← Book details Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 18

Sashe 8

Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    "Cikin rawar jiki bakinta yana rawa cikin dariyar yake tace hey my lil *Boy* yakake?.. ina fatan kasamu lafiya kamar yanda *Dad* yace wai wani Malami yace?...daga chan yace yess my sweet aunty lafiya lau nake, naji sauki, kuma *Dad* yafada mun duk abinda yafaru dani, thanks nagode sosai da kulawarki tareda irin kaunarki agareni nima ina kaunarki Allah yakarasa mama dankon zumunci.

cikin dariyar yake tace hey my boy kaifa d'an uwana ne dan haka kardamu duk abinda nayi maka kaina nayima, yanzu ina fata babu inda yakeyi maka ciwo daiko?...yace a ah sis kawai dai banajin karfin jikina ne, tace karka damu ahankali zaka dawo normal kaji ko?...to my sweet aunty nagode, yauwa zanzo gobe naganka ok to sai kinzo sannan yakashe wayar zuciyarsa cike da kaunar yar uwansa.

"Yayinda Ita kuma taja wani mugun tsaki mtww! yayinda zuciyarta cike da tsanarsa" cike da bakin ciki tace banza, harda wani cewa ina kaunarki  Allah yabar zumunci wawan banza nikuma bana kaunarka, shiyasama natsaneka  kuma sai naga bayanka sannan tashiga cikin gida tana sake jin tsanarsa aranta.

*Bayan sati biyu*
*******

  "Aban garen su *Beenazar* kuwa komai yana tafiya dai-dai gwani sha'awa suke rayuwarsu, tasakeyin girma sosa kasan cewar tuni cikinta yashiga watan haihuwa dan hakane ma yafito sosai, wanda alissafin mada sukeyi har yafara wuce lokacin haihuwar hakan yasa ko dayaushe cikin shiran haihuwar suke.

    "Yau Laraba tin da *Beenazar* ta tashi takejin maranta yanai mata ciwo, amma haka ta daure suka tafi school kasan cewa tanada lecture safe, saidai kachar suka gama lecture tafito takira *Bunayya*  kasan cewar shima yanada lecture, inda ko tayi sa'an yana fitowa tasa meshi daga jin muryarta yasan ba lafiya da sauri ya'isa gurinta tuni har tafara gumi,

yace lafiya ciki rawar murya tace yah *Bunayya* marata ke ciwo kamar zata fashe da sauri yace Subhallahi! to ko dai haihuwarce?..., tace yah* *Bunayya* ban saniba ok to tashi muje gida, nan yabud'e mata mota tashiga shima yashiga yaja suka tafi.

  "Gudu yake sosai saboda tuni har tafara fita hayyacita sai murkususu takeyi, tana salati tareda kiran sunan *Ammi* da *Abbu* dashi kansa *Bunayya* tana cewa zata mutu, hakan yasa hankalin *Bunayya* tashi sosai tunk kuma yagane cewa haihuwa zatayi,

domin yaji su umma nafadi takusa haihuwa dan haka cikin sauri yace sis *Beenazar* haihuwa fa zakiyi dan haka bari muwuce asibiti kinji ko?.., kai tagyad'a cikin tsananin wahala aikam *Bunayya* yana rufe baki  faya tafashe, dan hakan cikin sauri juya kan motarsa zuwa asibiti.

Cikin sauri akazo aka tarbesu inada kaitsaye dakin haihuwa
aka nufa da'ita, tareda bukatar kayan haihuwa yace to daga school yasuke, amma yanzu za'akawo sannan yakira waya gida yafad'a hakan yasa cikin lokaci kankaci sai ga Umma  direba yakawota, tareda tarkacen haihuwar kasan cewa *Bunayya* yafad'a nan yafad'a mata cewa sun shiga da'ita dakin haihuwa tace to tareda komawa gefe tana addu'ar Allah yadaukesa lafiya.

*****
Duk wani kokarin da likitoci sukai dan ganin *Beenazar* tahaihu dakanta abin yaci turo, har yamma gaba d'aya ta galabaita, hakan yasa sukace dole sai anyi mata c s dan haka tuni Umman takira *Ammu* da *Abbu* harda *Abba*, nan *Abbu* yasa hannun inda cikin kankanin lokaci akashiga da'ita aiki batareda bata lokaciba, aka ciro mata kyakkawan katon d'anta me kama da ubansa" sak *Bilal* tamkar yayi kaki ko kad'an be dauko *Beenazar* ba.

  koda Umma shi taba *Abba* yaimasa addu'a sannan yaba *Abbu* yana ganin tsananin kamar dayai da ubansa yace alhamdulillahi, sannan yaimasa Addu'a yaba *Ammu* itama tayi masa addu'a sannan tamikama *Bunayya* shama addu'ar yaimasa cike da so,

yaba*Basma* kasan cewar tuni itama tazo  aikam cike murna ta rungumeshi sai zuba mashi miliyoyin kiss take cike da kaunar yaron dataji yadarsu mata arai, sosai tarike shi da kyar tabasu *Bassam* suka dauke shi aikonsai fad'i suke lah! wlh yana kamada yah *Bilal*.

