← Book details Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 18

Sashe 12

Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kai ta gyad'a alamar to yace yauwa ki kwantar da hankalin, to *Abbu* yauwa to tashi kuge ga yar uwarki can tana jiranki idan *Abbanku* yadawo kizo kifad'amu zamu wata muhimmiyar magana dashi kinji ko?...tace to*Abbu* tareda tashi tafita, inda ta iske *Basma* suka nufi gidansu.

*******
Kodasu *Blue* suka fito kai tsaye gardin suka nufa, inda suka zauna akan wasu fararan kujeru 'karkashin bishiyar mangwaro, cike da farincikin *Bulama* yace kai my _guy_ wlh naji dad'in jin cewa sis *Beenazar* tahaihu Allah sarki baiwar Allah,

nikam har namatsu su" *papa* suje su dawo muma muje, da sauri  *Blue* yace ka daije kai kad'ai domin ni man daka ganni babu inda zanje saboda wannan matar wlh, cike da mamaki *Bulama* yace me kake nufine wai?...wani irin kallo yai masa tareda cewa ina nufin ni bazanje ko'ina ba, dasuna wani abu wai shi biko saidai kai kaje.

        "Cikin sanyi murya yace saboda me?.. saboda wlh ko kad'an banji inason taba balle har naji, san zama da'ita muyi rayuwar aure da sauri yace kai! my _guy_ to da dakai da'ita fa?...Harara ya watsa mashi yace dakace, kuma ada dinma banida hankali yanzu kuma da hankalina.

    "Sannan tuni zuciyata tayi nisa da so da kaunar my dream queen, wacce naji ajina kwanan nan zata bayyana agareni muyi aure, wato kenan duk abinda kafad'a agaban *Dad* da *papa* kad'ai fad'ane but amma baikai zuciyarka ba kenan?....

"Eh kusan hakane saboda bazanyi masu musu akan abinda sukace nayiba, but amma sam bana ra'ayinta zandai zauna da'ita ne saboda su" cike da mamaki *Bulama* yake kallonsa, sannan yace kuma har cikin zuciyarka iyakar gaskiyarka kake fad'a?... yace kwarai kuwa.

"Kai ya gyad'a alamar gamsuwa da abinda yafad'a wanda yatabbatar iyakar gaskiyarsa kece tunda yasan shi ciki da bai, saidai kuma ko kad'an baiyi tsammani hakan daga garesaba. hakan yasa, yace kenan dakace munyi "mata butulci ashe kai wanda zakai mata yafi namu ko?...cike da rashin fahimceta, yace kamar yafa?....cikin bacin rai yace kamar ban ta'ba sanin cewa kai  butulu babe sai yau, cike da mugun mamaki yakallesa yace!.....

Muje zuwa

*MEENAL or LUFHAT*

_Allah kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_

🎍🎍🎍🎍
     🎍🎍🎍
          🎍🎍
               🎍
🎍 *ZAUNJUN MAJNUN* 🎍
(Miji mahaukaci)

*BOOK 2* 3️⃣6️⃣to4️⃣0️⃣
🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍

WRITTEN BY

🎍 *AMINA UMAR FARUQ* 🎍

OR

🎍 *MEENAL*🎍

Marubuciyacer

*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUNJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*TASEERI*
and now
*ZAUNJUN MAJNUN part 2*

_SADAUKAWAR GA_

Iyayena abin alfarina ina godiya bisaga tarbiyyar dakukai mu, dan haka ina rokon Allah yasaka maku  da alkairi yakareku daga sharrin mutum da aljani, ubangiji yasa kugama da duniya lfy ameen ya rabbi.

Wannan littafin na kudi ne akan farashi me sauki, 200 naira only zaku iya turo kudin tawannan account no 0047769671 Amina Abdullahi A., Idan kuma katine sai ku tuntubi wannan lambar 08161850024, sai naji ku.

✍🏼

_Bismillahirramanirraheem!_

    """"Guy ni ne butulu"?....cikin mugun bacin rai yamike tareda nunashi da yatse, yace "eh kai! din ne butulu babbama kuwa irin wanda ban ta'ba ganiba arayuwata, shima cikin bacin rai yamike yace malam wai meye hakane kaketa faman kirana da wani mugun suna wai butulu?...ankiraka dashi d'in domin ka cancanci akiraka dashi kaji ko?...,

cike da takaici yace tukun nama tsaya wani irin butulci nai maka da har zaka ringa kirani butulu, saboda tsabar mugunta har da wani cewa babban butulu ko?...yace "eh kai babbn butulune nafad'a, kuma ni bani kaima butulci ba *"Beenazar* kaima butulci.

