← Book details Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 18

Sashe 7

Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yauwa son haka nakeso sannan magun-gunanka suna nan da "malam yabayar kayi amfani dasu, dan Allah karkayi wasa gurin amfani dasu kaji ko?... insha'allah *papa* bazanyi wasaba zanyi duk yanda akace nayi amfani dasu da izin Allah, yauwa to Allah yasa ameen.

"Sannan yamike yanufi gurin *Bulama* yaname yimasa kallo, me cike da kauna irinta aminan dasuka aminta da juna kwarai dagaske, cikin murmushi *Bilal* din yamikama *Bulaman* hannun inda shima yamiko masa hannun fuska dauke da annuri, jansa *Bilal* din yayi hakan yasa *Bulama* mikewa da sauri yana dariya suka rungume juna cike da kaunar junansu,

*Bilal* yana me shafa bayan *Bulama* yana fadin thanks so muchhh!, da abubuwan dakai mun my _guy_ u are the best friend in the world, I love u very very muchhh! Allah yabarmu tare cikin aminci dajuna, cikin murmushi *Bulama* yace ameen my best friend in the world.

********
"Sannan suka zauna dagan nan kuma sai suka fara fira, inda duk rabin firan akan rashin lafiyar *Bilal* din ne har aka kira sallar isha'i, sannan suka tashi sukaje sukai sallah bayan sun dawone sukaci abincin dare da kuku ya girka masu, sannan *Bilal* yace da *Bulama* pls my _guy_ tashi muje karakani babin saloon nayi gyaran fuska, yace ok.

"Daga gurin babin saloon din sai suka d'an zagaya gari inda sosai *Bilal* yaga abubuwa dayawa sun chanja, agarin zaria yayinda *Bulama* yake tayima firan abubuwan dasuka faru dashi, na irin shirmen da yaitayi na yarinta wani yai murmushi wani kuma yagyad'a kai yadinda can kasan zuciyarsa cike yake da tunanin "wanene yaimasa haka?...,saidai yakasa samun amsa kamar yanda *Dad* yakasa samun amsa.

"Sun d'an dad'e suna yawo sannan suka kama hanyar gida misalin karfe 11:00pm koshi saida *papa* yakira *Bulama* awaya yace" yazosu tafi gida dare yanayi sannan suka dawo, bayan yasauke *Bilal* sannan suka tafi gida.

"Inda suka bar *Bilal* din yana cewa *Dad* yabashi wayoyinsa yakira sweet aunty *Bebensa* yaimata surprised, ciki murmushi yamika masa wayarsa yana fad'in son gadai wayata ka kirata" dashi, amma wayoyinka suna chan abuja ajiye ni nama manta da jiya damukaje na dauko maka

   saidai idan kaje kadauko abinka but amma dai gaskiya yanzu kam sun zama Old monden, andaina yayinsu so yakamata kasamu sababbin yayi gasunan anata zubosu.

   "Cikin turo baki yace *Dad* dama ni kasan waya bawani dad'ewa sukeyi ahannanu naba nachanja, so dan haka bazanyi amfani dasuba kyauta zanyi dasu sim card dina kawai zan cire nasiya sababbin.

"Kai *Dad* yagyad'a yaname kallonsa cike da so da kauna yayinda yakejin wani irin matsananci farincikin, ganin yaronsa yadawo cikakken mutu. 

   "Shikam *Bilal* zama yayi me makon yakira aunty *Beben* kamar yanda yace" *Dad*, sai beyi hakan ba sai yafara kiran lambar *Mom* dinsa, murmushi *Dad* yai tareda cewa son kenan to ai tuni nafad'a mom dinka, yace ok *Dad* inason naji muryar tane yace ok aji lafiya sannan yamike yashiga ciki.

"Daidai lokacin da wayar *Mom* tashiga wacce ke zaune tazuba uban tagumi, wanda kusa kullum tana cikin tunanin halin da 'danta yake ciki sai taga kiran waya da lambar *Dad*, sai da gabanta yafadi cike da tashin ahankali ta dauka ciki zullumi  tareda tayin sallama saboda tsabar zullumi kartaji labari ba wanda takeson jiba, tace *Dr* ina fatan yaron naka yafarka cikin koshin lafiya kamar yanda kace" malam din yafad'a.

