← Book details Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 18

Sashe 16

Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Da sauri yasake cewa yauwa kafin nan bakaga wata black beauty tashiga ba?...,yace uhmm! naganta mana "matar d'an abokin *Dad* ce tun jiya da yamma sukazo lokacin kafita, tazo gaida *Dad* ne, najima yace sati daya zatayi saboda mijin nata yayi tafiya, da sauri yace what! wai da gaske ne ashe abinda *Dad* yafad'a?....yace Oh! baka yarda ba kena?....pls nidai kafito gani nan ina jiraka muyi magana ok yakashe wayar yana sakin murmushin zolaya..

Tsaye ya iske *Blue* sai safa da marwa yakeyi, cikin d'an tashin hankali yana ganinsa yanufe shi yana cewa pls my _guy_wai Ita dince matar d'an abokina*Dad*?...eh mana, cike da bugawar zuciya yatura hannun cikin lallausan suman kanshi yace gaskiya akwai matsala?...cikin dan mamaki yace matsala kamar yafa?...,yace saboda "ita ce my dream queen din danake fad'a maku" da sauri, *Bulama* yace me?...tare da d'an zaro ido alamar tsoro.

Yace wlh kuwa kuma gaskiya saidai ayi wacce za'a domin nidai wlh ina kaunarta" fiyeda tunaninka, dan haka dole "yasaketa na aura saboda wlh bazan iya hakuri da Ita ba....."Baki da hanci yasaki yana kallonsa kafin yafurta, shin _guy_ kasan me kake fad'a kuwa?...fuska had'e yace nasani mana, yace ok to Allah dai yataimake mu ba rashin lafiyarka bane yadawo.

Cike da masifa yace malam kamar yafa meka kenufi eye?... fuska had'e yace ina nufin indai baka sake dawo majnuniba, domin sai mahaukacine kawai zayayi abinda kake kokarinyi yanzu wato yace" asaki mata ya aura ina kata'ba ganin anyi haka eye?...cikin 'kufuluwa yace malam niba mahaukaci bane da hankalina kuma wlh tunda ina sonta" dolene "yasaketa na aura kagane ko?...yace tabd'ijam eh lallai nagane sosai makuwa saidai yaro kasani kana ruwa tsubul kuma kusada, so kaga tafiyata nan domin naga kamar bakada aikin yi nikam dai inada abinyi yawuceshi yanufi part din *Dad* yana dariya kasa-kasa,

  Cike da mamaki *Blue* wai asaki mata ya aura humm! wannan ma bayada hankali ko awani garin akeyin haka oho, Allah sarki sis *Beena* Allah ba azzalumin bawa bane saidai wanda yazalunci kansa, yau dai ga yah *Bilal* dinki Allah yakama makishi yana kokarin zama *MAJNUN* akan so da kaunarki koma nace yazama, yakarasa  fad'i da kyalkyalacewa da dariya dai-dai lokacin da yashiga falon *Dad* inda ya'iske yanata yima *Baffa boy* wasa suna dariya.

*******
"Nan yafad'a mashi yanda sukai da *Blue* din aiko nan sukai tayi mashi dariya, sai gashi yashiga fuska had'e inda sukuma suka gintse dariyar tasu, *Bulama* yakarbi *Baffa boy* yada fadin *Dad* kawoshi nakaishi gurin mom dinsa, yafita yanai masa wasa ta hanyar challasa sama yana cha'bewa shikuma yanata dariya.

Yayinda *Blue* yabisu da kallo gwanin sha'awa sosai yakejin so da kaunar yaron acikin ransa, amma yarasa meyasa zuciyarsa takasa aminta da mamansa tsaki yaja mtww, tareda zama yame kallon *Dad* wanda shima kallosa yake inda yahango tsantsan rigima kwance akan fuskarsa, murmushi yai yace son yadai?...ciki shagwa'ba me cike da tsabar rigima yace *Dad* I tell you "Ita ce kuma I really love her, kai ya girgiza tareda cewa son naji to yanzu me kakeso ayi tunda matar aure ce eye?.

da sauri yamike ya'isa gurinshi tareda zubewa kasa yadafa guiwoyinsa yace yauwa *Dad*, ka kirasa kace yasaketa" sai ni na aureta ido *Dad* yazaro yace haba son ina kaga ana hakan eye?....fuska yahad'e, kafin yace to nidai afara akaina dan wlh nibazan iya hakura da'ita sonta ba, da dai *Dad* yaga alamar rigama yake nema sai kawai yace kaga son barci nakeji so bari nage na kwanta, yamike yanufi d'aki yabarshi nan zaune inda yabisa da kallo yayinda yakejin zuciyarsa tana wani irin bugawa me cike da tsoro da fargaba.

