← Book details Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 18

Sashe 17

Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har sun mike sai sukaji motsi ta babban falo hakan yasa *Basma* tanufi falon inda taga *Blue* yana kokarin fita, sanye yakeda wata dakkaken shadda brown color, wacce tayi masifar yimasa kyau ta hanyar fito masa farar fatarsa wacce take shaki da kwantaccan gashi luffff!, sai kamshi turare yakeyi tashi ajikinsa kashin babu hula sai cukurkud'an gashin kansa dayaketa walkiya.

Cike da zolaya tanufi gurinsa da sauri fuska dauke da annuri, cak! yatsaya fuska murtik! cikin turanci tace hi my dear husband happy friday, woww! u are looking so good kayi masifar kyau gaskiya, to nifa yaka ganni nayi kyau?...taname juyawa, 'Dauke kansa yayi tareda kokarin bita gefenta zaya wuce da sauri tasha gabansa tareda d'an had'e fuska, tace wai nikam dai yah *Bilal* me nayi maka katsaneni ne eye?....cikin masifa hadeda tsawa yace malam saboda bana ra'ayinki ne wacce tazo gurinki Ita nake ra'ayin hope kingane ko?...,cike da nuna alamar mamaki tace yah *Bilal*  ni danake matarka baka ra'ayina sai ra'ayin matar aure Subhallahi! wannan wacce irin maganace haka?....cikin tsawa yace ban saniba kuma ko matar wanene ina sonta kuma sai nasameta, dan haka bani guri nawuce fashewa tayi da kukan karya tareda wucewa dagudu taje tafad'a ma *Beenazar* aikam suka shige daki suka ringa dariya kasa-kasa.

Can say suka fito inda *Basma* takarbi *Baffa boy* ta rungume dai-dai lokacin da, wayarta tayi kara koda taduba suna my dear ne yabayyana cikin murmushi tadauka, tace amincin Allah yatabbata ga mijina insha'allah ok gamunan zuwa suka fita suna yar fira part dinsu" *Dad* suka nufa.

********

Bakinsu da sallama suka shiga falon wanda yake dauke da mutane, *Dad* da *Mom* *papa* maman *Bulama* da kuma *Blue* wanda shigarsa kenan suma suka shiga, da sauri *Blue* yatashi tsaye yana me Kallon *Beenazar* wacce tayi masa masifar kyau, cikin rawar jiki dana murya yace haba my queen meyasa kike guduna kinsan irin azabar danasha kuwa saboda rashin ganinki, yana kokarin isa gareta da saurin *Dad* yace son tsaya mana hakan yasa yatsaya cak!
yayinda ita kuma kanta duke tanufi gurin *Mom* ta zauna tana dariya kasa-kasa zuciyata cike da kaunarshi tana me jin wani irin  farin cikin.

        Yayinda duka falon ake kallonsu ana murmushi dai-dai lokacin da itama *Basma* ta zauna kusada *Beenazar* din, bayan tamikama mama *Baffa boy* shikam *Blue* da sauri yazube gaban *Dad* tareda kama hannunsa yarike, jikinsa yana rawa zuciyarsa kuma sai akin bugawa take, yace *Dad* gatanan tazo ita ce my queen kataimaka mun kace" kartasake guduna wlh ina kaunar banason narasata, *Dad* rasata dai-dai yake darasa numfashina kaji?...

Kai yagyad'a tareda sakin murmushi sannan yace naji son yanzu ka nutsu ka saurari abinda zan fad'a maka kaji ko?..., kai ya gyad'a alamar to ya zauna ahankali tareda kurama *Beenazar* ido yanajin tamkar yaje yarungumeta yafad'a mata irin tsantsan kaunar dayake mata.

Gyaran murya *Dad* yayi tareda Kallon *Bulama* yace son yimana addu'a, nan yayi bayan yagama sannan *Dad* yace *Beenazar* tazo inda tazo kusada shi ta zauna cike dajin kunya, hakan ne yasake ba *Blue* damar cigaba da kallonta yana sakin murmushi me kayatarwa.

Cikin kwanciyar hankali *Dad* sannan yanuna *Beenazar* tareda fara bayani kamar haka son wannan din Ita ce *Balkisu* wacce ake kira *Beenazar*, da sauri yakalli *Dad* domin idan har baya mantaba sunan matar da'akace tashice, cikin murmushi yace "eh ita ce kuma matarka wacce na aura mata kana cikin halin rashin lafiya, Ita ce kuma naje nasake yimaka bikonta inda kace mun ka hakura zaka zauna da'ita to amma sai kakiyin haka, sai kuma akayi sa'a Ita dince dai wacce Allah yake nuna maka amafarki tareda jarabtarka da tsanani kaunarta, fahimtar hakan danayi yasa muka.