"Cikin shagwa'ba yace yesss! am ok assalamu'alaikum my lovel *Mom* the one and only, shuru tayi domin dai rabon dataji wannan nagartacciyar murya yau kimanin shekara daya kenan darabi harda wasu watanni, kuma acikin wannan tsawon lokacin babu ranan dazata fito tawuce batayi tunanin jin wannan murya me cike da natsuwa da kamalaba.

cike da shagwa'ba yasakeyin sallama tareda cewa *Mom* answer me now, u know I really miss u sweet voice ba?..., saida ta lumshe idon idan wasu hawayan farincikin suka zubo sharrr! akan kyakkawan fuskarta, sannan tace yesss! nasani u know nima nayi kewar wannan muryar taka me cike da natsuwa had'eda shagwa'bawa *Mom* da *Dad* da kuma aunty *Bebensa* ko?...,

    "Cikin murmushi yace yesss! my sweet *Mom* nakira nafad'a maki naji sauki, tace masha'allah *Dad* ka yafad'amin saidai namatsu na tabbatar da hakan sai kuma gashi naji alhamdulillahi yarona yadawo kamar yanda yake da, to bani labari yanda aikai sauki yazo cikin kankanin lokaci ko dayake duk *Dad* ka yafad'a mun yanda akai saidai hakan aikin ubangijinmu ne,

Wanda shine yake sanya cuta ajikin d'an adam alokacin dayaso yakuma cireta alokacin da yagadama batareda yai shawara dakowa ba. "

Kuma shine maji rokon bayinsa ayaukuma nasake gasganta hakan tunda gashi ya amsa addu'ata, konace addu'armu nida *Dad* ka da duk wani masoyinka akan yabaka sauki sai gashi yakarba alokacin damuka fitarda tsammani hakan, ko dayake ni akoda yaushe inajin araina dajikina cewa yarona zaya dawo kamar kowa, sai kuma gashi yau Allah yatabbatar mun da hakan alhamdulillahi! alhamdulillahi!! alhamdulillahi!!! Allah nagode maka Allah ka karama annabinmu daraja (SAW), inda suka karasa salatin tareda shi.

Sai kuma kawai yafashe mata dakuka wanda kanajinsa kasan nashagwaba ne, me cike da kaunar mahaifiyarsa da sauri tace a ah! wai shin yarona besan cewa yanzu yagirma bane?..,cikin turo baki yace *Mom* idan ina gabanki da *Dad* ni yarone, cikin dariya tace hakane to amma me makon naji kana farincikin kasamu sauki sai kuma naji kana kuka eye?....,

cikin kuka yace hakane *Mom* nayi farinciki da samun lafiyata nakuma godema Allah da ya azurtani da hakan, zan kuma cigaba da gode masa har karshen rayuwata, saidai ina kukane saboda dalilin rashin lafiyar tawa.

"Tace yarona kenan tabbas Allah abin godiya ne akowane hali d'an adam yatsinci kansa, dan haka kayi shuru kafada mun meye dalilin rashin lafiyar taka da haryasa kake kuka alokacin da yakamata kayi farin ciki eye?...shuru yayi cikin sanyin murya yace haka ne *Mom* amma bakijin dalilin rashin lafiyar tawa bane?...tace a ah son dalilin kenan shine Allah yasa maka cuta yanzu kuma yayaye maka,

da sauri yace eh *Mom* amma ai ance yimun akai tace kul! nasake jin hakan yafito daga bakinka, kasa aranta Allah shine mesama bawa cuta kuma shike yayema bawa kaji ko?... ahankali yace to *Mom* yauwa tareda sake tambayarsa to yajikin?...,

yace alhamdulillahi to masha'allah Allah yakara lafiya nan sukai magana tsakanin d'a da uwa sannan sukai sallama, akan bayan kwana biyu yana nam zuwa abuja yaganta sannan yakira lambar aunty  *Bebe* zuciyarsa cike da farincikin.

*Abuja*
********

"Aban garen aunty *Bebe* kuwa tin bayan dasu *Dad* suka dauko *Bilal* suka taho dashi, hankalinta yakasa kwanciya musamman dataji cewa aiza ayimasa magani Islamic, hakalinta yake atashe domin tana da tabbacin idan har zunje gurin malamai na kwarai, to tabbas zasu iya karya duk wani asirin datayi masa kuma tabbas zaya warke ne.