*Bayan kwana biyu*
*******
"Wasa wasa shirinsu *Dad* yana tafiya dai-dai yanda suka tsara, domin kuwa acikin kwana hudun nan duk yanda *Blue* din yaso ganin *Bilkisu* abin yacitura, hakan ne yasa harda wata yar rama yayi saboda damuwar rashin ganin nata gashi so da kaunarta had'eda wata irin zazzafar sha'awarta, sai sake ninkuwa yake azuciya da gangar jikinsa yayinda bayada aiki sai natasa *Dad* agaba dafad'in, dan Allah yasa d'an abokin nan nasa yasaki *Beena* shikuma ya aureta".

Saidai yai murmushi yace son kenan nibazan ta'ba iyacewa da d'an abokina yasaki matarsa ka auraba, alhalin suna ganin mutumcina ai ba'ayin haka domin yin hakan haram ne acikin addini, kuma kasan da hakan son amma meyasa kake kokarin take sani eye?...saidai kawai yaturo baki cike da yace *Dad* nidai kawai inasonta.

Maganar zuwa  gurin aiki kuwa tuni ya maida shi gefe domin kuwa yadaina zuwa, saboda gaba daya yamaida hankalinsa gurin ganin ya mallaki *Beenazar* dan haka sai *Bulama* ne kawai yake zuwa. *"Dad* da *Mom* sunyi magana har sun gaji, kasan cewar tuni tadawo kuma tasan dashirin ta ko dayaushe yana zaune babban falon part dinsu ko zaya ganta amma ina, ko gilmawanta baya gani saidai *Basma* wacce tadage sai art take amatsayin *Beenazar*, tana tashige masa tareda kiransa yah *Bilal* kamar yanda *Beenazar* take kiransa tana kuma kokarinyi masa duk wani abu da mata takeyi ma miji, yayinda shikuma yaketa shareta had'eda daure mata fuska, agefe d'aya kuma sunata shana soyayyar su itada  *Bulama* wanda tuni har manya sun shiga ansaka ranan aure bayan sun gama jarabawa kasan cewar sun kusa fara jarabawar.

  "Haka dai komai ya cigaba da tafiya yanda suka tsara har yau kwana hudu sosai, *Blue* yafad'a inda duk wanda yaganshi sai ya tausaya mashi kamar *Mom* sosai take tausaya masa dan haka tuni tafara rokon *Dad*, asassauta mashi hakanan wanda shikansa zuwa wannan lokacin tuni yafara tausayama tilon 'dan nashi, saidai kuma yana ganin har yanzu bai horuba tukun domin soyake  *Beenazar* tasake daraja da kuma kima a idonsa tayanda bazaya iya rabuwa da'ita ba, hakanan itama *Beenazar* din harda kuka takeyima *Basma* tareda cewa idan dai saboda Ita ake bashi wannan wahalar to ta hakura tayafe mashi, yayinda itakuma sai tayi dariya tace to ai *Dad* baice" masu sudaina ba, dan haka suka cigaba da gudanar da aikinsu.

********
"Aban garen aunty *Bebe* kuwa cikeda tsoro tabi Jiddo da kallo har tashige daki, yan mintuna kad'an sai gata tafito sanye da riga body hug da wandon crazy wanda yasa dukkan surar jikinta fitowa, musamman kirjinta tayafa gyale d'an karami akai tana rataye dajaka, yayinda kafarta sanye dawani high hil kallo d'aya zakaimata kagane babu tarbiyya atareda ita sai taunan cingam takeyi 'karas-'aras.

Kallonsu tayi sama dakasa batareda tace komai ba tasakai zata fita, da sauri aunty *Beben* da zuciyata yake aikin bugawa tace ke! Jiddo ina zakida wannan shirin haka eye?....,juyowa tayi dakarfi tareda buga mata wata uwar harara cikin tsawa tace ban saniba kuma baki isa ki hanani fitaba, sannan tasakai tafita inda tabar yan'uwanta sake da baki cike da mamakin wannan sauyi na yar'uwarsu, itakam aunty *Bebe* mutuwar zaune tayi inda ta cika da mugun firgicir.

