Sashe 18
Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Koda su *Dad* suka isa da kyar suka ganeta wanda ita ce dakanta ta tabbatar masu ai Ita ce, banda haka inda wani yafad'a masu to da bazasu taba yarda ba duk da hala saida *Blue* yace no *Dad* wannan ba aunty *Bebena* bace, Cike da tsanani nadama wacce za'a iyacewa marar amfani tace nice Bil boy, da sauri yamatsa gurinta yakura mata ido yana kallonta sosai halittarta yachanja tamkar wata dodanniya, yayinda miyau sai zuba yake takarka taccan bakinta gawani wari-wari datakeyi sannan wasu irin tsutsotsi sai zubowa suke takasanta.
Cikin bala'in tashin hankalin *Blue" yace wayyo na aunty *Bebe* wannan wani irin hatsari ne haka?...magana tafarayi dai-dain da *Bulama* da *papa* suka shigo, inda take cewa Bil boy alhakin kane yakamani akan abubuwan danayi taimaka kai da *Dad* harda *Mom*, dakuma mijina uban 'ya'yana Cike da mamaki *Dad* yace *Bebe* me kika aikata mana?...nan tafad'a masu dukkan abinda ta aikata babu abinda taboye har tarayyar datake da bokaye tana matar aure...da kuma wannan tafiyar dasukai wanda duk dantaga bayan *Blue* din ne.
Wani irin tsalle *Blue* yai tareda komawa gefe yana kallonta, sai kuma yadafa kasan da dukkan hannusa yasaki kara me cike da tsanani bakin ciki da bacin rai wanda yasa idonsa sukai wani irin jajir, jijiyoyinka shi sukai rud'uru'u sannan yawatsa mata wani irin Harara me cike da tsanani tsanarta akaro nafarko dayaji hakan iya tsawon rayuwar dayai zuwa yanzu, sannan cikin bacin rai yace nima natsaneki ko lahira bana fatan Allah yahad'ani dake kuma ban yafe makiba muguwa maciya amana, azzaluma macuciya fasik....sai yafashe da kuka tareda juyawa yafita da sauri inda *papa* yace da *Bulama* yabishi da sauri, karce zayai tuki dakanshi.
*Dad* kam tsaye yake 'kikam tamkar gunki yakasa cewa komai, sosai yake ganin abun kamar almara wai *Bebe* ta akata dukkan wannan mugayan aikin ga d'an uwanta, yayinda itakam sai kuka take me cike da nadama *papa* ne, yace da'ita keko meyasa kika aikata hakan ga mutanan dasukai matukar abinta dake eye?...cikin kuka tace *papa* san zuciya, yace bacinta tabbas baki kyautama kankiba gashi nan takaiki tabaro.
*Dad* yakalla yana kokarin magana *Dad* yarigashi dafad'in Barr in badan ni da hannuna nakarbi haihuwar yarinyar nan ba, to danace anchanja mun Ita ne to amma ko yanzu ina zargin Ita din bajinina bace da sauri yace haba *Dr* karka sheganta yarka mana dakanka, da sauri yace wannan din ai shegiyarce duk d'an halak bazaya ta'ba aikata wannan mugun halinba, dan Allah *Dr* kadaina fadin irin wanyan nan maganganun, cikin baci rai yace *Barr* nafad'a kuma kinji dai nace bai yafe makiba ko?...to nima ban yafe makiba dan haka gobe kiyama zakiyi bayani, abinda kika aikata sannan yasakai yafita zuciyarsa na 'kuna.
Fitar *Dad* tayi dai-dai da wani irin shakkuwa da tafarayi, da sauri *papa* yamatsa kusada ita yanai mata sannu kai ta gyad'a kafin tace dan Allah yanema mata gafara agurin *Blue* da *Dad*, yace karta damu insha'allah chan kuma sai yafara kakari da sauri yafara karanto mata kalmar shahada, sai duk yanda yaso takarba abin yafaskara har rai yai halinsa, ba tareda bata lokaciba aka bashi gawarta yanufo gida.