"Dan haka suna tafiya data koma gida tashiga toilet tadauki tukunyar tsafinta dan tasake birkice  kwakwalwar *Bilal*, cikin tsananin confidence nacewa zatayi nasaran akanshi  tafara sirkulle magana kamar yanda tasaba, saidai wani abin mamaki shine rawa hannunta yakamayi inda tukunyar takeson fad'uwa, kamar yanda kwanakin baya takeyi mata  aduk lokacin data d'auko zatayi tsafinta.

    "Hakan yasa cikin matsananci tsoro da faduwar gaba me tsanani, ta ajiye tukunyar jikinta yana wani irin bala'in rawa kallon tukunyar take cike da mugun tsoro hade' da matsananci mamaki, tana tunowa damaganar boka dungu nacewa duk ranan da tabari tukunyar nan tafashe tofa aranan dukkan asirinta zaya tonu.

Hakan yasa tayi sauri ajiyawa tareda maida ita ma'ajiyarta, tafito daga toilet din jikinta sai rawa yakeyi da sauri tashirya doguwar rigar atamfa baka, tasa gyale fari tareda rataya jaka tadauki key mota tafito falon inda ta'iske duka yaranta suna kallo, da sauri Jiddo ta kalleta cike da mamaki tace mom yanzu fa kika dawo sannan kuma zaki tafi to ina kuma zaki?...,

cikin tsawa tace Jiddo dani dake waya ajiye wani ne wai?....cikin d'an turo baki tace mom kece kika ajiyeni, to shine duk sanda zan fita saiki tsareni da tambaya eye?...ni sa'ar kice?...cikin sanyi tace a ah mom, to bansan haka nan kinji ko?...to mom Allah yabaki hakuri saidai wlh mom kirage yawo *Dad* yafara jin haushin yawan fitar da kikeyi.

Tsaki taja mtww! tareda fadin ke!ni banasan surutun banza kinji ko?...cikin turo baki tace to mom ina zakije?...fuska hade tace unguwa zani amma bazan da'de ba, idan Dad ku yadawo kice yanzu zan dawo, kai kawai ta gyad'a Ita kuma tafita da sauri.

    "Tana kokarin tada mota sai *Dad* yakira wayarta da sauri tad'aga bayan sun gaisa take tambayarsa yajikin lil *Boy*, cike da farincikin yafa'a mata abinda yafaru wato ankira malam yaima *Boy* addu'a yai barci, yace" idan yafarka insha'allah zaya tashi dasauki tamkar be taba ciwa ba, sannan yafada mata cewa malam yace" yimasa akai, sosai tanuna farincikinta najin zaya samu sauki da kuma alhinin wanda yaimashi.

"Sannan sukai sallama inda hankalinta yai mugun tashi dajin wannan mummunan labarin, aikam take ta tayarda mota jikinta yana bala'in rawa, kai tsaye gidan kawarta taje me suna Haj kulu ta labarta mata abinda yafaru aikam zama be ganmu ba, dan haka suka bazama gurin neman bokaye.

saidai duk inda sukaje basu iske bokan ba haka dai suketa fafutukan neman hatsabibin bokan dazaya mata aiki akan kada Allah, yaba duk wani malamin dasu *Dad* zasu kira yai nasaran warkar da *Bilal* din.

"Ahaka dai har kusayi nasaran samun wani shahararran hatsabinbin boka, wanda yake aiki tamkar yankan wuka saidai koda sukaje sun iske mutane sunyi mashi yawa, hakan yasa yasallami mutane akan cewa suyi hakuri bazaya samu ganinsu yauba saidai yai masu alkawari suzo gobe, aciki harda su aunty *Bebe* badan tasoba suka tafi.

Tana kokarin shiga gida taji wayarta yana kara koda ta dauko taduba sai taga lambar *Dad* hakan yasataji mugun faduwar gaba saurin dauka, tana fadin good evening *Dad* saidai jin natsatsiyar muryan me cike da kamala had'eda tsananin kwarjini, wanda rabon dataji ta andauki lokaci sai yau hakan yasata sake jin muguwar faduwar gaba. har wayar tana kokarin faduwa daga hannunta, da sauri tasake rikewa da kyau.
Chapter 7 · 0% Book details