To tun daga wannan ranan sai komai yasake ta'bar'bare mata wanda saidai muce Allah yasawake, domin kuwa tun ranan da tukunyar tsafinta yafashe siddabarun dake ciki yakoma kan Jiddo, shikenan tun daga wannan ranan sai jiddon tazama wata irin tantiriyar fitsararriya ta hanyar bin maza tamkar wata karya, wayanda duk rabi samarin datake yima walakaci ne shine yanzu sunga tazama wata iri,

shine suke kwansan suna rama abinda tayi masu ta hanyar yin lalata da ita, school kuwa tuni tadaina zuwa sai aikin yawon iskancin tareda shaye-shaye, yayinda kuma auny *Beben* bata iyai mata magana, asalima wani irin tsoronta takeji saboda tsawar datake buga mata dazaran tayi mata magana.

*********

*Bayan kwana biyu*

Ranan wata alhamis aunty *Bebe* ce zaune tabuga uban tagumi, duk talalace tafita hayyacita kasan cewar yau kimanin kwana uku kenan Jiddo  bata kwana agida duk inda take tunanin zata ganta bata gantanba, bata kuma san inda zata gantaba hakan yasake d'aga mata hankali kasan cewar duk wannan abun dake faruwa *Dad* jiddon bayana gari kimanin watansa uku kenan, yau yakirata yake saida mata yanan dawowa next week dan haka ciki masifar fad'an dayakeyi mata kwana biyun nan, wanda batasan abinda tayi masaba.

Yace da'ita tace da "Jiddo tadawo yanason ganinta yayi kewarta, tunda shi baisan abinda yasamu wayarta ba, idan yakirata baya samunta kasan cewar tace masa tana chan takoma gidan kawarta dazama, cikin masifar fad'a yace to fad'a mata tadawo gidan ubanta idan bahaka ba ransu zaya baci itada Jiddon, sannan yakashe wayar.

Hakan ne yasa suna gama wayar hankalinta atashe tanufi gidan kawarta, tafad'a mata duk halinda take cikin wanda daman tasan dasu saidai kari nan tabata labarin, cewa wani hatsabinbin boka yabayyana akasar Niger, batareda yin wani dogon tunani ba tace sutafi kasan cewar koce dama suna zuwa har can niger din neman asiri, dan haka  suka kwashe jiki suka tafi inda wani yaron kawarnata yajasu kasan cewar itama tuni tashanye mijinta, sai abinda tace kamar yanda itama aunty *Beben* ta yanshe nata mijin wanda yanzu yafara karyewa tunda harda tsawa yake mata.

Kwana dayini sukai ahanya sannan suka isa sunyi sa'a sun iske bokan, wanda
sukaima bayanin abinda yake tafedasu, cewar "yarta tabata tanason bokan ya taimaka yaimata abinda yarta zata dawo gida koda zasu koma su isketa agindan, sannan yakashe mata *Bilal* domin ta tsani ganinsa aduniya kilama shiyaima yarta asiri ta lalace.

Aikam take yabuga kasa yace masu aljanu aka tura mata dan su lalata mata rayuwa, dan haka karsu damu koda zasu koma gida zasu isketa, sannan yabata maganin yace tazubawa *Blue* acikin abinci idan har yaci shikenan za'a nemeshi sama ko kasa arasashi adoron kasa, kuma yatafi kenan har abada bazaya dawo ba sosai sukai murna tabiyashi ma'kudan kudi sannan suka dawo, sunso sudawo aranan amma hakan bata samuba suka bari sai gobe. 

*******

"Misalin karfe biyar na yammar ranan wata jumma'a da *Blue* bazaya ta'ba mantawa da'ita atarihin rayuwarsa ba, wacce kuma tayi yai dai_dai da kwana biyar kenan da suke gudanar da shirinsu, *Basmace* tafito cikin doguwar rigar shadda royal blue wacce tasha aikin duwatsu, anko sukai Ita da *Beenazar* har *Baffa boy* shima irin shaddan ne akasa mashi, sai suka yafa fararan gyale dasaka takalma farare shima *Baffa* takalmi farin suka saka mashi tareda hulla fara sai yaikamar dan larabawa, sunyi kyau sosai gwanin sha'awa kallo daya zakai masu kagane fita zasuyi.
Chapter 16 · 0% Book details