHAT CE or MEENAL*

_Allah kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_

🎍🎍🎍🎍
     🎍🎍🎍
          🎍🎍
               🎍
🎍 *ZAUNJUN MAJNUN* 🎍
(Miji mahaukaci)

*BOOK 2* page 6️⃣to🔟
🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍

WRITTEN BY

🎍 *AMINA UMAR FARUQ* 🎍

OR

🎍 *MEENAL*🎍

Marubuciyacer

*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUNJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*TASEERI*
and now
*ZAUNJUN MAJNUN part 2*

_SADAUKAWAR GA_

Iyayena abin alfarina ina godiya bisaga tarbiyyar dakukai mu, dan haka ina rokon Allah yasaka maku  da alkairi yakareku daga sharrin mutum da aljani, ubangiji yasa kugama da duniya lfy ameen ya rabbi.

Wannan littafin na kudi ne akan farashi me sauki, 200 naira only zaku iya turo kudin tawannan account no 0047769671 Amina Abdullahi A., sannan kuturo shaidar ku ta hanyar yin screen short ta wannan no 08161850024, Idan kuma katine sai ku tuntubi wannan lambar 09022880912, sai
najiku.

✍🏼

_Bismillahirramanirraheem!_

""""""''''Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ba tareda datace komai ba saidai tad'an rungumo *Beenazar din akafad'arta, cikin kwantar da murya cike da tausayi had'eda lallashi tace kiyi hakuri da abinda nai maki, hankali nane yai mugun tashi dana ganki dauke da wannan cikin,

wanda kowace uwace taga 'yarta dauke da ciki, alhalin ba aure tayiba kinsa dole ne hankali ta yai mugun tashi taji ba dad'in ace yarta na dauke da cikin shege ko?....,kai *Beenazar* ta gyad'a alamar "eh idonta yana cikowa da hawaye, tace to kingani dan haka kiyafe mun kinji?....

    Rungume  *Ammu* tayi tareda sakin kuka me ta'ba zuciya tana me fad'in  *Ammun* abinda kikaimun shine dai-dai, wanda na tabbata kowace uwa tazo ta'iske 'yarta haka irin hukunci da zatayi mata kenan dan haka dan Allah kidaina bani hakuri, tunda bakiyi mun komai ba.
Chapter 1 · 0% Book details