"Yarinyar data sadaukar darayuwarta ta aureka" alhalin kana cikin halin hauka ba tareda damuwa da haka dinba shine zakai mata butulci, yace to ni ina ruwana da sadaukar da rayuwarta datayi eye?..."eh dama shi d'an adam butulu ne arayuwasa kai masa halacci shiko yaimaka butulci.

   "Cikin jin haushi yaja tsaki mtww! tareda cewa to waini me nawa aciki, tunda bani taimawa halacci ba ku tayimawa dazaka wani dameni dacewa tayimun halacci nai mata butulci eye?... "Harara yasake banka masa tareda cewa "eh lallai kace haka mana saboda tsabar walakaci irin naka, sannan tunma baka gantaba  har kana wani cewa baka ra'ayinta" dayake kaidin babban butulune ko?...

cikin mugun jin haushi yanda yaketa kiransa butulu yace kaga malam kadaina kirana da butulu kaji ko?...shima cikin jin haushin yace bazan dainaba din, tunda butulci kayi.

Ok" to ka cigaba dakirana butulun nadai ce bana ra'ayinta kuma bazanje bikon ba kaji ko?...to kada Allah yasa kaje din mana sai me to idan bakaje ba eye?...fuska murtik yace sai kayi yanda zakai dani, yace uhum! ni babu yanda zanyi dakai saidai kai kayi yanda zakai dani tunda bafashi sai zanje eheee!,

cikin hassala yace to ina ruwana kai tazuwa mana idan ka'iya kafinruwa saurin zuwa kaji ko?..., kuma wlh idan kafad'awa *Dad* banjeba sai mun samu mummunan matsala dakai eheee!.

      "Cikin bacin rai yace Oho! dai wannan kuma yarage naka, saidai naje nayo maka bikonta" insha'allah kuma dole sai zauna da'ita eheee!. ya karashe fadi yana kokarin tafiya, yayinda shima cikin bacin rai yace zama "da'ita nabanza tunda bana ra'ayinta" kada Allah yasa kayi ra'ayinta din kuma insha'allah sai Allah yajarabeka da masifar kaunarta",

cikin masifar bacin rai yace mugu ba ameen na domin zuciyata my queen dream KAD'AI takeso, yace oho dai insha'allah sai Allah yakarbi addu'ata ni kuma nace ba ameen ba eheee.

     "Haka dai suka rabu baran baran kowa rai bace, inda *Blue* yabi bayansa da kallo yajin wani irin mugun bacin rai ganin yanda suka rabu da *Bulaman*, wanda wannan shine karo nafarko a tsawon zamansu dasuka samu matsala irin hakan da juna, hakan ne yasa *Blue* sakejin haushi da tsanar *Beenazar* wacce yatabbatar duk ita ce silar faruwan haka, tsaki yaja mtww! cike da mugun bacin bacin rai  sannan yanufi cikin gida yana fad'in I hate this girl before I see her.

*********

"Aban garan su *Dad* kuma aranan basuyi sanyi aguiwa ba, sukaje gidan alkali sasu inda kuma cikin sa'a suka iske baida d'eda dawowa, daga kotuba kasan cewar yau ya yanke hukunci akan wata shari'a da akadad'e ana gabatarwa.

     "Wanda  fitar *Abbu* kenan sukazo kasan cewar yashiga yafad'a mashi abinda *Beenazar* tafad'a yafaru tsakaninta da *Dad*, da yanda tanuna jin tsoron karsu" rabata da d'anta" yace mashi kar yadamu insha'allah baza su rabata da "d'anta ba.

"Bayan *Abban* yabukaci sanin suwaye aka fad'a mashi, ba tareda bata lokaci ba yasa akashiga dasu babban falonsa dayake ganawa dabaki inda ya'iskesu cike da girmamawa suka gaisa, kasan cewar yasan *Papa* dan haka bayan sun gama gaisawa yake tambayarsa yada cewa Barr *Bulama* aikin?...

alhamdulillahi ranka yadad'e, masha'allah kwana biyu ban ganka akotun mu ba I hope dai lafiya?...cikin murmushi ya amsa da cewa ranka yadad'e, lafiya lau wlh kwana biyun ne banyi aikin bane na tafiya ne.

