← Book details Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 18

Sashe 5

Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan haka yacigaba da yimasa addu'a tarefa tofamasa ruwan addu'ar, aiko *Blue* yacigaba da ihu da kara wanda kanaji kasan banashi bane, chan dai dayaji azaba tayi yawa yace da malam yatsaya zaya fita saidai wlh zaya koma jikin wanda ya aikosa ne, zayai masa illame muni daga shi har iyalinsa tunda yasa aka salemasa fata, malam yace shidai babu ruwansa yafita dai daga jikin wannan bawan Allah wanda baimasa komaiba.

"Yace yaji zaya fita saidai su sani akwai sihirin me tsanani ajikinsa", wanda idan basu dauki mataki akansa ba to akwai matsala babba, malam yace yagani kuma inasha'allah hardashi duk yau zayabar jikin nasa da izinin Allah, dan haka ta ina zaya fita?.. yatambayi aljanin inda yace ta hanci to bismillah muna jiranka.

"Wani irin atishawa *Blue* yashigayi ba sassautawa chan kuma sai yai shuru, dan haka malam yabashi ruwan addu'ar yasha da taimakon *Bulama* wanda yake rikeda *Blue*, yana gama shan ruwan addu'ar saiya fara wani irin kakari amai chan kuma sai yafara wani irin mugun bakin amai, Saida yai aman sosai sannan sai kuma yafadi agurin tamkar matacce. 

"Malam yace Alhamdulillahi! cike da tashin hankali sukai kan *Blue* din musamman *Dad*, da yadago *Blue* ya rungume batareda yadamu da aman dake jikinsa ba, asalima fadi yake my Boy! sai kuma ya kalli malam yace" malam naji kace Alhamdulillahi!, kuma gashi yafad'i bayako matsi.

    Cikin murmushi yace karka damu insha'allah komai yazama tarihi daga ciwon dayai da izinin Allah yaji sauki, yanzu kukaishi daki ku kwantar dashi zayai barci saidai koda kunga be tashi dawuri ba karkudamu zayai barci sosai ne wanda yake daukeda sauki acikinsa. "

  "Ajiyar zuciya *Dad* yasauke tareda kwalama kuku kira yazo ya gyara gurin yace ok sir, sannan yace da *Bulama* Son taimaka mukaishi ciki mu kwantar ok *Dad*, suka dauke shi suka kaishi saida suka cire masa wannan kayan najikinta kasan cewar duk sun facida aman da yai,

inda suka barshi dagashi sai farar singilet da farin box suka kara masa gudun a c kasan cewar sai wani irin mugun gumin yakeyi, sannan suka fito inda suka iske malam yana yima *Papa* bayani cewa akwai wasu magun-guna dazaya bashi wanda zayai amfani dasu,

insha'allah zasu taimaka mashi dayaki da duk wani sihirin daza asakeyi masa domin dai wannan  dayake jikinsa yanzu yazama tarihi da yardan Allah, sannan yanada kyau kuma suce yayi kokarin yaringa rikoda addu'a sosai, wanda insha'allah hakan yazai nisantashi da duk wani shaidanin aljani da mutum.

Nan *Papa* yafada'a *Dad* abinda malam yace" sosai ya gamsu da bayanin, tareda fadin insha'allah zaya sashi ya aiki da duk abinda malam din yace, sannan sukai mashi godiya sosai sannan *Bulama* yadaukesa yamai dashi gidan inda yakarbo magun-gunan, bayan duk yafada mashi yanda *Blue* din zayai amfani dasu sannan yadawo.

Idan ya iske su *Dad* suna nan  zaune suna fira cike da alhinin akan wanda yaima *Blue* wannan aiki, bayan yaba *Dad* tareda fad'a mashi yanda malam din yace yai amfani dasu sannan suka mike zasu tafi gida,

inda *Dad* yaketa yimasu godiya *Papa* yace badamuwa zasu dawo zuwa karfe uku tunda yanzu biyu takusa, wanda sunada tabbacin kila lokacin *Blue* din yafarka yace to shikenan, ya gode Allah yabar kauna da zuminci me dorewa *Papa* ya amsa da ameen ameen suka tafi.

inda bar *Dad* zaune yafada'a tunanin wanda yaima *tilon D'ansa wannan aiki, wanda iya tunaninsa yakasa tunowa wane yai masa har aka kira sallar azahar, sannan yamike yafita zuwa masallaci bayan yashiga ya gyarama *Blue* kwanciya cike da matsananci kaunar 'Dansa.