"Kwanan *Beenazar* hudu a asibiti aka sallameta inda kai tsaye gidan Umma *Ammu* tace akaita kasan cewar itake kulada ita acan asibitin, dan hakan ta ko yanzu ta cigaba da kulada ita har tayi arba'in sannan takoma gurin *Ammu*. 

Ranan suna yaro yace sunan *Abbu* wato Usman, dan haka bayan suna sai Umma ta cigaba da kulawa da *Beenazar* da d'anta kamar yanda *Ammu* ta bukata, inda suke kiran yaron da *Baffa boy* wanda kafin suyi arba'in tuni sunyi wani irin kyau da 'kiba gwanin sha'awa,

musamman *Baffa boy* da babu abinda yadamesa illa idan yai kuka abashi abincinsa, sabani *Beenazar* data d'an fad'a kad'an saboda tunanin halinda uban d'anta yake ciki, wanda akullum so da kaunarsa yake sake shiga ranta had'eda tausayinsa.

Hakan yasa tun bayan rabuwarsu bakinta be taba daina yimasa addu'ar samun lafiya ba, yayinda cikin zuciyarta takejin so da kaunar *Baffa boy* fiyeda da tunanin me karatu wanda akullum  kamanninsa dana mahaifinta suke sake fitowa wannan kenan.

*Bayan wata biyar*
******

Muje zuwa

*LUFHAT CE or MEENAL*

_Allaha kasa mucika da imani ameen ya rabbi?_

🎍🎍🎍🎍
     🎍🎍🎍
          🎍🎍
               🎍
🎍 *ZAUNJUN MAJNUN* 🎍
(Miji mahaukaci)

*BOOK 2* Page

2️⃣6️⃣to3️⃣0️⃣

🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍

WRITTEN BY

🎍 *AMINA UMAR FARUQ* 🎍

OR

🎍 *MEENAL*🎍

Marubuciyacer

*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUNJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*TASEERI*
and now
*ZAUNJUN MAJNUN part 2*

_SADAUKAWAR GA_

Iyayena abin alfarina ina godiya bisaga tarbiyyar dakukai mu, dan haka ina rokon Allah yasaka maku  da alkairi yakareku daga sharrin mutum da aljani, ubangiji yasa kugama da duniya lfy ameen ya rabbi.

Wannan littafin na kudi ne akan farashi me sauki, 200 naira only zaku iya turo kudin tawannan account no 0047769671 Amina Abdullahi A., sai kuturo shaidar ku ta hanyar yin screenshot sannan kuturo ta wannan lambar 08161850024, sai naji ku.

✍🏼

_Bismillahirramanirraheem!_

     *Abuja*

""''''''"""""BAYAN wata biyar din dasuka wuce wanda acikinsu abubuwa dayawa sun faru masu dadi da marasa dadi, kamar aban garen aunty *Bebe* kuwa marasa dadine sukayi mata dumu-dumu, domin kuwa tsawon watanni nan dasuka shud'e duk abinda tasa agaba batayi nasara akanshi, duk wani boka da malamin tsubbun da yakwana yatashi agarin abuja inda taji labarainsa" to saida sukaje gurinsa da kawarta inda take fadin bukatarta, na asake nakasa mata bawan Allah *"Bilal* saidai kuma har yanzu takasa samun nasara akansa".

"Saboda karfin addu'o'e dake fitowa ta'ban garori dadama, daga gurin masoya da malamai dan hakan har yanzu takasa samun nasaran, gashi kuma duk wayanda sukaje gurin bokayan da malamai tsubbun anyi masu aikin sun kumayi nasara amma banda "Ita, dan hakane yasa duk tazama wani iri, wanda idan ka kalleta dakyau zakaga kamar atsorace takeda mutane.

      "Sannan ga wasu irin mugayan mafarkai datakeyi masu matukar tsoratarwa, haka zalika har yanzu idan tadauki tukunyar tsafinta dan tayi tsafin saidai bayayi domin kuwa abin yacitura saboda har yanzu tukunyar rawa take sosai, wanda idan har tamatsa dole sai tayi tsafin kamar yanda takeyi ada chan, to ko tabbas tukunyar zata tarwatse ne.