Inda ya'iske *Blue* saboda tsabar bacin rai har wani dishi-shi yake gani amma wai ahakan yake kokarin tayarda mota saidai yakasa, hakan yasa *Dad* yakarbi key yamikama *Bulama* dan yajasu tunda shima ayanda yakejinsa bazaya iyatukin ba, suna isa gida *Blue* yabud'e mota yafito kai tsaye part dinsu *Mom* yanufa, domin ita kawai yakeson gani aikam tana falo itada *Beenazar* yashiga yafad'a akan jikinta tareda sakin wani irin mahaukaci kuka, yana fadin *Mom* mena tsare mata haka arayuwa datayi mun mugun tsana eye?...
*Mom* kam cikin tashin hankalin tace wacce?...bai iya bata amsaba, sai *Bulama* ne da suka shiga shida *Dad* yafad'a mata dukka abinda yafaru, yayinda *Dad* yakoma gefe yana sauke ajiyar zuciya, itakam *Mom* batayi mamakin jin hakan ba tunda abayyane tasha nuna mata tsanani kiyayya dan hakuri kawai tabasu, yayinda tace da *Beenazar* tashi ki kama mijinki kije ki lallashesa nima zan lallashi nawa, cike da kunya takamashi suka fita zuciyarta cike da mamakin aunty *Beben*.
Isar say *Dad* bada wani dad'ewa ba *papa* ya'iso da gawarta, sosai *papa* yayima *Dad* da *Blue* nasiha hakan yasa suka yafe mata, dan lokaci kankani cikin lokaci kankanin *Mom* da mama sukai mata wanka batareda nuna kyamar gawarba, wacce kokad'an batada kyaun kallo suka shirayata akayi mata sallah aka kaita gidanta na gaskiya.
Bayan sadakar bakwai *Blue* yasa akanemo Jiddo inda aka ganta d'akin wani saurayi duk ta lalace gwanin tausayin, asibitinsu aka kaita inda aka duba lafiyarta tareda yimata wankin ciki, sannan aka dauko malamin dayai masa addu'a lokacin da bayada lafiya, itama yaimata cikin sa'a itama tawarke tayi kuka sosai daji abinda yasame ta tareda mutuwar Mom dinsu.
Kasan cewar *Dad* dinsu Jiddo marayane ba uwa ba uba sai dangin ubanshin, sukuma yasan bazasu rike masa suba saboda irin walakaci da aunty *Beben* tayi masu, dan haka yanemi alfarman da yabarsu nan hannun *Mom* har yayi aure sai yakarbesu tace bakomai ai yaro nakowa ne, dan haka tarikesu inda tafara basu tarbiyya me tsabta wanda mahaifiyarsu bata basuba.
Aikam sai gashi wani irin nutsuwa yashigesu tamkar basuba, haka komai yacigaba da tafiya gwanin sha'awa agaresu tuni rayuwarsu ta sauya, hakan su *Beenazar* sosai suke gudanar da rayuwarsu me cike da zallar kaunan junansu da kwanciyar hankali, tuni aka yaye *Baffa boy* wanda dakanshi yadaina shan nonon wannan kenan.
*Bayan shekara uku*
Raran wata lahadi da misalin karfe goma shad'aya nasafe *Beenazar* ce naga tafito daga d'aki tu'kui-tu'kui da tsohon ciki, sanye take da doguwar rigar atamfar english blue da ratsin fari, tayafa farin mayafi tareda takalmi fari flat wanda yaso yad'an matseta kad'an saboda d'an kumburin da kafafunta sukai, sosai tazama babbar mace wance kallo d'aya zakai mata kagane tuni wayewa yazauna jikinta.
"Ahankali take takawa tana yamutsa fuska tareda rike kwan-kwaso, bayan *Blue* sanye yake da riga marron color da wando na jeans black kashi sanye da facing cap baka, wacce batayi nasaran rufe lallausan suman kanshi ba.