   "Masha'allah to Allah yataimaka ameen, to ina fatadai ba ankawo mun cin hanci bane, akan wata shari'a da'akeson agudanar ba ko?....cikin dariya *papa* yace a ah yallabai ai nasanka" kai baka kar'ban cin hanci, sannan nikaina idan har baka mantaba bana tsayawa marar gaskiya.

Murmushi*Abba* yai tareda cewa haka ne to meke tafe daku?..nan *papa* yafara fad'a mashi abinda ke tafe dasu, aikam kafin duk *papan* yagama fad'ar abinda yakawosu" *Abban* yafara fad'a da *Dad*  tareda cewa ainasan da maganar,  dama inajiran zuwanku shin dr abinda kai sam baka kyauta ba, ai bahujja bane dan d'anka bayada hankali sai bazaya iya tarayya aure da mace ba, nan dai sukai tabashi hakuri musamman *Dad* wanda shine me laifin.

        "Sannan *Abban* yad'aga waya yakira *Abbu* yace" yanason ganinsa, chan saiga shiya shigo da sallama suka amsa yana ganinsu" *Dad* yad'auke kai tareda zaunawa kusad'a *Abba*, ba tareda yakallesu ba yagaidasu" fuska had'e inda  suka amsa, ya kalli *Abba* yace yaya gani kace kanason ganina ?._ kasan cewar yanda yaji *Ammu* nakiransa yaya haka shima yake kiransa_

."Yace "eh dama su Barr ne, nan yafad'a mashi duk yanda sukai harda hakurin dasuka bashi gasunan kuma yakarajin komai abakinsu, aikam nan shima yafara fad'a ta inda yake shiga batanan yake fitaba, inda har yana cewa aikunce bacikin ku bane to yanzu kuma meya kawoku?....ko dayake nagane wato tunda kunga "yaron yayi kama danku shine kukazo danku rabata" da d'anta ko?...,

saboda sabar sonkai irin naku to yaya kasani bazan ta'ba yarda su raba "mamana dayaronta" ba, wanda dama sunce natane Ita kad'ai bada d'ansu ba. "Nan dai yaketa fad'a yayinda suketa bashi hakuri inda *Abba* yasa baki dacewa lallai basu kyautaba to amma tunda hakan tariga tafaru yayi hakuri, cikin sauke ajiyar zuciya yace shikenan yaya nahakura komai yawuce.

*******
"Bayan komai yalafa sannan suka fad'i abinda yakarkare kawosu", *Abba* yace masha'allah hakan yayi kyau sosai Allah yasanya alkhairi, Alh Usman kaji abinda suke bukata ko?...eh yaya naji kuma nayi farinciki sosai dajin cewa *Bilal* yasamu lafiya, dan haka badamu insha'allah mamana zata koma d'akinta wanda nakesa ran cewa zatasamu farinciki me d'orewa na har abada,

tunda dai nasan tana kaunar mijinta shima kuma nasan yana kaunarata cike da farin ciki *Dad* yace tabbas haka ne suna kaunar junasu sosai. "Yace dan haka sai akula mun da'ita" domin itad'in tamkar tsokar jikinace, koma nace maka itad'in tsokar jikinace ko kad'an banason bacin rainta,

ko wancan lokacin sosai naji zafin abinda akai mata" musamman idan natuna da irin sadaukar da rayuwarta datayi dan farincikina data "yan'uwanta, sannan aka kuntata mata duk sai naji ba dad'i to amma kuma sai na dan gana hakan da kaddaranta ne saboda haka Allah yabasu zaman lafiya da kwanciyar hankali acikin auran nasu.

   "Cikin sanyin jiki suka amsa da ameen, sannan *Abba* yace to masha'allah yanzu yaushe kukeson takoma ko Alh Usman?... yace "eh yaya hakane sai kufadi ranan dazata koma, cikin murna *papa* yace a ah kufad'a dai...a ah mun yarje maku kufad'a yace to idan babu damuwa nan da kwana biyu,

*Abba* yace jibi kenan ciki dariya yace "eh yallabai domin mu bamuki bama ace mutafi da'ita yauba,  a ah jibi yayi kusa kasan mata da kintse-kintse dan haka abari ta kintsa idan yaso rana Ita yau sai takoma ko Alh Usman?...eh yaya hakan yayi dai-dai, sukace to shikenan Allah yakaimu akamar gobene agurin Allah.
Chapter 12 · 0% Book details