*******

  "Aban garen su *Beenazar* kuwa", cikin wata biyun dasuka koma abuja da zama abubuwa da dama sun faru na cigaba agaresu, da farko dai ranan dasuka koma da kwana biyu lokacin sun natsu sai *Ammu* tadauko kudin gadonta taba *Abbu* tace",

yacire yabiyama su *Beenazar* kudin makaranta sauran kuma yaja jari sosai yai farin ciki da hakan. Idan ko hakan akayi bayan ankarboma su *Bassam* tresfar sai akasa su sabuwar makaratar kudi me kyau tareda biyan kudad'en, suka fara zuwa cike da farincikin.

inda itama *Beenazar* kasan cewar takardunta suna hannu kuma sunyi kyau sosai, dan haka akasamo mata addimition anan university of abujan inda *Bunayya* yakeyi, wanda tareda *Basmati* aka samo masu kasan cewar tunda nan Bestinta *Beenazar* zatayi nan,
sai tace to itama tafasa zuwa alhikimat university din nan zatayi.

     "Hakan bakaramin jin dadi *Beenazar* tajiba, wanda daman har tafara tunanin yanda zata ringa zuwa school Ita kadai, dan sai *Bunayya* yana daukar suna tafiya tare wani lokaci su dawo tare tunda kowa da kwas dinsa dayake karantawa, yayinda kuma wani lokacin  ya rigasu dawowa idan yahuta sai yakoma yadaukosu ba tareda nuna gajiyawa ba.

      "Yayinda shikuma *Abbu* suka yanke shawarar yafara zuwa abba yana siyo yadin hijabai, aiko hakan akayi bayan sun samu hayan wani babban shago acikin kasuwar abuja, sai yafara siyo yadin hijabai yana siyarwa inda ko cikin sa'a abin yakarbu Allah yasa masu albarka,

domin kuwa sosai akeyin cinikin tareda samun alkhari me yawa kafin kace me tuni arziki yafara zama, tuni *Abbu* yasiya mashin na hawa wanda *Abbu* ce tace yasiya ko yasamu saukin zuwa kasuwa, sosai yake samata albarka yaname jin kaunar matarsa aransa.

     "Yayinda *Bassam* da *Bash* suke bin *Abbun* zuwa kasuwa gurin siyarda hijabai, amman sai ranan asabar da lahadi idan lokacin zuwa Islamic yayi sai sudawo sutafi, hakan dai suke rayuwaru gwanin sha'awa cike da jin dadi da kwanciyar hankali, haka su *Beenazar* suna tazuwa school inda kuma suke maida hankalinsu sosai akan karatunsu.

   "Yayinda inda basu ganeba *Bunayya* yana nuna masu suna kuma ganewa sosai, haka dai rayuwar tamika inda zumunci yasake kulluwa tsakanin umman *Basma* da *Ammu* sosai, kasan cewar sun kulla kasuwanci nasaida zannuwan gado wanda sukeyo order daga Dubai, kuma sosai abin yakarbesu kasan cewar Umma tanada kawaye "matan manya" dan haka sosai suke samun ciniki me cike da alkhairi wannan kenan.

*******
*Zaria*

"Aban garen su *Dad* kuwa sosai *Blue* yake barci wanda yai mugun basu" tsoro, musamman *Dad* dayake lekashi lokaci bayan lokaci dan ganin ko yafarka saidai kuma har alokacin be farkaba sai barci yake, hakan yasa yace da *Papa* *Barr* kaga har yanzu boy be farkaba kana ganin babu wata matsala?... ni naga kamar barcin yayi yawa.

murmushi *Papa* yai yace insha'allah babu matsalar komai, kar kamanta malam yace"   zaya da'de yana barci kuma karmu damu dan munga haka duk cikin samun lafiya ne ko ?...yace "eh fa haka ne kawai nad'an damune darashin tashin nasa. 

     *Blue* kam barci yayi sosai me cike da wasu irin mafarkaiya wayanda bazaya iyacewa adadinsu yawansu ba, sannan kuma bazaya iyatunasu duka ba saidai kwai wani guda daya da yatsaya mashi arai, wanda dashi yatashi dashi aransa.

     "Misalin karfe bakwai saura minti goma shabiyar alokacin ma har anfara kiraye kiraye  sallar magrib", sannan *Blue* yafarka tareda tashi yana mi'ka bakinsa dauke da salati ahankali yazuro dogayan fararan kafafunsa kasa, wayanda suke dauke da lallauwan kwantaccan gashi.