Rungume yake da kyakkawan Baby me kamada *Beenazar* sak! harda chocolate color fatar *Beenazar* duk baby tad'auko, wacce akasama sunan *Mom* wato hauwa'u sai suna kiranta *Basoo* yayinda *Blue yake kirata da *Sona*, kasan cewar yana matukar jida Ita tako'ina gata sweet mom gata darling heart dinsa, so bai had'ata dakowa ba duk bata wuce shekara d'aya da rabi ba sanye takeda wata jar rigar kanti me kyau, da d'an karamin hijab dinta wanda ake kira half sunna wanda yafito da kyakkawan goshinta da gefe-gefen fuskarta dake kwance da yankananan suma, yatsunta biyu sanye cikin baki sai tsotso takeyi abinta hankalinta kwance sai sake lafewa take akan kafad'ar *Daddy* ta datake masifar jidashi.
Yayinda yake rikeda hannun *Baffa boy* wanda yaketa aikin zuba surutu tahanyar antayo masa da tambaya *Daddy* yauma zamuje gidan momina ne?...yana nufi *Basma* kasan cewar tahaihu jiya akai suna yanzu yaranta biyu dame sunan *Papa* da me suna umma.
Cike da yace eh boy zamuje gidan mominka amma sai anjima kaji?...yace to dai-dai lokacin da *Beenazar* take kokarin zama amma takasa saka makon rikewa da bayanta yayi hakan yasa tace wayyo *MAJNUNINA* bayana zaya karye, _kasan cewar haka yace taringa kiransa saidai batayin hakan sai lokaci-lokaci_ Da sauri yace sorry queen nace kitsaya na dubaki amma kin kiya, cikin shagwa'ba tareda turo baki tace banaso tunda jiya nima saida nace kayi karkayi kakiya saida kayi.
Dariya yai cikin sigar lallashi yace to yihakuri bazan sakeba harsai bayan kin haihu kinji tawan?...cikin turo baki tace to, yauwa to yanzu tashi muje nakaiki Dr Luba tadubaki tunda naga ai edd dinki kamar yaune ko?...kai ta gyad'a dai-dai lokacin da mararta tayi wani irin hautsinawa, aiko da sauri tafurta ya salam wayyo marata sannu bari nakai su *Sona* nazo mutafi, kai ta gyad'a.
Suna isa asibintin aka tarbesu da sauri kasan cewar sosai nakuda yataso, inda ko cikin sa'a batareda tayi dogon nakuda ba tahaifo kyakkawan katon d'anta me kama da ubansa, kalar fatane kawai yad'auko irin nata bayan tahuta aka sallamesu kasan cewar batajin ciwon komai, ranan suna yaro yaci suna *Dad* wato Lawai sai suna kiransa da *Barrak* haka rayuwarsu tamika gwanin sha'awa sosai *Blue* yake so da kaunar *Beenazar* tamkar yamaida ciki.
Tammatttt
_Ina mika godiya me tarin yawa ga d'inbin masoyana aduk inda kuke afadin duniya alkhairi Allah yakai maku_.
Alhamdulillahi anan nakawo karshe wannan littafin nawa me suna *ZAUJUN MAJNUN* na biyu, ina rokon inda nai daidai Allah yabani ladani nida masu karantawa inda nai kuskure Allaha kayafe mana, ameen sai mun had'u sabon alittafina idan Allah ya yarda me suna *KYANDIR* (wato me kyan banza) kai daga jin sunan littafin kasan akwai magana aciki, da haka insha'allah sai yafi wannan fad'akarwa, da nishad'arwa tareda soyayya me tsayawa arai, yana kuma dauke da tsantsan yaudara cin amana da hassada da kyashi, masu tambayar *Taseeri* document ya kammala dan haka kune meni a lambar wayana 08161850024 sai najiku nagode.
*MEENAL or LUFHAT CE*
_ALLAH kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_