"Gashi kusan kullum saiyi mafarkaiyan nan wanda aciki akesake tabbatar mata, da idan har tayi gangancin BARIN tukunyar nan tafashe to tasani komai nata yazo karshe, danka tadaina daukar tukunyar bawai dasunan tahakura tadai tsafinba, saidai dankwai tabarta tukunyar tahuta har zuwa tsawon wanin lokacin domin tunaninta yabata cewa ai tukunyar tagajine.

         "Ga wani abu dayafara bata tsoro koma yake bata wato shine, yanzu idan yaranta sunyi badai-dai ba tayimasu fad'a ga mamakinta sai suma suna mayar matada fad'an had'eda rashin kunya, musamman ma Jiddo yanzu sosai takeyi mata rashin kunya tun tana mamakin abin har yakoma bata tsoro sosai.

"Dan hakan duk tazama sukuku, saidai acikin zuciyarta mugun nufin nan nata yana nan akan sai taga bayan dan uwata, bawan Allah *Bilal* wanda yakemata sahihiyar kauna ta uwa daya uba daya domin shi betaba daukarta yar uba agareshi ba, yayinda  itakuma take masa matsananciyar kiyayya irinta wasu 'yan uban dasuka tsani abokan haihuwar su" ba gaira babu dalili wannan kenan. "To Allah yasawake, yakuma hadamu da yan uwan da suke kaunarmu tsakani da Allah ameen.

*Zaria*

*******

"Yayinda aban garen *Bilal* shima hakan abin yake wato abubuwa dayawa sun faru ta'ban garanshi sosai, masu dadi da masara dad'in saidai kuma shikam agurinsa masu da'din sunfi yawa, wanda sune suka baibayesa.

"Domin kuwa tuni yasamu lafiya fiyeda tunanin me karatu, kasan cewa kokad'an  baiyi wasa gurin amfani da magungunan da aka bashiba tareda yin addu'o'en da yasani, na neman tsari daga sharrin mutum da na aljan, dakuma wasu addu'o'en wanda malam yabashi yaitayi sosai hakan yasa yaji sauki matuka, yai garau abinsa.

      "Inda yadawo kyakkawa _guy_ abinsa kamar yanda yakeda harma yaso yafida yin kyau, saboda harda wani kiba yakara inda farinsa yasake fitowa sosai gashin kannan nasa sai sheki yake yanasake cukurkud'ewa, saboda tsabar gyara dayake mashi hakanan sajen nan nasa yasake kwantawa luf-luf, afuskar me cike da kwarjini da annurin ibada, hakan yasa sai wani shanin takeyi gwanin sha'awa idanka kallesa sau d'aya saika sake kallonsa saboda sha'awa.   

"Tuni yacigaba dayin harkokinsa na business dinda sukeyi shida *Bulama* wanda sosai suke samun riba, har suna shirin sake bude wani kamfani saboda bakaramin ma'kudan kud'ade suke samuba, dan haka suka zama wasu irin youngers alhaji kasan cewar kota'ina kudin shigo masu yake tunda tuni *Dad* da *Papa* sun bud'ema ko wani tabkeken pharmacy, agarin abuja.

     "Wanda suke ajere da juna guda ana admitin din mutane idan basu da lafiya, guda kuma anzuba magunguna masu kyau da'ake odarsu daga kasar wanje, duk da basu *Bilal* din ne ke zama ba wasu aminttatun mutanansu suka zuba, hakan bai hana ana tururuwar zuwa kai mutane ba tareda siyan magunguna saboda sauki dasukeyi, sosai suke tausama talakawa saidai duk bayan sati daya ko biyu suna zuwa, suga yanda komai ke tafiya kuma alhamdulillahi komai yana tafiya dai-dai.

       "Yayinda hakan bakaramin sake bakanta ran aunty *Bebe* yaiba shikam *Bilal* bai masan tanayiba, tunda azahiri bata nuna masa komai ba sannan itakanta babu abinda *Dad* yarageta dashi, balle tace" ai *Dad* komai shi yakeyi mawa Ita baya yimata gashi sosai yake kulada yaranta ta hanyar yimasu hidima, wanda ko Dama chan haka yakeyi masu to amma dai duk da haka zuciyarta tana nan cikeda tsanarsa, dakuma bakin ciki da kyashin abinda *Dad* yake masa.
Chapter 8 · 0% Book details