     Sannan yabude hannunsa yai addu'ar tashin daga barci wanda atunaninsa safiyane, bayan yashafa sannan yamike ahankali cike da jin wani irin kasala me tsanani wanda yasa yaji jikinsa yai wani irin nauyi, agogon dake manne abangon d'akin yakalla inda yanuna mashi karfe shidda da minti hamasin na yamma,

Ido yamurza da sauri tareda sake budewa, cikin turanci cike da mamaki ganin lokaci yaja yafurta _what!_6:50pm, ya akai nayi barci awannan lokacin eye?...sai kuma yaja guntun tsaki mtww! tareda tabe baki yace I think zazzabine yakeson kamani, naji jiki yai nauyi sosai maybe shiyasama nayi barci nan da "mom take cewa barcin la'asar barcin la'ana", saboda rashin kyansa, shiyasa natsanesa but amma kuma gashi nayi still tsakin yasake ja mtww! sannan cikin siririyar muryarsa yace astagafurilla.

  Sai kuma ahankali ya lumshe kyakkawan idonshi dasukai masa nauyi saboda barcin dayasha, wanda hakan yasa komai yadawo masa tun daga ranan dasuka dawo daga kasar waje shida *Bulama*, wanda idan be mantaba suna saukowa daga kan jirgi yaji kansa yai wani irin bala'i sarawa, wanda tunga sannan bazaya iyacewa kuma ga abinda yafaruba, sai yanzu dayatashi daga wannan nauyayyan barcin me dauke da wasu irin mafarkaiya barkatai.

     "Sai kuma yabude ido da sauri zuciyarsa tana wani irin mugun bugawa, kallon wani d'an karamin kalandar kwali dake kan drowar jikin gadon yai wanda yake dauke da rana kwanan wata hadeda shekara, kuri yaima kalandar da ido na yan mintuna wanda yanuna cewar yana karantawa ne, inda yaga yanuna muna yau asabar biyar ga watan shidda shekara ta dubu biyu da ashirin da d'aya,

Da haka yadauki kwalin da sauri jikinsa yana rawa yasake kalla tareda dubawa still dai abinda yagani yakaranta shine yasake gani yakaranta.

    "Hakan yasa yai saurin mikewa hannunsa rikeda kwalin zaya fita har yafara kiran *Dad*, sai kuma yatsaya cak! agaban mirron dakin tareda zuyawa ahankali cike da bugawar zuciya yakalli kansa amadubin, inda yaga wani irin uban kasumba dayataru akan fuskarsa wacce tayi wani irin fau, alamar dai_ she is not feeling fine_ gaduhu dayaga yayi sosai kamar dai bashiba haka yaga kansa amadubin.

   Dan haka yawaro ido cikin turanci yafurta me anya ni ne *Bilal* hada'ddan _guy_ da guys suke kira da *Blue* kuwa????....nooooo! is not me!...., *Dad* yafita da sauri yana kwalama *Dad* kira cikin tashin hankali har yana buga tuntu'be da kafet, yafita falon dai-dai lokacin da su *Dad* zasu fita zuwa masallaci yin sallar magrib.

    Da sauri suka tsaya tareda juyowa suna kallonsa fuskarsu cike da annuri, yayinda tuni *Blue* yakarasa gurinsu jikinsa yana rawa sosai had'eda bakinsa yaname, kallonsu tareda nunama *Dad* kwalin dake hannusa, yana sanyin magana amma bakinsa yakasa furta komai saboda wani irin nauyi dayaji yai masa.

"Cike da tsananin farincikin *Dad* yace" Masha'Allah *Barr* my Boy yafarka lafiya cike da murna *Papa* yace alhamdulillahi!, Allah mun gode maka Allah yakara lafiya alfarman annabin rahma (SAW) sukace ameen, sai kuma duk suka had'a baki sukace masa sannun yajikin?...

murmushi *Blue* yai da kyar kafin yafisgo am ok" da sauri yafada'a, sai kuma yakalli *Dad* wanda shima kallonsa yake fuska dauke da tsananin farincikin ganin ga dukkan alamu yaronsa yadawo hayyacinsa, dan hakan yace my Boy ya'akai ne?... cikin rawar murya yace *Dad* pls tell me today is what?...
Chapter 5 · 0% Book details