← Book details Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 18

Sashe 11

Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsanani zumud'i *Bulama* yace *Dad* ina kaga sis *Beenazar*?...wani kallo *Blue* yaimasa me cike da takaici, kafin duk *Dad* yabashi amsa *Blue* yayi sauri bashi cikin masifa yace malam bai saniba din d'an rainin hankali kawai, dana tambayeka ai cewa kayi "kai bakasan komai akan maganar ba amma yanzu dan rainin hankali kana wani tambayar ina akaganta" ko?...,

Shima cikin masifa yace eh! din malam aibakai na tambaya ba *Dad* nake tambaya kanji ko?.. tsaki mtww! *Blue* yai tareda dauke kai daga barin kallonsu, domin wani irin haushinsu yakeji. *"Dad* kam murmushi yai domin yasan wannan fad'an duk haushi yakeji saboda anyi masae auran bai sani bane,

sai kuma yad'afa kafad'ar *Blue* din tareda cewa my *Boy* karkaga laifin son nine nan, me laifin tunda ni nace kar wanda yafad'a maka komai, akan maganar auran kaji ko?...ba tareda yakalli *Dad* ba fuska murtine yace naji  *Dad* amma aidana tambayesa.
nuna mun yai baisan komai fa, to kayi kakuri kaji yarona?. kai ya gyad'a.

"Dai-dai lokacin da *Bulama* yasake cewa *Dad* yanzu sis *Beenazar* ta haihu?... fuska dauke da annuri yace kwarai kuwa son tahaihu, "yaronku" yana nan kyakkawan gaske tamkar d'an uwanka yayi kaki tsabar kaman dasukai, gashi d'an lukuti kamar d'an turawa yakarasa fadi fuska dauke da murmushi yana kuma Kallon *Blue* wanda yaketa cika yana batsewa.

"Cike tsanani farin ciki fuska dauke da murmushi *Bulama* yace kai! masha'allah, Allah yaraya *Dad* wai ina kaganta" ne sannan kuma meyasa kabari ta tafi bakutaho tareba munga beautiful boy dinmu eye *Dad*?..."Harara *Blue* yabanka masa tareda cewa ehe! laillai  saboda gata" mara zuciya, tayi maku halacacci ta hanyar auran mahaukaci d'anku" sai kuma kukai mata,

butulci ta hanyar koranta sannan dan tagansa yanzu sai tabiyosa saboda san kanku yayi yawa ko?....hararansa shima *Bulaman* cike da zolaya yace kaga malam bafa dakai mukeyin maganarmu ba, amma sai faman saka mana baki ka keyi.

"Cike da hassala yace nasa din kayi maganin hakan kaji ko?...yace kaga malam nidai kayimun shuru karnazo nabuge bakinka agurin nan, banza yai masa.

             "Hakan neyasa *Bulama* cewa uhum! da kasake magana agurin nan dakasani, *Dad* kyaleshi fad'amun ina kaganta"?.. murmushi *Dad* yai me kayatarwa sannan yace son naganta ne a *LUFHAT* shopping mall, cike da mamaki yace *Dad* to aimuma daga chan muke amma bamu gantaba kuwa, ikon Allah kenan aiko nikam achan naganta nan yafara tambayarsa sunyi magana me tace" masa meyace mata?...

     yace son batace mun komai ba asalima tsoro nagani yabayyana akan fuskarta, sannan kuma ta gudu. "Ido *Bulama* yazaro cikeda mamaki yace *Dad* tsoro kuma sannan ta gudu?..."eh kaidai, a ah *Dad* ko dai bata ganeka bane eye?...hum! son kenan wlh taganeni, abunda har  tana sake rungume d'anta tamkar nace zan kwace mata "shi yakarasa fadi, daidai lokacin da *Papa* yashigo bakinsa dauke da sallama.

"Suka amsa tareda yimashi sannun, ya amsa yana nufar gefen *Blue* ya zauna yana cewa son ya'akai ne cikin sanyi murya yace lafiya lau *Papa* sannun da dawowa yauwa son, yayinda *Dad* ya kallesa tareda cewa *Barr* harka dawo?..."eh *Dr* ya'akai ne naga kamar ran son dina abace, me kukai masa kaida "d'anka ne eye?...

   murmushi yai yace *Barr* laifin namune duka harda kai, saidai nawa yafi yawa dan haka kanema mun afuwa gurinsa.

         "Kallon *Blue* yai yace a ah wai haka ne son?...fuska tur'bune yace "eh *papa* ai hakan da akayi ba aimun adalciba gaskiya, yace to son kafin naji abinda akai maka kayi hakuri, sannan ina nema mana afuwa kaji?....yace ok *papa* nayi, yauwa son Allah yaimaka albarka ameen my *papa*. 