Nan yafad'a mashi duk yanda suka tsara har zuwa yau, dan haka ga queen dinka nan wacce kuma takasance matarka kema dota ga mijinki nan, inafata zaku rike juna amana cikin sanyi murya me nuna alamar tausayin kanta tace *Dad* inada magana, to dota inajinki...fuska had'e tace *Dad* yace baya ra'ayina so nima bana ra'ayinshi kaga zama dani dashi bazaya yiwuba, dan haka yasallami.

Wani uban zamura yai ya'isa gurinta tareda kama hannunta yarike, jikinsa da bakinsa suna yarawa yace kiyi hakuri kiyimun rai wlh bazan iya rabuwa dakeba ki gafarceni bisaga abinda nai maki, wanda nayishi abisa kuskure wato danace bana ra'ayinki bansan kece ba, aida ban fadi hakaba.

Cikin had'e fuska tace sannan kuma to aikace baka kaunata so zaman mezanyi da wanda baya kaunata eye?,.. haba my queen taya zance bana kaunarki alhalin kece rayuwata wlh ina kaunarki da dukkan zuciyata fatana kimanta duk abinda yafaru, sannan ki kaunaceni kamar yanda kike fad'amun amafarkina dan Allah kinji?.

Kai ta kawar d'aga barin kallonsa da  sauri yajuyo da fuskarta yana kallonta yace kin amince muyi zamanmu babu rabuwa har abada?...kai ta gyad'a alamar cike da kaunarshi aranta, yarungumeta batareda damuwa da mutanan dake falon ba, cike da tsanani farinciki yace nagode nagode sosai my *Queen* Allah yabarmu tare.

Gwanin sha'awa kallon d'aya zakai masu kaga sunyi matukar dacewa dajuna sosai suka burge dukkan wanda yake cikin falon, hakan yasa *Bulama* tafa masu su *Dad* suka tafa masu suna dariya, yayinda shikuma sai aikin kiss fuskarta yakeyi cike da matsananciyar kaunarta har yana kokarin kiss din bakinta, batareda yasan zayai hakan ba da sauri takauda kanta tana murmushi cike da kunya, dai-dai lokacin da*Bulama* yace hey are a mad, halan kamanta inda kakene ko?...Harara yabanka ma *Bulaman* tareda cewa "eh ni mahaukaci ne but amma akan kaunar my queen ko?...yana me sake rungumeta, dariya akai gaba daya falon. Sannan *Papa* yace to alhamdulillahi! tunda komai yadai-dai fatanmu kurike junanku da gaskiya da amana, nan dai akaita yimasu nasiha me shiga jiki daga nan kuma aka fara fira inda acikin firar ake sanarda *Blue* zancen auran *Bulama* da *Basma*, sosai yai farincikin jin haka domin yai matukar yabawa da natsuwar *Basman* ahaka dai har aka kira sallar magrib su *Dad* suka tashi suka nufi masallaci inda sukuma su *Beenazar* zasuyi tasu anan.

******
"Bayan dasukai isha'i sannan suka dawo, sukaci dinning wanda su *Beenazar* suka had'a *Blue* sai nan nan yakeda *Beenazar* har suka gama, *Dad* yace dasu *Blue* dauki *Basma* su kaita gida haka ko akai bayan su *Mom* da mama sun cikata da abin arziki, sannan suka kaita wanda kuma wannan ne karan farko da *Blue* yaga *Ammu* da sauran yan'uwanta su *Bassam*, aikam sosai sukaji dad'in ganin yah *Blue* dinsu dasukai matukar kewa inda shima yaji dad'in ganinsu, tareda jin kaunarsu aransa *Banuja* sarkin tambaya aikam tana tafaman tambayarsa inayaje tadaina ganisa, murmushi yai tareda cemata yayi tafiya ne  haka dai suka rabu cike da kaunar juna.

Adaran nan *Blue* ya angwance da amaryarsa *Beenazar* wacce yajita tamkar budurwa, shikam idanma badan dayasan tahaihuba dasai yace har yanzu itad'in budurwace gar aleda, cike da tsantsan kaunarta ya rungume matarsa suka sha barcinsu me dad'i wanda suka da'de basuyi ba, yayinda suka wurgar da *Baffa boy* chan gefe lol.