    "Sannan *papa* yasake cewa Dr me mukayima son dina ne?...cikin dariya yafad'a mashi komai, masha'allah Allah sarki *Beenazar* ta haihu?...eh wlh Barr d'anta" yana nan tamkar d'anka yayi kake, cikin murmushi yace madallah Allah yaraya akan sunna to ameen inji cewar *Dad*.

"Cikin bacin rai *Blue* yace to yanzu *papa* anyimun adalci kenan?.., ace aimun aure banida lafiya naji sauki amma ba'a fad'amun ba har gashi matar tahaihu, duk ban saniba saboda Allah fa?....kafad'arsa *papa* yad'an bubbuga cikin sigar lallashi.

    "Sannan yace am very! very!! very!!! sorry my son tabbas munyi maka laifi babba, saidai kasani duk dan muga farincikin kane mukai hakan kaji?...cikin sanyi murya yace to shikenan *papa* komai yawuce.

"Yauwa son nagode amma kasani lokacin dana dawo naji hukuncin da Dr ya yanke nakoran *"Beenazar* din, dacewa wai cikin jikinta banaka bane" ko kad'an banji dad'i ba wanda naso nanuna masa hakan ba dai-dai bane, to amma sai bai bani damar hakan ba shiyasa kawai nabi dashi ayanda yakeson.

"Yace *papa* aina fad'a mashi na basu kyautaba, *Dad* yace lallai nayi kuskure ina kuma sake neman afuwarka, itama *Beenazar* din zan nemi gafararta insha'allah sannan inason kamaida matarka albarkacin yaronku ko Barr?... "Yace tabbas hakan yanada kyu shine dai-dai, shidai *Blue* baice komai ba domin sosai yakejin haushin wannan al'anadin.

"Yayinda *papa* ya cigaba da cewa to yanzu dr yazamuyi mugano inda *"Beenazar* din take anan cikin garin eye?...yace to shine kuma abin tunani, gashi kuma batako tsaya kunyi magana ba balle tafad'a maka inda suke ko?...yace "eh wlh saidai naga lambar motarsu", yauwa to yalambar take?....

nan yakaranto masu, aikam nan take *papan* yace ah! to ai wannan lambar motar gidan alkali sasu ne, cike da farincikin*Dad* yace masha'allah shikenan sai muje da sauri *Blue* yace *Dad* wai me zakuje yine kuma?...yace a ah boy muyo maka bikon "matarka mana ko Barr?...yace tabbas, haba *papa* bayan kunsa keta.

           "Cikin dariya yace son aiwannan sakin bai sakuba tunda wani baya sakarma wani mata, dan haka insha'allah zamuje mudawo maka da "matarka kayi hakuri ka zauna da "Ita kodan albarkacin yaron ku" kaji?....ko kad'an azuciyarsa baiji son wannan matarba wacce ko saninta baiyi ba.

       "Amma yasan bazaya taba jayayya da mahaifiyarsa da mahaifinsa da kuma aminin mahaifinsa ba, domin sud'in mutanene masu matukar muhimmaci agaresa, dan haka cikin sanyin murya yace to *papa* duk yanda kukai shine dai-dai.

      "To shikenan yanzu mu zamu fara zuwa sannan kuma sai kuje ko Dr?..eh Barr hakan za'ayi, ko son yakarasa fadi tareda kallon *Bulama* yace "eh *Dad* hakan za'ayi, yauwa to Allah yai maku albarka suka amsa da ameen dai-dai lokacin da *Blue* yamike yakalli *Bulama* wanda  yake kallonsa yanai masa murmushi kasa-kasa, yace to malam aisai katashi muje ko?....

dariya yasaki tareda tashi yana fadin ok my _guy_ muje, suka fita inda suka bar su *Dad* suna tattaunawa akan yanda zasu tunkari gidan alkali sasu.

********
"Aban garan su *Beenazar*  kuwa da gudu *Bunayya* yacilla hanci motar kan titi, cikin rawar murya tace pls yah *Bunayya* kayi sauri mubar nan kaji?...cike da mamaki ya kalleta batareda yace komai ba, yacigaba da tukinsa yake cikin kwarewa saidai kuma had'eda sauri wanda yake nuna cewa shima yanada uzurin zuwa wani wurin ne.

"Yayinda *Beenazar* din sai sake kwakume *Baffa boy* takeyi ajikinta tamkar *Dad* yabiyota yakwaceshi, kirjinta kuwa sai aikin bugawa yake cike da tsoro sai leke takeyi tagefen wondon datake zaune, hakan yasa *Bunayyan* cewa sis *Been* _kasan cewar haka yake kiranta wani lokaci_ wai ya'akai ne?..naji kince nayi sauri mubar shopping mall din, yanzu kuma naga sai faman leka wondo kikeyi shin meke faruwa ne?...

      "Da sauri *Basma* tace yah *Bunayya*, wlh wani mutumine daga kawai sunyi karo shikenan kuma sai naga yabiyo mu, cike da mamaki yace kamar yafa "ya biyoku to yai maku meye"?...wlh yah ni bansani ba, but amman sai naga kamar sis *Beena* tasanshi.

Da sauri yakalli *Beenazar* din tareda cewa sis *Been* wai kinsan shi?..., kai ta gyad'a alamar "eh ok wanene?..me makon tabashi amsa sai kawai tafashe da kuka.

         "Hakan yasa yace Subhallahi sis *Beena* halan "wanene shi"?.., meyasa dan na tambayi wanene shi kike kuka eye?...cikin kuka tace yah *Bunayya* inajin tsoron karda yakwace mun yarona ne, cikin mamaki yace yakwaceshi saboda me to?... cikin kukan tace yah *Bunayya* "shine *Dad* mahaifin yah *Bilal*, fuska had'e yace ok no wander to akan wani dalilin zasu kwaceshi" bayan sunce ba cikinsu bane eye?...,

tace "eh duk dasunce hakan to amma yanzu zasuce" nasune tunda sunga yaimugun kamada yah *Bilal* din, dan haka zasu iya kwaceshi ni kuma gaskiya bazan iya rabuwa da yarona ba takarashe fadi tareda kara sautin kukanta.

             "Cike da tausayinta *Bunayya* yai fakin gefen hanya yakashe motar, sannan cikin sanyi murya yace kiyi shuru kidaina kukan, insha'allah bazasu ta'ba rabaki da d'anki ba kinji ko?...kai ta gyad'a alamar to sai da yatabbatar tayi shuru, sannan yatada motar suka nufi gida alokacin tuni bawan Allah *Baffa boy* yayi barci.

*****
Ahaka su *Beenazar* suka isa gida sukuku jiki bakwari dukansu, bayan *Bunayya* yasaukesu akofar gida yabud'e masu boot *Basma* ta kwashe kayansu sannan yatafi, inda sukuma kai tsaye suka nufi 'ban garen su *Beenazar* din suka shiga, da sallama *Ammu* ta amsa wacce kallo d'aya tayimasu tagane babu lafiya, tuni *Basma* tanufi ciki dan ajiye kayan dake hannunta.

"Cikin d'an faduwar gaba *Ammu* tace lafiya naganku haka?...takarashe fadi tana kurama *Beenazar* ido, tareda mika hannu takarbi *Baffa boy*, tana sake cewa me yasame shi?...murya asanyaye tace bakomai barci yakeyi ok.

"To ke kuma me yasameki kikai kuka har idonki yai kozai-kozai eye?...me makon tabata amsa sai tafashe dakukan wanda dama yana kusa, kallonta tayi tareda cewa hum! kedai kuka baya ta'bayi maki wuyar yi, to ya faruwar ne?...dai-dai lokacin da *Basma* tafito dan haka ita ce tafad'a mata abinda yafaru, duk dacewa taji faduwar gaba hakan bai hanata cewa shine kike wannan kukan?....

cikin shagwa'ba had'eda d'an turo baki tace *Ammu* idan suka kwaceshi" kuma fa?....,to sai me idan sun kwaceshi sai shikenan bazaki iya rayuwa ba komai eye?...dai-dai lokacin da*Abbu* yashigo, sannu sukai masa ya amsa tareda cewa a ah lafiya gaku tsayyaye chirko-chirko kamar kajin dasukai fad'a suka gaji, yakarasa fadi tareda sakin dariya itama *Basma* dariyar tayi,

Amma banda *Ammu* da *Beenazar* dake aikin sharan hawaye, kallonta yai yace a ah! wanene kuma yata'bamun uwata eye?...yana me ruko hannunta suka nufi falo zomuje naji halan fatimata ce ko?..., a ah *Abbu* ba ita bace to wanene? fad'amun.....

Bayan sun zauna sai tafad'a masa duk abinda yafaru, murmushi yai me kayatarwa tareda dafa kanta yace anzo gurin, sannan kuma ranan takusa zuwa wanda dama nadad'e ina jiran tazo dan haka karkudamu mamana, insha'allah babu wanda zaya rabaki da d'anki kinji ko?...
Chapter 11 · 0% Book details