Washegari asabar ba aiki, dan aka sai misalin karfe goma shad'aya da rabi nasafe, suka tashi sukai breakfast bayan sunje sun gaida su *Mom* inda suka bar *Baffa boy* achan, sun dawo sai suka yada zango akaramin falonsu, inda *Beenazar* tayi kwance akan cinyar *Blue* tanata zuba masa shagwa'bawa yana biye mata, sanye yake cikin dakakkiyar shadda gold color Ita mahaka saidai nata yellow dinki daguwar riga, sunyi kyau sosai kana kallonsu kaga amarya da ango masu matukar kaunar juna.

        Cike da nishad'i yace my queen fad'amun dani da yah Bilal majnuni wakika fiso?...,cike da zolaya ta kallesa tareda shafa kyakkawan sajansa sannan ta yamutsa fuska tace gaskiya nafison *MAJNUNINA*, ido yazaro yace really?..yesss! baki yaturo cike da shagwa'bawa inda take taga yadawo sak! majnunisa, dariya tayi tareda rungumeshi yace why? kikafi son shi?...

tace saboda yafisona bayason ko kad'an yaga 'bacin raina lokacin muna tare inajin wani irin nishad'i marar musaltuwa, yace ok i promise daga yau sai nafishi" sonki bazan ta'ba barin na'bata maki raiba saidai abisa kuskure insha'allah, sannan zan riga saki nishad'i fiyeda yanda yasaki, yaname rungumeta sosai ajikinsa cike dajin dad'i tace nima nayi alkawarin faranta maka da dukkan karfina insha'allah.

    Haka nan suka wuni sunata zuba soyayyarsu gwanin sha'awa, babu inda *Blue* yaje sai sallah kawai yake zuwa yadawo, misalin karfe biyar na yamma lokcin tuni sunyi wani wankan sun sake wasu kaya, suna zaune ababban fall suna fira still yanzuma kwance take akan cinyarsa tanayi masa firan irin abubuwan dayai tayimata lokacin yana cikin hauka, idan wani yai dariya wani kuma ya girgiza kai cikeda tausayin kanshi.

   "Suna cikin haka sai wayarsa tayi kara kamar bazaya dauka ba, saida *Beenazar* tace anafa kiran wayarsa sannan fuska yad'an yamutsa tareda cewa nifa banason muna soyayyarmu atakura mana, miko mun nakashe da sauri tace a ah! kasani kowani muhimmin abune yataso ok to bani nagaji, bakuwar lamba yagani dauka yayi tareda sallama chan yace "eh nine sai kuma yayi shuru yana saurare abinda ake fad'a.

  Sai kuma yamike zumbur cikin tashin hankalin yace ok ok gani nan zuwa yanzu yakashe wayar, da saurin tace lafiya....cikin tashin hankalin yace aunty *Bebe* ce wai tayi hatsari tana asibiti kwance, Subhallahi!..ahanyar dawowa?..eh ina ganin bari naje pls ki kulamun dakanki kinji?...yana me shafar gefen fuskarta kai ta gyad'a tareda cewa nima ka kulamun da kanka adawo lafiya, ok Allah yasa my queen yadauki key mota yaimata kiss agoshi yafita da sauri.

       Aharabar gidan yaga *Dad* yafito shima cike da tashin hankalin ya isa gurisa yana cewa, *Dad* yanzu aka kirani wai aunty *Bebe* tayi hatsari "eh nima haka, to yaushe "ta dawo daga inda aka turasu agurin ankin nata?...yace wlh bansani ba tunda ko d'azu nakira lambarta bayashiga, to ko ahanyar dawowan tayi hatsarin?...to kila yanzu dai mutafi asibitin mugani.

"Aban garen aunty *Bebe* tsabar  farinciki yasatace saidai suka baro garin niger acikin daran nan, dan haka suka taho saidai suna gafda shigowa abuja ne sukai mummuna hatsari saka makon matsananci barcin daya kama direban, inda take shida kawarta suka mutu yayinda itakuma tayi mugun raunin ta hanyar karairayewa, adukkan wata gaba dake jikinta hakan yasa gaba daya halittarta yachanja, inda aka kwashesu zuwa asibitin shine aka kira *Blue* da *Dad* wanda sun d'auka ne acikin wayarta.
Chapter 17 · 0% Book details